*MASOYA UKU*
_(The three lovers)__(True love, intense jealousy & betrayal.)_
Page 7
Not edited🤙🏻
........... A firgice Amatullah ke kallon Ammar da yake wuci kamar zaki, gaban tane ya fad'i jikin ta ya Soma rawa tana so ka kwace rik'on da yayi mata Amma ta saka, gabadaya tsoron sa ya mamaye Mata zuciya bata tab'a jin tsoron Ammar kamar na lokacin ba.
Shi kuwa Anwar Yana ganin haka yayi sauri ya sake ta ya afka mota yaja da sauri ya bar wajan Yana dariyar mugunta, tafiya yake Yana dariya kamar mahaukaci ya rausayar da Kai yace, "Yanzu aka fara wasan Amatullah babu ta yarda za'ayi na yarda wani ya aure ki bani ba.
Da sauri Ammar ya kalli inda motar take ganin Bata nan yasa ya cizi baki dan da sai ya saka an Kama Anwar.
Ita kuwa Amatullah juyawa bayan ta take ganin Anwar ya bar wajan ta sauke ajjiyar zuciya ta juyo da kallon ta ga Ammar, jan hannun ta yayi suka shiga cikin gidan Sarki ta kofar baya suna shiga daki ya cillar da ita ya zuba Mata manyan idon sa da suka koma ja sabida bala'in kishi, iya kadai idon tsoro suke bata hakan yasa ta sunkuyar da kai jikin ta na faman rawa zuciyar ta na bugawa da sauri.
Rasa abinda zaice Mata yayi sai safa da marwa yake a parlourn kalaman da yaji suna fadawa junan su suna yi masa yawo a ka, juyowa yayi gare ta murya a dashe yace, "Shi wancan din waye?".
Jikin tane ya soma rawa gaban ta na fad'uwa ta rasa me zata ce masa ita bawai tsoron sa take ji ba tsoron yanayin da ya same su take yi tsoron ta kar ya sanar da wani abinda ya faru, tsawar da yayi Mata yasa ta dawo daga duniyar tunanin da take tace, "Wani ne."
"Waye Wani bashi da suna?". Bakin ta na rawa tace, "Aboki nane, Dan Allah Yaya Ammar kayi hakuri Kar ka fadawa Daddy wallahi tsautsayi ne ban tab'a hugging nashi ba sai yau Kuma yau din ma shine ya fara bani b......" Cikin daga murya yace, "Kika sake Kika k'arasa maganar Nan sai na b'alla ki wallahi, yarinya ce ke baki san abinda ya kamata ba? Zaki fad'a min waye ko sai na karya ki yanzun Nan" ya fad'a Yana nufo da zafin nama.
Yadda yake magana a wani firgice kamar bashi ba yasa tsoron ta ya k'aru ta fara ja baya Tana hawaye tace, "Yaya Ammar shine Wanda nake so shine wanda nake burin aura bani da Wanda nake son na aura sama dashi Ina son sa sosai, Dan Allah yaya Ammar kaje kacewa Daddy baka Sona kaima kaga sai na auri Wanda nake so bazan iya rayuwa ba sai dashi dan Allah ka taimaka mana Yaya Ammar" ta fada tana fashewa da kuka.
Cak ya tsaya ya kasa motsawa kamar Wanda aka yanke Masa jijiyoyin sa,Jikin sa yayi bala'in sanyi Nan take zuciyar sa ta fara harbawa da sauri, kirjin sa ya fara zafi gumi na keto masa ta ko ina babu shiri ya zauna sharaf a kujera Yana sauke numfashi, kallon ta yayi da idon sa Wanda suka kankance yace, "Kin tabbata abinda Kika fada gaskiya min gaskiya shi kike son aura?".
Da sauri ta amsa Masa da, "eh Yaya Ammar shi nake so shima Kuma Yana Sona sosai." Hannun da ya fara matsewa kamar yadda yadda saba suna bada sautin kasss Yana shafa side din zuciyar sa dake Masa zafi.
Cize baki yyi yace, "Shikenan tashi kije" Yana Gama fadar hakan ya runtse Ido tare da cize baki.
Kallon sa tayi sai taji kamar Bata kyauta ba abinda tayi Amma dake zuciyar ta nasan abinda ta fada ta kawar da zancen tace, "Dan Allah Kar ka fadawa daddy abinda......" Cikin karaji yace, "enough, get lost" ya fada Yana runtse Ido sabida yadda zuciyar sa ke bugawa kmaar zata fito.
Kasa daurewa Ammar yayi ya kwantar da kansa a jikin kujera Babu abinda ke Masa yawo a kunne sai kalmar _Eh Yaya Ammar shii nake so_ watsi yayi da pillow dake kan kujerar, dafe side din zuciyar sa yayi Yana karata innalillahi wa'inna ilaihir raj'un, a hankalin ya dinga Jin sanyi Yana ratsa shi har zuciyar sa ta danyi sanyi Amma yadda kalaman Amatullah ke Masa yawo a kamar lkcn take fada Masa.
Kafin wani lkc zazzabi Mai zafi ya rufe shi ga ciwon kai suka had'ar masa lkc daya, Dakyar ya mik'e ya shiga daki sa balli pcm yasha ya hada da maganin ciwon sa ya kwanta akan gado Yana ajiyar zuciya.
Amatullah kuwa cikin sanyin jiki take tafiya tana dana sanin sanar da Ammar da abinda ta fad'a masa sabida tsoron ta Kar ya fadawa Daddy ta shiga uku, sai da ta Kai kofar gida ta kalli wayar hannun ta taga har tara ta wuce nan take gaban ta ya Fad'i me zata cewa Mama in ta shiga? Daurewa tayi ta karasa cikin gidan, a parlour ta tarar da Daddy da Mama tana shiga Mama tace, "Daga Ina kike?".
Bakin tane ya fara rawa tace, "Uhumm daga wajan Rahma nake naje akan wani assignment".
Daddy yace, "Shine Zaki fita baki sanar ba Kuma?". Sosa Kai tayi tace, "lokacin Dana fito Mama Bata daki shiyasa".
Daddy yace, "Shikenan jeki Kar ki sake dai".
Kamar jira take ta shige daki da sauri.
Rashin comments Mai yawa yasa bana typing sosai.

ESTÁS LEYENDO
MASOYA UKU
Romanceta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.