25

67 5 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_


_(True love, intense jealousy & betrayal)_



By
Neat Lady





Not edited🤒



Dedicated to Ummu Nabil😍






Page 25




........... Tabbatarwa tayi idon ta biyu ba mafarki take ba yasa ta fara kalle-kalle kamar mahaukaciya ta mike a guje ta shiga daki tana kuka mai ban tausayi, jikin ta ke bala'in rawa ta manta da wani ciwo dake hannun ta sabida tsabar tashin hankali.


Sai da tayi kukan wanda ake kira kuka kafin tayi shiru tana kallan gefe daya na dakin, "Wannan wacce irin jarabawa nake ciki?  Waye wannan Wanda ya saka Anwar yaci Amana ta bayan tarin kaunar da na nuna masa? Me zanyi mai zan tuna? Wa zan fadawa?" Amatullah ke fadar hakan tana hawaye muryar ta a dashe.

Kamar an tsikare ta tashi ta shiga binciken wayar ta ta ko ina amma babu ita babu alamar ta tun tana ganin abin kamar wasa har ya bata tsoro ta duba ko ina bata ganta ba, jin an turo kofa yasa ta mayar da hankalin ta game shigowa, "Wayar ki kike nema? An fada miki ni sakarai ne da zan bar miki waya a hannun ki? Na dauke wayar ki ba zaki sake amfani da waya ba kuma kinga gidan nan na saka security sosai babu Wanda zai barki ki futa in ma kin futa zaki dawo sabida na zuba police dog's a kofar gidan nan wallahi yayyaga miki fata zasu yi babu abinda ya dame ni, shawara ta rage game shiga rijiya ko ya fada ko ya fasa" yana gama fadar hakan ya juya ya kulle kofar.


Da6as ta zauna a wajan ta rasa kuka zatayi ko ihu? Magana zata yi ko shiru? Salati kawai take a zuciyar ta idon ta a rufe.

Jingina tayi a jikin gadon sai a lokacin ta tuno da ciwon dake hannun ta ta runtse ido ta kalli wajan har yanzu jini yana fitowa, har ta mike da niyar saka dettol a wajan sai kuma ta koma ta zauna dan bata ga amfanin hakan ba a halin yanzu tafi kaunar mutuwar ta fiye da lafiyar ta, tankwashe kafa tayi a kan tayal tayi tagumi ta rasa abinda zata yi.

"Ina ma ban kashe aure na da Yaya Ammar ba da yanzu ina zaune cikin farin ciki da sa6anin yanzu, ina ma ban dawo ga Anwar ba da yanzu ina can cikin kwanciyar hankali, wayyo Allah na shiga uku ni Amatullah, ya Allah ya zuljalalu wal'ikram ka kawo min dauki Allah ka fitar dani daga wannan bala'in da nake ciki" ta karasa fada tana sake rushewa da kuka.




***********

"Me kika gani kika ce haka?" Ammar ya fada yana kallan Nanah dake gefen sa akan kujeru a harabar wani katon gida na alfarma.



"Ka rame da yawa kamar ba kai ba dole nayi tunanin ba lafiya kake ba" Nana ta fada cike da damuwa.

Murmushi yayi dan ya kwantar Mata da hankali yace, "tunanin ke ne yake sani rama" ya fada yana kallan fuskar ta.

Dan murmushi tayi ta kawar dakai tace, "Ka fada ne dai kawai amma ai ban kai matsayin kayi rama a kai na ba."

"Haka kike gani kenan?."

"Hakan ne ma ai".


Dan murmushi kawai yayi cikin dauriya yake maganar da har ga Allah ya gaji kawai dan ya faranta mata yake yi, " To shikenan tunda baki yadda ba ki fada min meye ya sani rama a tunanin ki."

"Tunanin tsohuwar matar ka mana" ta fada tana dan hade fuska cike da kishi.


Hade rai yayi kamar bashi bane ya gama murmushi yanzu yace, "Mun taba fada dake?."

Girgiza kai tayi Alamun A'a ganin yadda yanayin sa ta canja lokaci daya, "to kar ki sake yi min wannan maganar Indai ba so kike raina ya baci ba kar ki sake."


MASOYA UKUKde žijí příběhy. Začni objevovat