*MASOYA UKU*
_(The three lover's)__{True love, intense jealousy & betrayal}_
By
Neat LadyDedicated to Ummu Nabil😍
Not edited🤒
Page 32
........ Da hanzari aka dauki Aunty aka Shiga da ita daki ana bata taimakon gaggawa, kuka sosai Humayrah da Rahma suke yi Na rashin Yar uwa da sukayi, "a yanzu addu'a take bukata daga wajan Ku ba kuka ba, ita da tayi shahada ma ga juma'a ga kuma ciwon ciki ne ya kashe ta ai ita ta dace, kuyi hakuri Ku daina kuka" Yaya ta fada da sigar rarrashi.
Cikin lokaci kadan mutuwar Sumayya ta bazu a ko ina, haka aka dawo da ita gida akayi mata suttura bayan sallar aka tafi kaita gidan ta na Gaskiya, a lokacin Aunty ta farfado har ta dawo gida tana kuka.
Sosai Amatullah taji mutuwar Sumayya tayi kuka sosai tana mata addu'ar samun rahamar Allah, gida ya cika makil ana ta karbar gaisuwa har dare yayi.
Haka aka kwashe kwanaki uku ana karbar gaisuwa har kuma lokacin Amatullah bata San da maganar auren ta ba, ranar da akayi uku da daddare ciwon cikin Amatullah ya tashi sabida bata San cin abinci gabadaya.
Tana daki tana rike ciki tana kuka Aunty Hafsa ta shigo tana fadin, "Amatullah ki fito falo mana ana ta zuwa gaisuwa ba'a ganin ki" ta fada tana karasowa inda take kwance.
"Ciki nane yake ciwo" Amatullah ta fada dakyar.
"Subahanallah amma shine baki fada ba? Period pain ne?".
" A'a ciwon ciki ne" ta sake fada tana cize baki."
"Okay bara Na kira Ammar" ta fada tana ficewa da saurin gaske.
Har zata fita kuma sai ta duba hannun ta taga waya sai kawai ta binciko number sa ta kira shi, dake dare yayi yana zaune a bedroom din sa shida Nana wayar ta shigo yayi kamar bazai dauka ba ganin wacce take kiran yasa shi ya dauka, "Ammar in ba damuwa pls kazo ka duba Amatullah ciwon ciki ne yake damun ta" ta Hafsa ta fada a rude.
Mikewa yayi yace, "Okay gani nan zuwa" yana fada ya kashe wayar ya bude inda yake ajjiye allurai ya dauka ya hada da sring sannan yace, "Bara naje akwai patient a gidan" bai jira mai zata ce ba ya fice daga dakin.
Jallabiya ce maroon colour a cikin da mai gajeren hannu, koda ya shiga falon babu kowa sai Aunty Hafsa da Mama, Mama tace, "Tana daki a kwance bata San cin abinci ne dan Allah ka saka ta taci abinci".
Ya amsa da to tare da nufar dakin, a hankali ya bude dakin ya hango ta a kwance tana mutsu-mutsu, karanar riga ce a jikin ta iya guiwa kuma irin me kama jikin nan ce ta kwanta a jikin ta sosai gashi juye-juyen da take yi ya saka ta tattare ta dawo iya cinyar ta.
Da Sauri ya karasa gare ta ya zauna akan gadon ya dago ta ya kwantar da ita a jikin sa a rude yace,"ciwon cikin ne haka? Sannu ki bar kuka pls" ya fada yana kokarin hada allurar dake hannun sa.
Bata amsa masa ba tayi shiru ta kwanta a jikin sa sai hawaye da take ji, "period pain ne?" Ya tambaye ta yana jan allurar a cikin sirinji, bata amsa masa ba sai rike shi gam da tayi ganin allura a hannun sa.
A hankali ya daga rigar ta ta baya ya saka sirinjin a hankali gudun kar ta ji zafi, amma sai da tayi kara ta sake rike shi tana kuka, shafa kanta yake a hankali yana fadin, "Is okay an gama ki bar kuka" tun yana jin kukan ta har bacci ya dauke ta.
Jin tayi bacci yasa ya zame ta daga jikin sa ya kwantar da ita maimakon ya rife ta sai kawai ya tsaya kare mata kallo, lumshe ido yayi yana tunanin yanzu wannan halittar ta sake zama mallakin sa a karo na biyu, murmushi yayi kawai ya dauki blanket ya rife ta ya fito ya ja mata kofar yayi gida.

KAMU SEDANG MEMBACA
MASOYA UKU
Romansata aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.