26

73 5 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_



_(True love, intense jealousy and betrayal)_





By
Neat Lady





Not edited🤒




Dedicated to Ummu nabil😍




Page 26






.......... Idan tane ya sauka akan wani gansamemen kato ga uban ciki  ya daga hannu ya mari Anwar, bata gama mamakin sa ba taji yana fadin, "ya mukayi dakai? Ba nace maka kada ka bari wani Abu ya same ta ba?" Ya fada a fusace yana kallan Anwar.


Kallan sa shima yake cike da mamaki amma dake Neman kudi yake yasa ya kwantar da murya yace, "Sorry oga taurin kai gare ta ne babu yadda bana yi da ita akan taci abinci amma ta k'i ci dazu ma kokarin guduwa tayi bata san da security a a gidan ba."


Dauke Kansa yayi daga kallan Anwar ya mayar da kallan sa ga Amatullah da ta zuba masa ido Baki bude tana kallan halittar Allah, murmushi ya saki take bacin ran dake ransa ya kau sabida tozalin da yayi da abar kaunar sa, ganin yana matsowa inda take yasa ta fara jin tsoro amma bata dauke idon ta a Kansa ba.

A gefen gadon ya zauna ya mika hannu zai taba fuskar ta tayi saurin juyar da kai tana k'walalo ido, Dan murmushi yayi irin nasu Na yan duniya kafin yace, "Anwar Na gama dakai yanzu, zaka ga alert anjima da amma Na rage wani Abun a ciki sabida yadda Na baka ita ba haka take yanzu ba, now u can leave" ya fada amma idon sa Na kan Amatullah.


A hankali Anwar ya juya ya fita yana jin wani Abu kamar kishi yana bin jikin sa wannan dalilin ya saka yaji jikin sa yayi bala'in sanyi.


"Cutie you are so beautiful" ya fada yana kanne mata ido daya yana dan matsowa gare ta.

Bata ce komai ba sai bala'in tsoro da ya cika ta gaban ta Na faduwa, "ki tashi kiyi wanka ki shirya kici abinci" ya fada still idon sa a kanta.



Dauke kai tayi daga kansa sai yanzu ta tuna ashe fa Anwar ya sake ta bata da aure kenan ya tabbatar auren ta biyu yanzu za'a fara irga mata aure itama, kuma gata a zaune da wani kato a daki babu auren sa a kanta a matsayin karuwar sa, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba tana tausayin kanta dangane da wannan rayuwar da ta tsinci kanta a ciki.

"Haba cutie meye na kuka kuma" ya fada yana kokarin rungume ta.

Saurin matsawa baya tayi tana kallan sa cike da kyama, ganin hakan yasa ya mike ya fice yana kallan ta.

Da Sauri ta mike zata kulle kofar amma babu Key's din da alama an cire su, da baya ta koma ta zauna ta rike kai da hannu tana rera kuka.

Cikin kuka take fadin, "Wayyo Allah na, Dady, Mama, Yaya, Umma, Yaya Ammar, Yaya Yasir kuzo Ku taimake ni kafin na mutu, zuciya ta zafi take yi sauran kadan ta fashe Dan Allah kuzo Ku tafi dani zan mutu" ta fada tana sake rushewa da kuka kamar anyi albishir da mutuwar ta.

Haka tayi kukan ta koshi ta zauna tana ajiyar zuciya kamar karamar yarinya.

Haka take ta zaune babu ci babu sha babu ba batun wanka sallah kadai ke saka ta tashi daga Inda take zaune itama sallar a zaune takeyi sabida jirin da ke kwasar ta har biyu-biyu take gani.

Gyangyadi ta fara a wajan da take cikin tsoro baccin yake daukar ta tana bude ido har baccin ya dan yi nisa kadan, leko dakin yayi yaga tana cure waje daya a zaune tana bacci a hankali.

Karasowa yayi a hankali yana tafiya cikin sand'a ya zauna a gaban ta yana Kare mata kallo, wutar sha'awar ta ke kara ruruwa a zuciyar sa sai lashe baki yake yana hadiyar yawu, hannu ya kai fuskar ta yana shafawa a hankali cikin kwarewa.

MASOYA UKUTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang