Page 2

149 5 0
                                    

*THE THREE LOVERS*

_(True love, intense jealousy & betrayal)._

Free book

Page 2


*ASALIN SU.*

Alhaji Muktar Sarkin kasuwa Wanda ake kira da Baba tsohon mai kud'i ne irin na dah ya mallaki kadarori da dama kuma mutum ne mai yawan taimako yana daya daga cikin masu taimakon talakawa a garin kano, fulanin adamawa ne irin kyawawan Nan kana kallon su kaga fulani, Alhaji Muktar yana da mata guda d'aya tun auren saurayi da Buduwar wato Hajiya Azumi wacce ake kira Yaya dattijuwar arzuki ce akwai kyauta sai dai ta mace mai fad'a sosai kuma bata tsoro ko kad'an ko waye Dan ta mare shi ba abune mai wahala ba a wajan ta ga barkwanci da zolaya, tun farkon auren su da Allah ya basu haihuwa sai yaron ya mutu a haka har ta haifi yara hudu amma Allah bai raya su ba har suka fitar da rai, lokacin da suka haifi Ali basu saka rai dashi ba sai gashi Allah ya raya musu shi yana da shekara uku a duniya suka sake haifar mace aka saka mata Asiya bayan ita sai Umaima amma itama bata jima a duniya ba Allah ya karb'i abar sa.
Ali ya taso cikin gata shida Asiya amma duk da gatan da suke samu hakan bai hana Yaya tayi musu tarbiya mai kyau ba.
Kyawawan fulani ne kaf familyn babu bakar fata Allah ya basu baiwar kyau kamar su sukayi Kansu,
Jikan sarkin Kano wato Abdulkadir sun taso tare da Ali cikin aminta mai ban sha'awa basa fada ko kadan kullum suna tare bacci kawai ke raba su hatta makaranta d'aya suke wajan zaman su d'aya a ko wacce makaranta hakan yasa mahaifin sa wato Alhaji Sani Haruna lamido yake ce musu Hassan da Usaini sabida shakuwar su, A gidan Alhaji Sani Haruna Lamido yaran sa uku Ahmad ne babba sai Abdulkadir sannan Hajara itace autar su, tun a haihuwar Hajara Allah ya dauki ran mahaifiyar su wato Hajiya Hadiza hakan yasa Yaya take kaunar Abdulkadir sosai Dan yaro ne mai hankali sosai.
Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya har suka girma sosai suka fara kasuwaci, a rana Allah ya had'a su da matan da suke so har maganar aure ta shiga tsakanin su, rana d'aya aka daura musu aure suka tare a gidan su na alfarma bayan daurin auren su da kwanaki kad'an Alhaji Muktar Allah yayi masa rasuwa, babu yarda basu yi ba akan Yaya ta dawo gidan amma taki tace ta zauna ita kad'ai hakan yasa suka samo mata mai aikin gida.
Mardiya itace uwar gidan Ali ita kuma Mariya matar Abdulkadir, yadda suka ga mazajen su suna kaunar junan su hakan yasa suma suka June suna aminta da girmama juna
Lokacin da Allah yayiwa Haruna lamido rasuwa wato kakan Abdulkadir lokacin Mariya tana d'auke da cikin wata biyar, ansha kuka sosai sabida sarki adalin sarki ne kowa addu'ar sa Allah yasa a samu mai imani kamar sa.
Babu zato babu tsammani aka sanar da Abdulkadir za'a yiwa sarauta dah yaki karb'a yace sai dai a bawa Ahmad amma yace Sam baya so hakan yasa aka bawa Abdulkadir sabida Alhaji Sani yace baya raayin sarauta shima.
Ansha shagalin nadin sarauta aka raka sarki gidan sa, cikin adalci sarki yake gunadanar da sarautar sa kamar kakan sa, bayan ta haihu aka samu ya mace aka saka mata sunan mahaifiyar sa da ta rasu wato Hadiza hakan yasa ake ce sunan Ummi, babu jimawa Mardiya ita ta haifi yar ta mace wacce taci sunan yaya na gaskiya wato Hafsa, anyi shagalin suna sosai lokacin Ummi tana da wata uku a duniya.
Bayan kwanaki kad'an sarki Abdulkadir ya nemi da ya bawa aminin sa sarautar waziri amma Sam yaki yace shi baya so yafi son kasuwanci sa, dakyar aka shawo kan yaya ta amince ta dawo gidan Ali da zama amma baza kace ma tana gidan ba.

