Page 23

67 3 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_



_(True love, intense jealousy & betrayal)_



By
Neat Lady



Not edited🤒


Dedicated to Ummu Nabil😍

Jinjina gare ku:

Fatima Mahmoud
Maman bilal
Amina Lawal Gwarzo
Asin fati
Na'ima Bala
Maman Mubina&Khausar
Fatima Bello

G.G.S.S Fatima Muhammad ina gdya da soyayya a gare ku Allah ya bar zumunci😍🤝🏼





Page 23




........ Abincin dake hannun ta ya fadi kanta ya bugu da hannun kujera tayi Yar kara kadan, nuna ta yayi da yatsa yace, "As from today kika sake ambatar sunan wancan dan iskan a gidan nan wallahi sai na balla ki, kina san sa kenan ko? Shiyasa kika sha abinda zai kawo miki period dan bakya sona ko? Dan kinga ina mararin ki ma yasa kike wani ja min aji wannan bai ishe ki ba harda ambatar sunan sa a gaba na, first and last kar ki sake in Kuma ba haka ba zan nuna miki waye Anwar" ya fada ficewa daga falon.

Da mamaki sosai ta bishi da kallo hannun ta Na kan kuncin ta, me hakan ke nufi kenan? Tun ba'a je ko ina ba ya fara daukar hannu yana Marin ta? Shin wai ita yake so ko kuwa jikin ta Wanda yake korafi akai? Bata da Wanda zai bata amsa wannan tambayar tata wannan dalilin yasa taji abincin ya fice mata akai ta mike kawai ta koma daki ta kwanta lamooo akan gado.


A harabar gidan ya zauna yana fuci gabadaya haushin ta yake ji yayi tsaki ya dauko wayar sa a aljihu, lalaluben number yake har ya gano wacce yake nema ya danna kira ba jima aka dauka.

"Hello" Anwar ya fada murya a kasa.

"Hiiii Baby ykk? Ya amarya?" Wacce ya kira take fada cikin yanga.

"Ina so kizo gida na na mai tama anjima".

"Bada amarya kazo ba?".

"Da ita nazo zaki zo ki tafi ne cikin sirri".

" Sirri? Sabida kayi mata kake cewa zan zo na tafi cikin sirri? Tsoron ta kake kome? To bazan zo ba ka nemi wata."

"Haba Baby kin San dai babu wacce nake ji da ita sama dake in banda haka ma nida nake da amarya ai da kinga bazan nemi ki ba amma na nemo ki ko hakan ya nuna miki matsayin ki a zuciya ta."

Jin hakan ya saka taji dadi a ranta tace, "Okay zan zo" tana gama fada ta kashe wayar.

Murmushi yayi Dan yasan Baby Mery badai kishi ba yanzu sai ta tarwatsa masa gida.




*********


Zaune yake a Airport din yana jiran azo a dauke shi duk ya gaji sai duba agogon hannun sa yake yana tsaki, motar yasir ya hanga yasa ya mike da Sauri yana jan jakar sa Dan burin sa kawai ya Ganshi a gida.

Bude gaban motar yayi ya shiga da murmushi a fuskar sa ya kalli yasir, Yasir yace, "Barka da sauka mutanen Germany."

"Ya kuke ya mutan gidan" Ammar ya tambaya yana zare sim card din Germany daga wayar sa, "lafiya lau kowa yake."

"To masha Allah haka ake so ai" ya fada yana dago kansa.

"I hope dai abinda ake je nema an samu?" Yasir ya tambaye shi hankalin sa na kan titi.

"Tunda kaga na dawo Kasan ai lafiya ta samu".

" Kai Alhamdulillah naji dadin hakan sosai na taya ka murna" Yasir ya fada da murmushi.

MASOYA UKUTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon