Page 21

67 5 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_


_(True love, intense jealousy & betrayal.)_


By
Neat Lady



Not edited🤒



Dedicated to Ummu nabil😍


Jinjina ga:
*Ummu nabil fans grp*
*The three lover's fans grp*
*Zafafa novel's grp*
*Gaskiya writers fans grp.*

Dama grps din da ban San su ba amma su sun sanni ina mika sakon gaisuwa da jinjina a gare ku Kuna bani nishadi😂👍🏾😍


Page 21



......... Amatullah ta kalle ta tace, "To ni zan saki kaina da zakice shiri ne Inda ni Na saki kaina sai kice haka, ke ni ba wannan bama ya batun ki da khaleed?" Ta fada Dan ta kawar da waccan maganar.

"Eh jira muke Na karasa makaranta tunda an kusa in yaso daga baya sai ayi abinda za'ayi".

" to shikenan Allah ya zaba mana mafi alkairi. "

Ta amsa da amin.




Bincike sosai Dady ya saka ake masa akan Anwar nan aka gano mahaifin sa ya jima da rasuwa su biyu kuma Allah basu saga Anwar sai kanwar sa janan, a cikin unguwar su ba aji wata magana Mara kyau game da Anwar ko mahaifiyar sa ba sai dai kowa ya fadi alkairin ta amma badai sharri ba Dan mace me San jama'a.

Sosai su Dady sukayi farin ciki da jin labarin Anwar lokacin da ya sake dawowa wajan Dady Dady yace ya turo.

Har lokacin Anwar basu hadu da Amatullah ba so yake sai ya gama komai an saka rana sannan su hadu.


Ai kuwa haka akayi kannen mahaifin sa suka zo aka zauna dasu mai martaba aka tsayar da lokacin biki sati uku masu zuwa aka bada kudin aure naira dubu dari biyu.

Washe gari da yamma ta shirya tsaf cikin doguwar riga fara ta saka hula a saman hulan ta yafa mayafi,wayar Anwar ce ta shigowa wayar ta ta dauka yana shaida mata ya iso ta amsa ta kashe wayar.

Mikewa tayi ta dauki key din falon Dady ta fito, tunda ta fito ya hango ta ya zuba Mata ido yana kare mata kallo, mamaki yake yanzu wannan halittar ta kusa zama tasa? Ya kasa tabbatar da hakan.

Sai da ta karaso tayi murmushi tace, "muje". Ta fada tana yin gaba shi kuma yana kare mata kallo tana tafiya yana hasashen ranar da zata zama tasa.

Bude falon tayi ta Shiga shima ya biyo bayan ta ta juyo da niyar yi masa magana taga ya zuba mata ido yana kallan ta yana Dan cije baki, kallan sa tayi tace, "Wannan kallan fa?" Ta fada tana murmushi itama.

"Kinga yadda kika kara kyau kuwa Gaskiya kina hutawar ki" ya fada yana yi mata kallan kasa-kasa.

Murmushi tayi tace, "To ka zauna mana sai muyi maganar daga baya."

Kafin tayi wani aune ya rungume ta yana shafa bayan ta yana sauke ajjiyar zuciya yana lumshe ido, "Amatullah Allah ya nuna min ranar da zaki zama mata a gare ni, Amatullah ina sanki ina kaunar ki Dan Allah kar ki guje ni" ya fada idon sa a lumshe.

Zame jikin ta tayi tana murmushi tace, "kwana nawa ya rage, nidai ka zauna kawai."

Ba musu ya zauna ita kuma ta bude fridge ta dauko masa ruwa da lemo ta ajjiye  masa itama ta zauna, ya kasa dauke ido a kanta sai murmushi yake kafin kuma ya hade rai yace,"Anya baki karya min alkawari Na ba?".

Sai da gaban ta ya fadi Dan ita kanta tana jin tsoron sanar dashi tace, "Kai ka jika ka daina wannan maganar mun jima bamu hadu kamata yayi mu bawa junan mu kulawa ba wannan maganar ba" ta fada tana tsiyaya masa lemo a Kofi.

MASOYA UKUحيث تعيش القصص. اكتشف الآن