*MASOYA UKU*
_(The three lover's)__(True love, intense jeolousy & betrayal)_
By
Neat LadyNot edited🤒
Page 17
.........Amatullah tana zaune tana tunanin abinda Anwar yace Ammar ya bude kofa da sallama ya shigo,har ya karaso Inda take bata sani ba tayi nisa cikin tunani.
Dafa ta yayi hakan yasa ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi, hakan nan ta samu kanta da sakar masa murmushi tace, "Sannu da zuwa" bai amsa ba sai zama da yayi kusa da ita cike da damuwa yace, "Tunanin me kike yi haka?."
"Babu komai" ta bashi amsa tana juyar da fuska, "kamar ya babu komai har na shigo baki sani ba kuma kice min babu komai".
" Na gaji ne kawai" ta bashi amsa a takaice, mikewa yayi yace, "Shikenan, kedawa kuka dawo? Bayan nace ki kira".
" Bayan mun fito zan kira ka kenan sai ga Bala shine na biyo su Rahma muka dawo."
Bai amsa ba kawai ya shiga d'aki tabi shi da kallo, ta wacce hanya zata bi tace ya sake ta? Shine abinda kawai take tunani.
Jin sa shiru bai fito ba ga kuma abinci ta ajjiye yasa ta mike cike da karfin hali ta nufi dakin sa, tazo gab da dakin sai kuma ta tsaya a hankali tace, "To ni me zance masa? Ni da zamu rabu ina ruwa na da cin abincin sa? Kafin mu rabun dai na dan kyautata masa ko yafi saki na da wuri" da wannan tunanin ta fara knocking din kofar.
Daga ciki taji ya amsa a hankali, da sallama ta turo kofar ta shiga dakin, karewa bata tsaya kallan dakin ba ta tsaya a bakin kofar tace, "Na gama abinci fa" ta fadi hakan a sanyaye.
Yana zaune ya dafe kai yace, "ki ci kawai bana jin dadi" ya fada ba tare da ya dago ya kalle ta ba.
Sai taji babu dadi cikin damuwa tace, "Sannu, amma ya kamata kaci abincin sai kasha magani".
Dago kai yayi akayi sa'a suka had a ido ya lumshe ido yace, " Bazan iya ci bane maganar nan da nake miki ma karfin hali nake yi".
Jikin tane ya sake yin sanyi a hankali tace, "Sannu Allah ya kara sauki" daga haka ta bude kofar ta fice daga dakin.
Falon kasa ta koma ta bude abincin ta dauki tuwo daya ta saka daya ta zuba miya ta dawo saman ta zauna, bud'e tuwon tayi daga leda amma ta kasa saka hannu taci hakan nan taji itama ya fice mata a kai, tana nan zaune ita bata ci ba kuma ita bata rife ba tayi shiru tana juya shi a hannun ta.
"Ya kika kasa cin abincin" ya fada a hankali.
Juyowa tayi ta kalle shi yana tsaye a bayan ta ya hard'e hannu a kirji ya zuba mata ido, dauke kai tayi daga kallan sa dan bata iya juye kallan cikin idon sa tace, "na kasa ci ne."
Karasowa yayi ya zauna kusa da ita ya kalle ta yan a karantar yanayin ta yace, "Meyasa?."
"Haka kawai." Dan murmushi yayi yace, "Ban yarda ba, ko dan banci bane yasa kika ki ci?".
Idon tane ya ciko da hawaye cikin shagwaba tace," bana so nayi abinci ba'a ci ba" ta fada hawaye na sakkowa daga idon ta.
"Oh god, to meye na kukan? Na fada miki bana san ganin hawayen ki ko? Is okay zanci."
Goge hawayen fuskar ta tayi ta mike yace, "Ina zaki kuma?".
" kasa zanje na dauko maka abincin yana dining" ta fada tana niyar Barin wajan.

YOU ARE READING
MASOYA UKU
Romanceta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.