Page 34

115 4 1
                                        

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_

_{True love, intense jealousy & betrayal}_



By
Neat Lady



Dedicated to Ummu Nabil🥰


Not edited🤒



Page 34



..........Kamar yadda ya fada haka akayi cikin kwanaki an gama zuba komai Na sabon gidan komai iri daya akayi ba'a banbanta komai ba hatta kayan kitchen dady ne ya zuba.

      Ana eh gobe zasu tare Nana Na zaune ta zabga uban tagumi ba komai take hangowa ba sai yadda gobe zata kasance a wajan ta, yana zaune gefen ta yana kallan ta ya kuma San abinda take tunani sai yaji babu dadi a ransa ko kadan baya so ya ganta cikin damuwa yace, "Nana tunanin me kike yi haka?".

Cire hannun ta tayi daga tagumin da tayi Tace, " Gobe nake tunawa".

"Meyasa kike tunanin gobe?".

"Sabida ban san a yadda zata kasance min ba" ta fada murya a sanyaye.

Mikewa yayi yace, "tashi ki raka ni unguwa" ya fada yana kallan ta.

Ba musu ta mike ta saka hijjab suka fito ya kunna mota ta Shiga suka fita daga gidan, yawo kawai suka dinga yi a gari suje nan suje can kawai dan ya sata farin ciki, ai kuwa taji dadin yanayin har zuciyar ta bata boye masa ba ko a fuska.

Hadari ne ya hado sosai gari yayi baki ganin haka Amatullah dake zaune a gidan Aunty Nafisa ta mike tace, "Aunty hadari ya hado sosai gwara Na wuce kawai kya karasa min bayanin a waya".

" to ai baza'a zo daukar ki ba" Aunty Nafisa ta fada.

"Na hau napep kawai Na karasa" tana fada tana ficewa da sauri-sauri gudu-gudu.

Sosai iska take kadawa kura Na tashi Amatullah Na tsaye a kan titi tana jiran abun hawa, ruwa mai karfi aka fara maimako ta koma sai ta cigaba da tsayawa a kan titin.


Har ya gota sai kuma ya tsaya yayi baya yazo dai-dai Inda take, ganin hakan yasa Amatullah bata rai sosai ta juyar da kai tana tsaki, sauke glass din motar akayi fuska ba walwala yace, "Baza ki shigo bane ba" jin muryar Wanda yayi magana yasa tayi saurin juyawa ta kalle shi ta zaro ido tana goge ruwan fuskar ta ai da sauri ta bude bayan motar ta shiga.

Kasa tayi da kanta tana sauraren fadan sa da zai biyo baya dan ita bata lura da Nana bama gabadaya kawai hannun tane ya kai kofar baya ta bude ta Shiga kawai.

"Bakya jin magana ko? Ke wai kunnen kashi gare ki ne? Uban ma me kikeyi anan? Daga ina kike? Tsaywar me kike yi a kan titi ana ruwa?" Yaya Ammar ya fada cikin fada.

Kanta a kasa har lokacin cikin shagwabar tace, "Gidan Aunty Nafisa naje fa tun safe nake a gidan."

"Shine ba zaka ki iya jira ruwan ya dauke ki fito ba? Ban ma ce miki ki daina hawa nappep ba?."

Kamar zatayi kuka tace, "To Na kira wayar su taki Shiga kuma ga hadari shiyasa Na fito ."

Kwafa yayi kawai ya rage a.c motar dn yasan yanzu zata fara rawar sanyi, cikin lokaci kadan zazzabi ya rife ta sosai ta kwantar da kanta tayi shiru.

"Zazzabi ko?" Ya tambaya yana kallan ta ta mirror.

Daga kai kawai tayi alamun eh kawai bata ce komai, tsaki ya kuma yi yace, "baki san ciwon kanki ba daman ai".

" Sannu Amatullah " Nana ta fada a hankali.

Saurin dagowa tayi ta kalle ta suka hada ido ko Wacce kirjin ta ya buga Amatullah ta daga mata kai kawai dan ita bata san tana cikin motar ba.

MASOYA UKUCerita yang bikin terobses. Temukan sekarang