page 24

66 3 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_



_(True love, intense jealousy & betrayal)_



By
Neat Lady





Not edited🤒



Dedicated to Ummu nabil😍






_Ina ganin sakon godiya da addu'ar Ku nagode sosai Allah ya bar kauna._


Ummu nabil fans grp & the three lover's fans ina mika sakon gdy a gare Ku gabadaya Allah ya bar kauna.😍





Page 24




.........Fadawa kan gado Amatullah tayi ta saki kuka mai ban tausayi da kunar raii, magana take a zuciyar ta tana fadin, _Ni Amatullah yau nice nake auran mazinaci abinda Nafi tsana a rayuwa ta kenan na tsani zina na tsani mai aikata ta Amma yau nice nake zaune waje daya dashi har yake taba jiki na._ dukan katifar take ta na kuka a fili tace, "Na shiga uku in Amatullah wacce masifa ce wannan ke bibiya ta? Auren da bai wuce kwana goma ba nayi karo da matsalar da bazan iya jura ba, Allah ka kawo min dauki" ta fada cikin kuka sosai.

Tun tana kukan me sauti har ta koma yin na kurame, ganin kukan bazai mata amfanin komai ba yasa ta mike ta dauro alwala ta Tayar da sallah tana yi tana hawaye.



Anwar kuwa juya shi kawai take tana sarrafa shi da salo kala-kala Wanda bata tab'a yi masa ba, ya fice daga hankalin sa tana surutai cikin karaji ba tare da ya sani ba,abinka da dare Amatullah tana sallah ta jiyo yadda yake ihun dadi yana surutai, faduwa tayi akan sallayar ta cure waje daya ta toshe kunnen ta ta boye kanta a tsakanin guiwar ta amma bata daina ji ba.

Kamar zararriya ta mike tana kalle-kalle wajan TV ta nufa ta kunna ta kawai tashar Saudia ta kure volume, a lokacin an saka kira'ar mahir cikin suratul tauba, gefe ta koma ta zauna tana zare ido tana ajiyar zuciya.

_ya zanyi? Wanne mataki zan dauka? Wa zan fadawa matsala ta ko naji dadi?_ amsa babu hakan yasa ta sake fashewa da kuka har da shashsheka.

Karatun alkur'anin ne ya fara ratsa ta sai ta dauko alkur'ani ta nemi dai-dai Inda yake tana bi a hankali har taji zuciyar ta na sanyi ta dinga ajiyar zuciya.

Bata an kara ba sai jin kiran assalatu tayi cikin mamakin saurin lokacin ta rage sautin karatun a lokacin har an fita daga suratul  Yusuf, alwala ta sake yi ta tayar da sallar asuba.

Bayan ta idar tayi lazumi tare da azkar har gari yayi haske sannan ta mike ta kwanta, duk yadda take jin baccin amma ta kasa idon ta kyam kamar ba kwanan zaune tayi ba, haka ta dinga juyi da ta rife ido Anwar take gani shida Karuwar sa sai ta daina rifewa ta barshi a bude hawaye na yawo a idon ta.


Su kuwa basu San ma bata yi ba Dan kwana Baby tayi a gidan Dan kawai ta bakantawa Amatullah yasa ta dage tana rikita shi, baccin asara ya dauke su babu sallah balle salati har bayan sha daya na safe.

Shine ya fara bude ido ya ganshi a kwance babu komai a jikin sa gefe kuma ga mace ta juya masa baya itama babu komai jikin ta, sai a lokacin komai ya fara dawo masa ya zare ido ya diro daga kan gadon ta dauki gajeran wando ya saka ya fice da sauri.


Tana kwance kamar dazu ta kasa tashi tayi ko wanka ma balle batun abinci kuma, a mutukar sanyaye ya shigo ya karasa kan gadon ya zauna yace, "I'm sorry nasan nayi miki laifi amma ki yafe min rashin tsarkin da Baki dashi shine ya jani na aikata hakan badan naso ba, kar ki dauka halayya tace haka jiya na fara shima kuma na kai karshe wajan bukatar ki na rasa yadda zanyi shiyasa amma ki yafe min bazan sake ba".

MASOYA UKUWhere stories live. Discover now