Ba'a jima sosai ba sarki ya fara Neman kara aure inda ya samo yar Jigawa Wato kaltume, suna zaman lafiya babu laifi Dan ita Mariya babu ruwan ta sab'anin Kalmute da take makirar gaskiya sai dai akwai kissa, a gaban idon ka zata nuna ita Mai kaunar kace,
Bayan shekaru biyu Mardiya ta haihu ta haifi namiji aka saka masa suna Yasir yana da kwana arba'in aka Mariya ma ta haifi danta namiji kyakykyawa ake saka masa Ammar, haka rayuwa ta cigaba da tafiya su Ammar na girma suna da shekara uku Mardiya ta sake haihuwa namiji aka sa masa Ahmad, bayan an wasu watannin kaltume ta haifi yarta mace aka sa mata suna wato Nafisa.
Bayan shekaru tara lokacin Kaltume tana da yara uku duka mata hankalin ta ya tashi sosai akan lallai sai ta haifi namiji sabida ganin yadda Mariya take da maza har gudu biyu ita bata dasu ga wani cikin a tare da ita kuma, Mardiya ta sake haihuwar yarinyar ta uku aka saka mata suna Amatullah sabida yadda yarinya ta shiga ran kowa.
Tunda aka haifi Amatullah Ammar yake jin haushi sabida Amatullah ta kasance yarinya mai jiki tun tana jaririya hakan yasa Mardiya ta sha wahala wajan haihuwar ta babu Wanda yayi tunanin zata rayu dalilin hakan yasa Ammar ko kallon ta ba yayi, dariya yake bawa kowa musamman Yaya da takan ce masa ita zata bashi ya aura shi kuma yace Allah ya kiyaye.
Satin Amatullah biyu Mariya ta haifi ya mace itama aka saka mata suna Rahma, zumunci sosai ake tsakanin Mariya da Mardiya ba'a jin Kansu tsakanin yaran su ma in baka sani ba kaga dan waccan anan baza kace ba nata bane, su Amatullah nada shekara biyar Mariya ta sake haihuwar Hamza jin hakan ya tayar da hankalin Kalmutume sosai ta fara yawon malamai akan a taya ta addu'a Allah ya bata namiji, koda ta sake samun wani cikin ta d'auka namiji ne ta siyo kayan maza da yawa amma Allah ya canja ya sake bata mace a lokacin Mardiya ma ta haifi Kabir, bakin ciki wajan kaltume baa maganaa ji take kamar ta kashe yaran gabadaya.
Lokaci daya aka aurar da Hafsa da Ummi in aka kai Hafsa Zaria ita kuma Ummi a cikin garin take.
Tun tashin Amatullah jinin su bai hadu dana Ammar ba sabida ya kasance mutum ne mai fad'a da zafin gaske ga son girman tsiya kafin kiga hakorin sa a waje zaki jima ita kuma a rayuwa ta tsani mutum Mara fara'a hakan yasa in ta ganshi sai dai ta d'auke kai shi kuma hakan yana bashi haushi sbd shi mutum ne me son a girmama shi a duk inda ka ganshi ka gaishe shi especially in Yana cikin abokan sa,
Ammar da Yasir tare suka yi makaranta tun daga primary har Digree, bayan kammala karatun su Ammar ya fito a cikakken likitan Mata shi Kuma Yasir ya fito a babban lauya me zaman kansa, babu jimawa aka ginawa Ammar katafaran asibiti me zaman kansa babu jimawa aka dibi ma'aikata aka Fara gunadanar da aiki, Ammar yana da ciwo a zuciyar sa bangaren dama na zuciyar sa yayi rami hakan yasa ya dage sai ya karanci likita Dan yywa kansa magani, yaso ya karanci likitan zuciya Amma sai ya tsinci kansa a bangaren Mata.

MASOYA UKUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora