Page 29

78 5 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_



_(True love, intense jealousy& betrayal)_



By
Neat Lady




Dedicated to Ummu nabil😍


Not edited🤒


Page 29



......... Salati kawai suke cikin tashin hankali babu Wanda bai dauka ranta ne zai bar gangar jikin ta ba, karasawar Ammar wajan ya duba cikin alluran dake wajan ya samo ta bacci ya bude yayi mata a jijiya bacci ya sake dauke ta.

Ajiyar zuciya yayi ya kalli su Yaya dasu ke tsaye cirko-cirko suna kallan ta ya dauke kai ya mayar da kallan sa ga Nana dake inda ya barta da alama babu Wanda ya kula da itama.


"Ammar bata samu tab'in hankali ba kuwa?" Dady ya tambaya a sanyaye.

"Banjin hakan gaskiya sai dai hakan ya faru da itane tana tunawa duk a tunanin ta a can Inda abin ya faru take, tayi bacci yanzu zuwa anjima zata farka ya kamata a zauna a kusa da ita kar ayi nisa dan da ta farka ta ganku."

Girgiza kai sukayi suna mamakin me ya faru da ita haka har ya kai ta ga irin wannan firgitar, sai a lokacin Mama ta juya ta ga Nana tsaye tace,"Nana tare kuke Ashe? Shigo mana kya tsaya anan kamar bakuwa."

Duk suka juyo da kallan su gare ta suka gaisa cikin fara'a kafin Yaya tace, "Yo ai duk laifin sane ya barta a tsaye ko wajan zama bai bata ba" ta fada tana hararar sa.

Ita dai Nana murmushi take sabida taji dadin yadda suka karbe ta, suna zaune anyi shiru babu mai magana har kusan minti goma kafin Mama tace, "Ammar ya kamata kuje gida fa dare yayi".

Maida kallan sa yayi ga Nana kafin yace, " To Mama " yana fadar hakan ya karasowa Inda Nana take suka yi musu sallama suka tafi.

Ko a mota duk yadda yaso ya kawar da tunanin Amatullah kasawa yayi hakan yasa yayi shiru suna tafiya ita kanta ta tausayawa Amatullah din duk da bata ga fuskar ta ba amma yadda taji tana surutai yasa jikin ta yayi sanyi sosai har suka karasa gida.

Bayan sun koma Ammar bai kyale Nana ta kwana da damuwa ba sai da yasan yadda yayi ya saka ta farin ciki a daren.

Amatullah bata farka ba sai misalin karfe sha daya na safe a lokacin duk sun hallara a asibitin, a hankali take bude ido bata sauke shi akan kowa ba sai Mama dake zaune gefen ta tana lazumi dan idar da sallar walahar ta kenan.

Zubawa Mama ido tayi tana so ta tantance ita dince ko kuwa gizo take mata, a hankali ta furta, "Mama" da Sauri kowa ya dago kai cikin farin ciki aka karaso Inda take kowa yana jera Mata sannu.

Likita ne ya shigo ya kalle ta yace, "Yanzu me yake damun ki?".

Cikin ta ta nuna da kai tana lumshe ido, " Suma zasu daina amma sai kina cin abinci kina kuma shan magani " ita dai bata amsa ba dan ko magana tayi har cikin ta take ji.

Fita likitan yayi Mama ta karaso kusa da ita ta riko hannun ta itama ta matse na Mama gam ta fashe da kuka, rarrashin ta Mama tayi sannan tayi shiru Aunty Hafsa ta karaso wajan tace, "Amatullah sannu kinji Allah ya baki lafiya".

Daga kai tayi kawai tana share hawaye, dake asibitin na kudi ne bandaki ta shiga akwai toothpaste ta dauko da sabon brush a ledar sa ta bude ta hado da ruwa a roba ta fito wajan Amatullah.


Zama tayi a gefen gadon tace, " Amatullah gwara ki wanke bakin ki kici abinci kina jin dai abinda Dr yace".

Yaya dake wajan tace," Gaskiya ne gwara kici abinci, ku taimaka mata ta tashi."


MASOYA UKUOnde histórias criam vida. Descubra agora