page 5

88 4 0
                                    

*MASOYA UKU
_(The three lovers)_


_(True love, intense jealousy & betrayal.)_


Page 5

Not edited🤙🏻

........... Isar ta cikin gidan ta k'arasa inda suke zama ayi karatu anan ta tarar da Malam Bello har ya k'araso, gaishe Shi tayi sannan ta koma gefe ta zauna ta cigaba da biya karatun ta Dan yau ita zata bada hadda.

Bayan jimawa sauran suka hallara a wajan kowa ya zauna aka fara karin alkur'ani Mai girma kamar Koda ya yaushe, bayan an kammala K'arin Amatullah ta mik'e tsaye ta fara rairo kira'a Mai dadin sauraro cikin suratul Maryam, kowa yayi shiru Yana sauraron ta karatun na ratsa jikin su, Ammar dake zaune a inda ya Saba zama indai zasu yi karatu jinginar da kansa yayi jikin kujerar da yake zaune ya lumshe ido sautin muryar ta na ratsa ko wanne sassa na jikin sa, shaukin kaunar tane yake Kara fizgar sa wani irin yammmmm yake ji a jikin tun daga dan yatsan kafar sa har kwakwalwar sa.

Sa da ta Kai inda zata tsaya sannan ta tsaya ta samu waje ta zauna, kabbara akayi mata dan karatun ya biyu ko gyara daya Bata samu ba shiyasa Malam Bello yake alfahari da ita.

Gab da magariba suka kammala karatun kowa ya watse daga wajan, Amatullah da Rahma suka jera suna tafiya har suka kusa isowa kofar part din Umma, Rahma ta kalli Amatullah da hankalin ta ke wani wajan tace, "Nikam wai me yake damun kine? Tun d'azu na lura da bakya cikin walwala."

Ajiyar zuciya tayi tace,"Wallahi bestie ina bala'in tausayawa Anwar baki ga halin da ya shiga ba lkcn dana sanar dashi za'ayi aure na Rahma wallahi yana sona sosai Nima Kuma haka" ta fada idon ta na cikowa da kwallah.

Dafa ta tayi tace, "Abinda na Saba fada Miki shi zan maimaita Miki addu'a zaki cigaba da yi in Yaya Ammar ba alkairi bane a wajan ki Allah zai canja miki shi ki kwantar da hankalin ki kinji."

Share hawayen ta tayi suka cigaba da tafiya.

A parlour suka zauna Ahmad dake fitowa daga dakin Umma ta kalli Amatullah yace, "A'a matar Yaya irin wannan karatu haka nifa da na shigo na dauka bakin larabawa muka yi Ashe Ashe kece." Dariya tayi tace, "Kai kam Yaya Ahmad baka rabo da tsokana wallahi." Waje ya samu ya zauna yace ,"Babu batun tsokana fa Amatullah Allah da gaske kira'ar ki na da Dadi sosai Allah ya Kara basira."

Murmushi tayi tace, "Amin to nagode, Ina Umma ne?". "Tana ciki ita da Yaya Ammar nee yanzu zasu fito."

Jin an ambaci sunan sa yasa ta mik'e da sauri daga wajan tace, "Shikenan kawai ka gaishe ta in ta fito bara na lek'a wajan Aunty mu gaisa" ta fada tana k'ok'arin barin wajan.

Rahma tace, "Ki Bari ta fito Mana muyi sallah Sai mu tafi can gidan sai na kwana ma a can." Amatullah ta girgiza Kai tace, "Kya tawo daga baya nikam sauri nake yanzu".

"Kar ki sake ki fita daga Nan sai an idar da sallah" Ammar ya fad'a lokacin da yake fitowa daga dakin Umma.

Cak ta tsaya ta runtse Ido har ga Allah bata San sake had'a Ido dashi wata mahaukaciyar tsanar sace take bin ko Ina na jikin ta hakn ya saka bata juyo ba Kuma bata cigaba da tafiya ba, kallon Ahmad yayi yace, "Kai kuma kana ji ana Kira baka tashi ka tafi masallaci ba Dole Suma suk'i tashi ai, babban banza, Yana Gama fad'ar ya fice daga parlourn fuskar Nan a had'e.

Da harara ta bishi zuciyar ta na mata K'una ta samu waje kawai ta zauna tare da dafe Kai, Ahmad kuwa murmushi yayi ya fita daga parlourn.

Sallah suka yi sannan suke je suka gaisa da Umma suka fito tare, Part din Aunty suka nufa fuskar Amatullah a had'e dan har lokacin haushin Ammar take ji. Da sallama suka shiga part din Aunty cike da fara'a Humayra ta mike tana tana fadin oyoyo matar Yaya.

Murmushi tayi suka nemi waje suka zauna ta kalli Humayra tace, "Ina Auntyn?".

Humayra tace, "Tana ciki yanzu zata fito". Sumayya dake gefe ta had'e Rai Bata ko kallon inda su Rahma suke Danna wayar ta kawai take yi Suma basu kalle ta Dan sun San ba mutunci gare ta ba.

