page 8

81 4 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lovers)_

_(True love, intense jealousy & betrayal.)_


Page 8


Not edited🤙🏻

...........Bayan an idar da sallar asuba kamar kullum Mai martaba Sarki shida aminin sa sun jero suna tafiya Daddy ya duba inda Ammar ke zama yace, "Aa wai ni kam yau Ina Ammar nee ban ganshi ba?".

Mai martaba Sarki shima yace, "Abinda nake tunani a raina kenan nima, Anya qalau yake kuwa Dan babu abinda yake Hana shi fitowa sallah." Daddy ya Kalli gefen sa yace, "Ahmad maza keja dakin Ammar kaga lafiya yake bai fito sallah ba, Allah yasa dai ba ciwon sa bane ya tashi."


Ahmad ya nufi part din Ammar da sallama ya shiga d'akin ya hango shi can k'arshen gado yana rawar sanyi, da sauri ya k'arasa gare shi yace, "Yaya Ammar lafiya  me ya same ka? Ko ciwon Kane ya tashi?"

Zame blanket din yayi ya dago kai murya a dashe yace, "Ahmad bani ruwa da sauri". Da sauri Ahmad ya dauko masa ruwa ya bashi, Dakyar ya mike zaune ya bude jarkar ruwan Yana Sha yana runtse ido.

Ahmad yace, "Haba Yaya yanzu baka da lafiya shine babu Wanda ka sanarwa?." Murya can kasa yace, "Kaga Ahmad bana son magana Kuma bana so kowa yasan da maganar rashin lfyr nan." Cike da mamaki Ahmad ya kalle shi yace, "Au rashin lfyr ma abin b'oyewa ne? Bayan kasa yadda kake Shan wahala idan ciwon ka ya tashi."

Banza yayi masa Baice komai ba ya maida kansa ya kwanta.

Fita Ahmad yayi ya koma inda ya bar su daddy.

Daddy yace, "Ya akayi Ahmad lfy yake?". Ahmad yace, "Baya jin Dadi ne shiyasa bai iya fitowa ba Amma Yanzu yasha magani ya kwanta."

Daddy yace, "To madallah Allah ya bashi lfy, Amma gsky bashi da lfy sosai tunda har ya kasa fitowa sallah."

Tafiya suka cigaba da yi suna Hira shida aminin sa.

Da misalin karfe Sha daya na safe Ammar ya farka da salati a bakin sa, mik'ewa yayi Dakyar duk da yaji saukin ciwon kan dana kirjin ya shiga band'aki ya watsa ruwa hade da dauro alwala, a bakin mirror ya daure da rigar wanka gashin jikin sa ya kwanta sai digar ruwa yake, lumshe Ido yayi can ya bude ido ya dauko body lotion Mai kamshin gaske ya shafe jikin sa, body spray ya dauk'o ya feshe ko Ina na jikin sa Nan take dakin ya dau kamshi, ajiyar zuciya yayi ya mike ya nufi jikin wadrop ya bude ya zubawa kayan nasa Ido, wani blue din wando ya dauko hade da farar riga ya ajjiye a kan mirror, bbu bata lokaci ya shirya ya tsaya gaban mirror ya dauki perfume after dressing ya fesa a jikin sa, sallaya ya shimfida ya tayar da sallar walaha kamar kullum bayan ya idar yayi lazami ya mike tsaye.

Lokaci d'aya maganar Amatullah ta Fad'o Masa a rai, runtse ido yayi Nan take idon sa ya kada ya koma ja, da baya ya koma ya zauna a bakin gado ya dafe Kai,

Turo kofar da akayi yasaya dago Kai ya Kalli Mai shigowa, Umma ce ta shigo ganin haka yasa ya mike ya durkusa har kasa yace, "Umma barka da safiya."

"Barkan ka? Meya same Kane haka ka fada lokaci daya? Kodai ciwon Kane? Mikewa tsaye yayi yace, "ciwon Kaine Umma ba yadda kuke tunani bane ba"

Umma tace, "Badai Wanda ka Saba yi bane ba?". Daga Mata Kai yayi yace, "Bashi bane ba in shine ai ynz ban tashi ba."

"Haka ne sannu, Allah ya Kara lafiya" tana gama fadar haka ta juya ta fice daga dakin.

Komawa yayi ya zauna Jim kadan ya mik:e kamar an mintsene shi ya dau waya ya fita.

Dake ranar Zaman fada ce hakan ya saka ya nufi fada ya Kai gaisuwa a hanya ya hadu da Aunty suka gaisa ya fita daga gidan.

MASOYA UKUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora