Tallah

243 10 0
                                    

*THE THREE LOVERS*

_(Jealousy, true love and betrayal)_




Yana son bala'in sonta da kishin ta takama da sarauta ya Hana ya baiyana hakan iyayen su sun hada su aure duk da hakan Yana nunawa shi ba son ta yake ba umarnin iyeye ne.

Bata kaunar sa tun tana karama har ta girma tana da Wanda take bala'in son shima Yana sonta sai dai Kash iyayen su sun katse masu soyayyar sakamakon hadu su aure da akayi da Wanda Bata so.

Ya dauki alkawarin rabu su Koda ta aure Wanda aka Bata a gida bazai barta tayi zaman lfy ba sai ya kashe Mata aure duk sbd son da yake Mata.

Ta bayyana Masa Bata son sa akwai Wanda take so hakan ya kaishi ga rashin lafiya Amma duk da hakan Bai sanar da kowa abinda tace ba ya rufa Mata asiri sabida mutukar mahaifin ta ya samu labari sai ya Saba Mata.

Tayiwa saurayin ta alkwarin Koda tayi aure baza ta rabu dashi ba suna tare a waya Bayan waya ma zasu dinga haduwa a Kai a Kai.

Ta hakura an cigaba da biki har ya Kai ga an daura aure ranar daurin auren saurayin ta ya karya Mata zuciya da kalaman sa masu tsuma ta suka shirya guduwa ta fita ta same shi a inda suka yi zasu hadu.

A can gidan su ango ma kishiyar Mahaifiyar say tayi alkwarin rabu su Kota halin k'aka.

Hankalin iyayen ta ya tashi dake ba kowa yasan Bata son auren ba babu Wanda yayi zargin wani abun sai Mahaifiyar ta da kakar ta har suka Kai ga sanar da mahaifin ta ganin abun bana Kare bane ba, ran mahaifin ta ya baci yayi alkwarin indai hakan ta tabbata to tabbbas sai ya tsine Mata.😱

Shawara ta canza ta mike da niyar komawa gida Amma kalaman saurayin ta suka sake karya Mata zuciya ta koma ta zauna a wajan, yayi nasarar gano inda take yazo ya same su rungume da juna hakan ya harzuka shi sbida bala'in kishi Amma ya daure ya sanar da ita halin da iyayen ya suka shiga.

Kallon ta Ammar yayi yace, "Ban Miki Dole ba in Kinga Zaki tawo sbd mahaifan ki ki tawo mu tafi in Kuma shi zaki bi yadda Kika ga yafi Miki kawai".

Juyawa tayi da niyar Isa wajan Ammar Amma kalaman Anwar suka sake karyawa Amatullah zuciya ta tsaya cak ita Bata yi gaba ba ita Bata yi baya ba.

Alkwarin Anwar ya dauka na indai ta barshi wallahi sai ya kashe kansa.

Shin Ammar zata bi ko Anwar? Iyayen ta ko saurayin ta? In ta bar Anwar ya kashe kansa fa? In ta bishi iyayen tafa? In ta yarda ta bi Ammar tayi Yaya dashi kenan Bayan Bata son sa Kuma ga auren sa kanta? In Kuma ta barshi wanne Hali zai shiga shima? Anya bazai sake ta ba kuwa? Koda ta yarda ta bi Ammar Anya Anwar zai barsu suyi zaman lfy? Ko kuwa kishiyar Babar su Ammar zata barsu zaman lfy?

Anwar ko Ammar wanne Amatullah zata dauka?.


Coming soon✍

MASOYA UKUМесто, где живут истории. Откройте их для себя