💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 116
Da mugun sauri zeenat ta dawo dakin hannuta rike da pampers saboda yadda taga nablah na tsiyaya tasan pad ba zai mata ba wanda zuwa lokacin tuni baba bilki ta gama kimsa nablah data ke juyi da juya shanyayyun idanunta tamkar zata mutu..
zeenat ta mikowa nablah dake cikin bayi pampers din ta kar'ba da kyar ta saka jikinta na wani irin shaking.
Baba bilki ta kamota Suka fito ta canza riga mara nauyi iya gwiwarta Suka kwantar daita akan bed..zeenat ta fita daga dakin tana Neman layin deeni Amman shr tana ringing bai ɗauki kiran ,
wani irin gudu deeni yake akan titi da taimakon Allah ya samu ya karaso estate dinsu yana parking ya fito da sauri daga motor ko tsayawa rufe kofar motar bai yi ba, ledar mganin daya siyo ya dauka ya shiga gidan agigice ..Sanda ya shigo dakinta tuni har bacci yayi nasarar dauketa dan hk ya tsaya yana kallonta kafin daga baya ya karaso inda take kwance tana bacci da sauke numfashin wahala
A hankali ya soma tashinta yana hura mata iskar bakinsa a fuskarta .Ahankali ta bude shayayyun idanunta tana kallonsa dasu idanunta cike da rad'ad'in ciwo har wata uwar rama tayi ta gyara kwanciyarta tana yatsina fuska jikinsa ya janyota sosai ya rungumeta yana Kare mata kallo hankalinsa a matukar tashe da ganin yadda ta dawo cikin lokacin kankani, ya shiga shafa bayanta yana jin dumin jikinta na
ratsashi..
muryarsa a sarke ya kira sunanta "pure hrt .......
kasa amsa masa tayi sai idanunta data zuba cikin nasa masu narkar masa da zuciya batare da tayi kokarin cewa wani Abu ba " sannu ya kike jin jikinki?
tace "uhm sanda cikinta ya sake murd'awa da karfi ta saki kara me karfin gaske ,tana dafe mararta da hannuta daya tana yarfe dayan Hannunta da cizan lip's dinta ,bashiri deeni ya rude ya zabura ya kamkameta ajikinsa"
meke damunki ina ke miki ciwo tell please Gaya min inda ke miki ciwo? duk a lokaci daya ya jero mata tmbyr yana rungume daita .ta kasa magana sai juya kai kawai take ,babu shiri ya duro daga saman gadon ya nufi wardrobe dinta ya dauko mata doguwar riga ya daura maman ta jikinta ya dauketa ya fito daita rungume ajikinsa yana kiran zeenat da karfi ... "Zeenat.. !!
"Zeenat.. !!
Ta sauko da hanzarinta km a rude saboda yadda yake kiran sunan nata afrigice ,yana tafiya yace "kizo muje hospital ...a rude tace "OK har ta biyo bayansa sai kuma ta juya da sauri ta koma dauko mayafi
shi km ya nufi compound din gidan daita jikinsa har tsuma yake tsabar tashin hankali gabadaya ya gama rudewa ya Manta da wani maganin daya siyo mata sbd ganin yanayinta,
baba bilki ta biyosu har gurin mota tayi musu addua a adawo lfy Allah yaba da lfy kai tsaye family hospital dinsu suka nufa daita .Da gaugauwa aka yi attending dinsu
Dubawar farko doctor ya tabbarmasa da ciki gareta misscarriage tayi deeni yayi shock tare da shan jinin jikinsa hankalinsa km yayi mugun tashi da jin abinda doctor yace.ita kuwa zeenat kadan ya rage batayi suman tsaye ba, tsabar firgici da mamaki 'wani ciki ..?
"ciki wani cikin ga nablah....?
Shiru tayi kawai tare da hada hannuwata guri daya ta dunkulesu Kana ta shafa fuskarta da hancinta tana hadiye wani abu dataji ya tsaya mata arai..Taimakon gaugauwa akayi mata ,tare dayi mata wanki mara..
Zeenat ta kira ummi tana sanar mata ummi tace "again wani cikin batare dana samu jikokin ya'yan dana fi kauna arayuwata ba nake mafarkin samun su .......?
"uhmmmmm umminah kar kice hk please ...."ba laifinta bane itama daga Allah ne, na sani mamana Amman Ina son ganin tsatsonki a duniya kuma acikin gidan deeni kafin mutuwata, bakida kowa bakida komai bakida wani da zaki kira shakikinki a wannan duniyar idan bani a Raye ya'yanki sune gatanki,sune komanki sune farincikinki.
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..