*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_By
Neat LadyDedicated to Ummu Nabil😍
Not edited🤒
End🤒🙏🏼
A gurguje🏃🏼♀️🤒
........ Ganin halin da take ciki ya sa hankalin sa ya tashi ya karaso wajan fa sauri ya tsungana yana girgiza fuskar ta amma babu alamun motsi a tare da ita.
"Amatullah dauko mayafin ki muje asibiti" ya fada yana cicci6ar Nana yana fita da ita zuwa inda ya ajjiye mota.
Yana saka ta Amatullah na fito ta shiga suka kunna mota suka tafi a 360, koda suka isa emergency aka wuce da ita aka fara mata taimakom gaggawa har aka samu jinin dake zuba ya tsaya kafin a samu numfashin ta ya dawo Normal.
Amatullah tana cikin dakin Ammar da nurse's mata suke duba ta, sai suka gama sannan ya juyo ya kalli Amatullah ya lumshe ido kawai baice komai ba ya zare handgloves din ya zubar a shara ya fice daga daki.
Ganin ya fita yasa Amatullah tabi bayan sa har ya shiga office, "Ina fatan bata yi miscarriage ba" Amatullah ta tambaye shi tana zare ido.
Ajiyar zuciya tayi ya zauna akan kujera yace, "We lost our baby".
Ya salam shine abinda Amatullah ta fada tana jin babu dadi kamar itace tayi 6arin.
"Gashi ban fito fa waya ba da Na Sanar dasu Mama" Amatullah ta fada murya a sanyaye.
"Na fada musu" ya fada yana mikewa da niyar fitowa daga office din.
Babu jimawa su Mama suka karaso a ganin tana bacci yasa suka samu waje suka zauna.
Sai da akayi kusan 1hour da yi mata allurar ba ta farka ganin ta a asibiti ya saka ta tuno da duk abinda ya faru amma bata nuna ba sabida ganin su Mama a wajan, ganin ta samu lafiya sai da ciwon ciki da ciwon kai da take fama dashi yasa suka fara kokarin komawa gida.
Basu suka bar asibitin ba sai bayan sallar i'sha,Ko a mota babu Wanda ya kula kowa ta tafiya kawai ake yi har aka isa gida, sababbin ma'aikatan da aka kawo sun gyara ko ina Na gidan ciki harda wajan da Nana ta fadi.
Yana rike da hannun ta har dakin ta ya kwantar da ita tare da rife ta da bargo amma baiyi mata magana ba, sai da taga yana kokarin fita sai ta fashe da kuka yana fadin, "Shikenan Na rasa baby na."
Juyowa yayi ya kalle ta yace, "Hakuri zakiyi Allah ne ya baki kuma shi yane ya kaddara haka sai kiyi addu'a Allah ya sake baki wani, ki kwantar da hankalin ki ki daina kuka kinga dai ba lafiya ce dake ba, ki jira ni yanzu zan dawo" daga haka ya bude kofar ya fita ya hau sama dan ya watsa ruwa.
Washe gari.
Karfe goma na safe Aunty Jamila ta sauka a gidan cikin girmamawa suka gaisa da Ammar da yake shirin fita, dakin Nana aka nuna mata ta shiga Nana Na ganin ta ta mike ta fashe da kuka.
Karasowa wjan ta tayi tace, "To meye abin kukan Nana? Murna zakiyi da gani Na ai ban kuka ba."
Zama suka yi a kan gadon Aunty jamila ta kalle ta tace, "Sannu ya jikin naki".
Zata bata amsa aka bude kofa aka shigo, daya daga cikin masu aikin ce ta shigo hannun ta dauke da tray Wanda aka cika shi da kaya ci Dana sha aka ajjiye a gaban Aunty jamila ta juya ta koma.
"Wai garin ya hakan ta kasance ne Nana? Kin san ina Kaduna tun shekaran jiya sai naga wayar Ammar jiya yana Sanar dani kin zame akan steps kin yi bari."

VOUS LISEZ
MASOYA UKU
Roman d'amourta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.