Da fara'a Aunty ta shigo parlour suka gaisa tace ta gaida Mama da Yaya suka yi sallama suka fito.

Mik'ewa Humayra tayi ta shiga d'aki hakan yasa sumayya ta kalli Mahaifiyar ta tace, "yanzu Dan Allah Aunty meye kike wani sakar masu fuska haka? Kinga wannan Amatullah din na tsane ta kamar yadda na tsani mutuwa ta Aunty gashi kowa gidan Nan sonta yake basu da magana Sai ta bikin ta da Ammar."

Murmushi tayi tace, "Sumayya ke yarinya ce ni nasan duk abinda nake k'ullawa babu ta yarda za'ayi na Bari auren Nan yayu Koda yayu baza ta taba samun kwanciyar hankali ba a cikin gidan nan sai ta fita da k'afar ta wallahi dani suke zancen ai."

"Yawwa Aunty amma naji dad'in wannan Shirin naki Kinga waccan Humayra Sam Bata da hankali tai ta wani yi musu dariya wai ita taga y'an uwan ta." Tsaki Aunty tayi tace, "Duk ki kyale ni dasu zanyi maganin su baki daya."

A hanyar su ta tafiya gidan su Amatullah Rahma ta kalle ta tace, "wai me yake damun Sumayya ne?."

Amatullah tayi tsaki tace, "me yake damun ta Banda hauka da rashin tunani Ni bani da lkcn ta kema kin San da haka tayi duk abinda taga zata iya dai-dai ne a wajan ta Bai Dame ni ba ni."

Allah ya kyauta Rahma tace suka cigaba da tafiyar su, Koda suka Isa gidan Part din Yaya suka wuce anan suka yi sallar Isha suka cigaba da kwasar Hira wajan Yaya.

Sallamar Ammar ce tasa Amatullah ta tsayar da dariyar da take yi ta kauda fuska, Yaya ta washe baki tace, " A'a manyan gari yau Kaine a wajen nawa?" B'ata Rai tayi ta sake cewa, "Eh Dole Daman ka manta Dani Mana tunda kayi amarya yanzu" ta fada haka tana kallon Amatullah.

Murmushi Mai tsada yayi har hakoran sa suka baiyana yace, " Ni na Isa nayi haka kawai dai Allah bai kawo ni bane sai yau" ya fad'a Yana k'arasowa cikin parlourn.

Zaman sa kenan Yasir shima ya shigo cike da fara'a Yaya tace, "Kace tare kuke ma Kai yau naji dad'in zuwan ku sosai, maraban ku." Zama shima Yayi suka gaisa cikin nishadi da farin ciki.

Amatullah ta mik'e ta kalli Yaya tace, "Yaya bara muje mu kwanta muna da lecture gobe da safe" ta fada tana k'ok:arin barin inda take, Yaya tace, "Babu wata lacca da kike da ita kawai dai kice dan angon naki yazo ne Zaki maza ki gudu kije ki Masa kwalliya ko?".

Zaro Ido tayi tace, "Wacce kwalliya Kuma Yaya Ni bacci zanyi ma, Kuma ba lacca ake cewa ba lecture ake cewa in turawa suka ji kince lacca sai sun bindige ki" ta fada cike da zolaya. Dariya Yaya da Yasir suka yi Banda Ammar da yake satar kallon ta ta gefen Ido.

Yaya tace, "To uwar yan iyayi naji, Amma dai Kar ki kwanta ki bari Zaku dan yauta da angon naki". Shagwab'e fuska tayi tace, "Nidai gaskia bacci nake ji Dan Allah kice na kwanta,"

Yasir yace, "Tunda akace Kar ki kwanta Kar ki kwanta din in ba so kike ranki ya b'aci ba Kuma".

Ammar dake zaune a gefe yace, "jeki ki kwanta kin cika Mana kunne" ya fada kamar bashi yayi maganar ba hankalin sa na kan wayar sa.

Kamar jira take ta bud'e k'ofar ta fita tana hararar sa, ganin Haka Rahma ma ta bud'e kofar tabi bayan ta.

Ajjiye wayar yayi ya sauke ajjiyar zuciya ya fara matse Yan yatsun hannun da suna bada sautin kassss kamar yadda ya saba, Yaya ta kalle shi cike da tausayawa tace, "Ammaru wai har yaushe zaka Kai kana b'oye abinda ke ranka ne? Meyasa baza ka fito ka Fadi abinda ke ranka ba ko kaji sauki a zuciyar ka, kuma Kafi kowa sanin yadda kake ji in ciwon ka ya tashi akan me zaka dinga takurawa kanka ne."

Yasir yace, "Abinda muka tattauna kenan d'azu amma Sam yaki wai shi lallai sai dai ayi auren a haka baya so ya nuna mata Yana sonta ban San meyasa ba."

Ammar ya kalle su yace, "Kar ku damu babu komai Ni bana son maganar ma".

Yaya tace, "To ai shikenan Allah ya shige Mana gaba tunda haka ka zab'a uban yan tsari." ta fada tana sakar masa harara, dariya sukayi Suma suka amsa da amin.

MASOYA UKUWhere stories live. Discover now