*MASOYA UKU*
_(The three lover)__(True love, intense jeolousy & betrayal)_
By
Neat LadyNot edited🤒
Page 15
....... Cike da mamaki mutanen gidan sarki ke bin Aunty da kallo wasu suna daukar maganar shirme wasu tsinewa Amatullah.
Aka taru aka cika ana ta gulma, a guje akaje aka Sanar da uwar gidan sarki abinda yake faruwa takaici ya kamata ranta ya baci amma bata fito ba ta tura Ahmad yaje ya Sanar da me martaba abinda yake faruwa.
Bayan fitar ta cike da Bacin rai Ammar ya zauna akan kujerar ya kurawa waje daya ido yana tunanin abinda ta fada akan Amatullah, sautin kukan ta yaji hakan yasan ya juya da Sauri ya kalle ta ya dafe kai tare da fadin, "me yasa kike kuka kuma? Pls stop crying i don't like it pls."
Ita dai kuka take sosai sabida cin mutuncin da Aunty tayi mata _daman har yanzu ana wannan al'adar a gidan sarakai? Naga an daina kai ya waye an samu walwar yad'uwar addini amma tazo har take Kiran na Mara tarbiya akan abinda bai kai ya kwo ba_ abinda take ta fada a ranta cikin takaici tun yanzu ta fara ganin wulakaci ina ga gaba kuma.
Jin abinda Aunty tayi yasan ran me martaba ya baci ya kira meeting din gaggawa yace kowa da kowa Na gidan ya hallara har bayi sannan ya aika aka tawo da Yaya.
Cikin bayin sarki aka aika akace ta kira su Ammar, koda ta Sanar dasu basu jima ba Amatullah ta yafa mayafi suka fito har fadar cikin gida.
Mai marbata ya kalli Aunty yace, "Maimaita me kikaje yi gidan Ammar." Babu bata lokaci ta sanar dashi ta dora da cewa, "Daga Na fadi haka Ammar ya mike yana min tsawa wai Na zagi matar sa har cemin akan matar sa bb abinda bazai iya yi min ba" ta fadi hakan tana kuka.
Cike da mamaki Ammar yake kallan ta yana fadin lallai matar nan makira ce.
Cike da fusata Hajiya Yaya tace, "To ina ruwan ki me ya kaiki? Shishshigi ko Neman gulma? in ma karba jinin budurcin ne ke zaki je? Matsayin uwa kike a wajan sa fa amma ki dauki kafa zik'au-zik'au ba kunya kice wai kinzo karbar shaidar matar sa wannan ai shirme ne a ina kika ji ana wannan jahilcin yanzu? Ko ke anyi miki haka da aka auro ki? Wanda bai gada bama yake sarki yanzu balle Wanda ya gada, kawo mutunci wannan abinda ya shafi ma'auratan ne bake ba, har da tara bayi wai su shaida tsabar zubarwa da Ammar da Amatullah din kima da mutunci."
Mai mastaba jin Yaya tayi shiru ya sa yace, "Kiyi hakuri Yaya, kar Na kara jin wani Abu makamcin wannan a gidan nan kuskure ne tunda kinyi ya wuce kar a sake gangancin maimaita irin sa kinji Na fada miki."
Cikin kuka tace, "Allah ya Baku hakuri banyi hakan da wata manufa dan Nima da nasan haka zaimin rashin kunya babu abinda zai kaini" ta fadi hakan tana goge hawaye.
Mama ta kalli Ammar da Amatullah tace, "Ku bata hakuri." Yaya tayi caraf tace, "Hakurin uwar me zasu bata? Me suka yi mata ita taje har inda suke ta shiga hurumin da ba nata ba, ke da baki je ba yayi miki ne?."
Ammar ya kalle ta yace, "Allah ya wuci zuciyar ki" jin hakan yasa Yaya taja saki tace, "Yanzu sai ki koma ki Tara bayin da kika Tara ki fada musu a kul naji wani ko wata Na wannan maganar in kuma ba haka ba wallahi hukunci zai biyo baya."
Cike da takaici Aunty ta mike ta fice daga fadar, mai martaba ya kalli Amatullah da kanta yake kasa yace, "Kiyi hakuri kinji kar ki saka wannan a ranki, sannan bana so maganar nan taje kunnen koda mahaifan Amatullah ne".
Aka amsa da to kowa ya watse Ammar da Amatullah suka nufi part din Umma suka gaisa kamar babu abinda ya faru, ita dai Amatullah sunkuyar da kai Kawai take sabida kunyar Umma take ji sosai.
VOCÊ ESTÁ LENDO
MASOYA UKU
Romanceta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.