Page 16

103 4 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover)_


_(True love, intense jeolousy & betrayal)_



By
Neat Lady


Not edited🤒


_Zaman aure da Wanda zuciyar ka bata so sai ka kai zuciya nesa kayi yak'i da shaidan in na haka ba kome zuciyar ka ta d'arsa maka akan abokin zaman kawai aikatawa zaka yi ba tare da dogon tunani ba, haka ta kasance tsakanin Amatullah da Ammar, Ku cigaba da kasancewa dani dan jin yadda labarin zai kasance._😊


_Hak'ika ina ganin masoya sosai da suke nuna kauna a zahiri😍 ina jin dadin hakan matuk'a Allah ya bar zumunci._🥰



Page 16




......... Har wayar ta tsinke ba'ayi picking cike da takaici Amatullah ta jefar da wayar akan gado zuciyar Na kuna.

Haka Amatullah ta dinga trying number Anwar amma no answer har bayan i'sha, bata fito ba yana daki tana buga a waya, Ammar bayan ya dawo daga masallaci ya kalli Abinci yaga yadda aka kawo shi haka yake da Alama dai bata taba shi bama, tsaki yayi direct ya nufi dakin ta.

Dan knocking yayi tare da tura kofar da sallama, a ciki ta amsa masa sallamar ba kuma tare da ta dago ba, kallan ta yayi yace, "Lafiya baki ci abinci ba?".

Cike da kosawa ta kalle shi ta rausayar dakai tace, " Na koshi bana jin yunwa." A yadda take maganar ya gane yanayin ta yayi murmushi yace, "Malama ki fito kici abinci ki saka cin abinci a cikin sharadan da Na baki dazu, so tashi muje" ya fada yana tamke fuska.

Kamar zatayi kuka tace,"Wallahi Bana jin yunwa yanzu zanci anjima" ta fada a shagwab'e.

Banza yayi mata ya bude kofa kawai yayi ficewar sa, dole ta mike ta fito tana masifa a zuciyar ta dan tasan halin sa baya san maimaita magana .

Zama tayi a kujerar dake kallan sa ta dauki plat ta bude, mandi rice ce sai grill chicken sai cole slow da kayan fruit, dan Kadan ta zuba ta koma gefe ta zauna.

Ba tare da ya kalle ta ba yace, "Abincin ma sai nace ki zuba min?." Dago kai tayi dan ita harga Allah ta dauka yaci, turo baki gaba tayi ta dauki plat ta zuba masa ta karasa gaban sa ta ajjiye akan table din dake kusa dashi, kallan abincin yayi ya dago ya kalle ta yace, "Abincin waye wannan?".

Cike da mamaki ma take kallan sa lallai ya raina mata hankali yace ta kawo abinci ta kawo yace kuma Na waye, cike da takaici tace, " Naka ne".

"An fara miki kowa rumbu ne irin ki, rage rabin sa yayi min yawa." Ya fada hankalin sa Na kan tv.

Ranta ne ya baci da taji sunan da ya kira ta dashi wai rumbu, ragewa tayi ta bar dan kadan ta kawo masa ta ajjiye bata jira yayi magana ba ta juya da sauri ta koma mazaunin ta.

Dan murmushi yayi kadan sannan ya sake cewa, "Ba ruwa ba lemo a haka zanci abincin?."

Wayyo Allah ta furta a zuciyar ta a fusace ta mike ta kawo masa ta koma ta zauna tana hura hanci, dariya yake a zuciyar sa dan shi dariya take bashi sosai kawai yana dannewa ne.

Shiru falon yayi babu me magana sai karar tv da take tashi kadan-kadan, Amatullah ce ta fara mikewa zata shiga daki taji maganar sa yace, "Dawo".

Dafe kai tayi tana jin kamar ta shake shi, dole ta dawo ta zauna rai a bace, bai kulata ba ya cigaba da cin abincin sa yana satar kallan ta yana jin wani Sabon nishadi Na ratsa shi.

Sai da ya gama ya kalle ta yayi mata alamun da ta tafi, ai kuwa kamar jira take ta mike a fusace tayi daki ta banko kofa.

Shima mikewa yayi yana murmushi ya shige dakin sa.

MASOYA UKUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora