*MASOYA UKU*
_(The three lovers)__(True love, intense jealousy & betrayal.)_
By
Neat LadyPage 10
Not edited🤙🏻
..........fita yayi zuciyar sa fes da Jin ta hak'ura zata aure shi duk da Bata so din shi yasan ta yarda zai saka ta taso hakan yasa Yana tafiya tana murmushi.
Washe gari amatullah da wuri ta tashi Dan yau take da final paper hakan yasa da sauri-sauri take gudanar da abinda zatayi, shiryawa tayi cikin uniform din ta ya dauki jaka da wayar ta ta fito da sauri, Bata tsaya bin takan Mama Bata kawai ta fito, waya ta Kira Rahma anan take sanar da ita ai ita tana school ma, kashewa tayi tare da karasowa parking space din gidan.
Mai gadi ta kalla tace, "wai Ina Bala ne?"Mai gadi ya Bata amsa da fadin, "tun dazu ya fita bai dawo ba" dafe Kai tayi kawai ta fito bakin titi Dan tasan in ta tsaya jiran na gidan sarki Bata lkc zata yi gwara ta hau Keke napep.
Kusa mintin ta biyar a tsaye bb mota, dafe Kai tayi tana duba agogon hannun ta tana da exam karfe goma gashi yanzu har Tara da rabi bata tafi bama.
Har motar ta wuce ta dawo ya sauke glass ya kalle ta yace, "Shigo". Ba musu ta bude gaba ta shiga Dan neman taimako take a lokacin.
Tafiya suka Fara yi babu Wanda yake magana sai sautin Ac da yake fita, dakyar ta lalubo magana tace, "Ina kwana". Dago Kai yayi ya kalle ta ya kau da Kai yace, "Lafiya, karfe nawa kike da exam din?".
"Karfe 10" ta amsa tana sunkuyar da Kai, kallan agogon hannun sa yayi yace, "Shine Kuma baki fito ba sai yanzu?". Rau-rau tayi da Ido kamar zatayi Kuka tace, "Na rasa Wanda zai kaini ne shine na fito neman Keke napep."
Kallan ta yayi yace, "Kaf fad'in gidan kice an rasa Wanda zai kaiki makaranta."
Kallan sa itama tayi suka hada Ido ta dauke Kai tace, "basa nan ne duka sun fita Ni Kuma gashi Ina sauri." Dauke Kai yayi shima ya sake fad'in, "meyasa baki shiga cikin gida ba kin nemi Ahmad ba?."
Cike da kosawa tace, "Sauri nake ne shiyasa" ta fada kamar zatayi kuka. Hakan ya saka ya kalle ta daman fuskar sa had'e take babu fara'a cikin ta, ya sake cewa, "first and last kar na sake Jin labarin kin fito kince Zaki hau kake napep, kinji".
Ta amsa da to tana mamakin yadda yadda saki baki suke Hira haka duk da fuskar sa daure take, ita dai burin ta kawai ta ganta a school.
Bai sake ce mata komai ba har suka karasa makarantar, har zata bud'e sai ta juyo ta kalle shi tace, "Nagode" sannan ta bud'e motar ta fita da sauri.
Ajiyar zuciya yayi yaja motar ta ya nufi asibiti.
Isar sa ya fito daga motar tare da bude bayan motar ya dauki jakar sa, har yayi gaba sai ya dawo ya bude motar inda Amatullah ta zauna Yana neman face mask din sa, ganin waya a wajan ya saka ya dauka ya kalle ta ko ba'a fada ba yasan wayar Amatullah ce, rufe motar yayi ya nufi office.
Bayan sun fito daga exams Amatullah ta duba jakar ta baga waya ba hakan ya ta dafe kai tace, "wayyo Allah" Rahma ta kalle ta tace, "Qalau kike wayyo?". Yatsine fuska tayi tace, "Waya ta na manta a motar Yaya Ammar wllahi."
Tsaki tayi tace, "Shine kike wani wayyo Allah in Mun koma gida in ya dawo daga asibiti sai muje ki karb'o, ke ni ba wannan ba, kin fahinci page 10 na handout din community health?".
Amatullah tace, "Ina fa tun jiya nake maimaitawa Amma wallahi na kasa ganewa gashi gobe zamuyi sa ni duk jiki na yayi sanyi." Rahma tace, "Ai kawai in Mun koma kizo muje wajan Yaya Ammar ya Koya mana kin san halin malamin nan Kuma kin san babban course ne Dole mu iya."

YOU ARE READING
MASOYA UKU
Romanceta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.