*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_By
Neat ladyDedicated to Ummu nabil😍
Not edited🤒
*An fafata😂 tsakanin team din Nana da na Amatullah sharyin ya burge ni sosai🤣 nayi dariya kamar babu komai, nagode muku Allah ya bar kauna.*😍😍
Page 36
.......... Ammar ne ya kula da hawayen da take yi da sauri ya saki Amatullah ya karasa gare ta ya rike ta yace, "Nana baki da lafiya ne kike kuka?" Zaunar da ita yayi akan kujera ya kalli Amatullah yace, "dauko ruwa" ba musu ta bude fridge ta dauko ruwa ta bude da kanta ta karasa wajan Nana ta mika mata.
Kin karba tayi sai ma kawar dakai da tayi kamar ba ta ga Amatullah din ba, janye hannun ta tayi bata damu ba sabida ta dauka duk cikin ciwo ne dan sun dauka bata da lafiya ne.
"Meya same ki?" Ammar ya tambaya cikin kulawa.
"Kaina ne yake ciwo kadan" ta fada tana dafe kai.
"Ayya sannu, Allah ya kara sauki" Ammar ya fada yana karbar ruwan hannun Amatullah yana mika mata.
Karba tayi tasha ta jinginar da kanta kirjin ta na bugawa, kallan Amatullah Ammar yayi yana so ya karanci yanayin ta amma ko kadan bata nuna da wani abun ba, ya mayar da kallan sa ga Nana yace, "Kema bakya san hutawa ne ai da sassafiya kin tashi kina girki da kin huta da older nayi niyar bayarwa".
"Taci abinci sai tasha magani ta huta ko?" Amatullah ta fada tana kallan Ammar.
Ammar yace, "Eh Gaskiya ne kawo mata abincin" inda ta ajjiye abincin taje ta bude flask din ta hada mata tea ta debo chips ta kawo ta mika masa ya bata.
Zama yayi a kusa da ita yana bata a baki yana satar kallan Amatullah da take danna wayar ta, mikewa tayi tace, "bara na dawo" bata jira mai zaice ba tayi sauri ta koma dakin ta.
Dafe kirji tayi sabida yadda yake bugawa da sauri ta runtse ido ta kawar da tunanin a ranta ta nufi part din Ammar, gyarawa tayi ta wanke toilet ta kade falon dake babu dauda bata bata lokaci ba ta gama, kasa ta dawo ta gyara nata dakin tayi zaman ta bata fita ba.
Ammar kuwa sai da ya tabbatar ya bawa Nana kulawar da ta kamata sannan ya mike ya koma bangaren Amatullah, a zaune ya same ta tana kallan tv ta dora kafa kan daya tana kadawa.
Karasowa yayi ya zauna kusa da ita yana jiran yaji tayi korafi akan abinda yayi Nana amma sai yaji shiru sai ma juyowa da tayi ta sakar masa murmushi tace, "Ya jikin nata?".
"Ta samu sauki ciwon kan ma ya warke".
"Masha Allah ya kara lafiya".
" Amin, bakiyi breakfast ba."
Yatsine fuska tayi tace, "Bana jin yunwa ne Allah kuma dan Allah kar kace sai naci yanzu" ta fada tana marairaicewa.
Rungumo ta yayi ya saka hancin sa a wuyan ta cikin murya kasa-kasa yace, "Kema kin san bazan kyale ki ba sai kinci, ga cake din ki ma bamu samu mun yanka ba".
"Nidai Allah na koshi zanci lunch anjima, ai lafiyar ta tafi yanka cake na saka shi a fridge ayi breakfast dashi gobe."
Sosai yaji dadin abinda tace hakan ya saka yace, "To abar batun cake yanzu breakfast dinki."
"Shikenan to naci cake din ma yanzu, amma kai kayi breakfast din kuwa?".
Kwanciya yayi akan kujerar yayi filo da cinyar ta yace, " Sai na tabbatar mata na sunci sun koshi kafin naci nima".

ESTÁS LEYENDO
MASOYA UKU
Romanceta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.