Page 33

92 5 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_


_{True love, intense jealousy & betrayal}_



By
Neat Lady



Dedicated to Ummu nabil😍


_Kowa ya rude ya rikice🤣 ko ina na zaga naji ana dan Allah kar Ammar ya sake ta, gaskiya jiya nasha comments na kuma sha addu'a nagode Allah ya kara zumunci._🥰🥰



Not edited🤒


Page 33




......."Mama kiyi hakuri bazan iya sakin ta ba" ya fada kansa a sunkuye.

"Ashe ta fini a wajan ka ban sani ba? Lokacin da ita tace ka sake ta sai ka sake ta amma ni nace ka sake ta kaki ko? Wannan shine matsayin uwa da ka bani?" Mama ta sake fada cikin fada da daga murya.

"Nima kenan baka bani matsayin uba ba ka nuna min yau ban isa da kai ba ko?"Dady dake gefe shima ya fada cikin Bacin rai.

Dafe kai Ammar yayi ya rasa abin fada sun saka shi a tsaka mai wuya ya rasa me zaice dakyar ya iya yace, "ba haka bane ba Dady wallahi kun wuce yadda kuke tunani a waje na na dauke Ku kamar Umma da Abba haka kuke a waje na amma wannan hukuncin yayi min tsauri bazan iya ba dan Allah Ku yafe ni Ku kuma gafarce ni dan Allah" ya fada kamar zaiyi kuka.

"Kamar yadda kuka isa da shi haka na isa daku gabadayan ku dan haka ina baku umarnin Ku bar wannan maganar Ammar bazai saki matar sa ba" Yaya ta fada daga bakin kofa rai a bace itama.

Jin muryar Yaya yasa suka juya suna kallan ta Dady yace, "Yaya kin San laifin da yarinyar nan ta aikata kuwa? Ashe sakin da akayi mata yace mana lafiya ce bashi da ita Ashe ita ta saka yayi hakan? Lokacin da yace mana an sace ta Ashe guduwa tayi? Yaya wacce tayi wannan me take nuna mana kenan bamu isa da ita ba bamu isa mu bata umarni tabi ba kuma ta nuna mana saurayi yafi mu kuma kice mu kyale ta Yaya? Tunda bata San Ammar din gwara ya sake ta kawai taje ta zauna da Wanda take so wanda ya fimu" ya fada cikin kasa da murya.

"Duka naji wannan bazai saka Ku saka yaro ya saki matar sa ba kuma wannan maganar a barta a nan wajan bana so su Mariya suji wannan labarin ina nufin maganar ta tsaya iya nan kar Ku kuskura naji wani ya sake Tayar da zancen nan, abinda ya wuce ya riga da ya wuce kuskure ne tayi Ku hukunta ta ta wani 6angaren amma ba ta hanyar raba ta da mijin ta ba, wannan tsakanin tane da mijin ta ruwan sa ya kyale ta ruwan sa kar ya kyale ta, ta kalli Ammar tace, "Wuce kayi tafiyar ka, ke kuma ki biyo ni" ta fada tana barin wajan.

A fusace Mama ta bar dakin haka ma Dady, jiki a sanyaye Ammar ya fita shima, sum-sum Amatullah ta mike tana rike kai ta nufi 6angaren Yaya.

A sanyaye Amatullah ta karasa falon Yaya ta samu waje ta zauna Yaya ta kalle ta tare da mika mata ruwa tace, "Karbi kisha" ba musu ta karba tasha tana sauke numfashi irin na Wanda yaci kuka ya koshi.

"Amatullah naji abinda kika aikata ban hana Ammar ya sake ki dan wai kinyi dai-dai bane sai dan na hana sabida sakin shi zaifi cutarwa ba ke ba, kinyi kuskure waye ya fada miki ana biyewa san zuciya? Waye ya fada miki ana bin shawarar zuciya? Ni nasan a lokacin auren Ku na farko dashi bashi kike so ba shiyasa lokacin da akace an sace ki din nan ban yarda ba kawai nayi shiru ne sabida furucin mahaifin ki akan ki."

"Lokacin da akayi auren na dauka zaki nutsu sabida nasihan da akayi miki Ashe ba haka bane ba a abinda kike shiryawa shi kuma ya biye miki sabida kawai ya faran ta miki rai baya San Bacin ranki sai ya fadi dalilin da babu Wanda zaiga laifin sa, sai gashi kin auri Wanda kika fito dan shi ya wulakanta ki ya nuna miki shi bama sanki yake ba kudi sun fiki, na tabbata da iya wannan aka barki nasan kinyi nadama akan hakan domin kin banbance meye so meye kuma yaudara da cin amana, dole ran iyayen ki ya baci Amatullah in badan nasan San da ammar yake miki ba ko wallahi da ni da kaina zance ya sake ki amma nasan in nayi hakan shi zai cutar ba ke ba."

MASOYA UKUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora