page 4

91 5 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lovers)_


_(True love, intense jealousy & betrayal.)_

_The three lovers dai shine Masoya uku, na mayar dashi da Hausa ne sabida akwai Wanda suke san karantawa in suka ga sunan da english sai su dauka english novel, wasu kuma suna san littafin amma basu san sunan sa ba shiyasa na mayar dashi da hausa._


page 4



Not edited🤙🏻

............. Zuba mata ido yayi cike da zargi yace, "What are u doing here?". Juyawa tayi taga dai Anwar ya bar wajan tayi ajiyar zuciya ta juyo ta kalle shi tace, "friend d'ina ce zata zo daman zamu anan sai mu k'arasa gidan to tace ta fasa k'arasawa" ta fada tana kokarin raba shi ta wuce.

Cinkiko hannun ta yayi ya had'a ta da bangon wajan ya zuba mata golden eyes din sa yace, " I said what are u doing here? Don't make me stupid". Wani irin yarrrrr take ji a jikin ta saboda yadda ya rik'e hannun ta laushin hannun sa na ratsa ko ina na jikin ta hakan ya saukar mata da mutuwar jiki, cikin cool voice tace, "Na fada maka gaskiya nida k'awa ta ne."

Kallon ta Ammar yake cike da rashin yarda, bai sake cewa komai ba yaja hannun ta suka bar wajan basu tsaya a ko ina ba sai a bakin motar sa ya kalle ta yace, "Shiga". Kallon sa tayi itama tayi ta turo baki gaba  tace, " Ni ba yanzu zan tafi ba kaje kawai daman ai ba tare muka zo ba." Had'e rai yayi kamar bai taba dariya ba yace, "ke ina miki Wasa ne? Dallah malama shiga kona mare ki" yadda yayi maganar cikin kakkausar murya yasa ba shiri ta bude ta shiga tana kunkuni.

Cikin gidan ya koma babu jimawa sai gashi da Hamza sun fito tare ya shiga mota shima suka fara tafiya.

Tafiya suke babu Wanda yake magana sai sautin karatun alkur'ani da yake tashi da motar yana bi a hankali cike da kwarewa, kallon sa tayi tana mamakin haka ya iya karatu dama rana ta farko da taji ya dan burge ta dan tana son namiji mai ilimin addini, shi kuwa yana kallon ta gefen ido farin ciki na ratsa zuciyar.

Danger ce ta tsayar dasu can gefe Amatullah ta hango almajira tana bara hakan yasa Amatullah ta sauke glass da niyar bayar da sadaka, motar dake gefen side din Amatullah driver ya kalle ta yace, "Wow! Kai kaga wata kyakykyawar yarinya kamar ita tayi kanta" ziro hannu Amatullah tayi ta mik'awa almajira kud'in godiyar da take yasa tayi murmushi har hushiryar ta ta baiyyana, rikicewa mutumin ya sake yi tare da fadin, "Gaskiya yan mata kin had'u I love u".

A fusace Ammar ya daga glass din zuciyar sa na harbawa da sauri da sauri, cize baki yayi tare da runtse ido take idon sa ya fara juyawa zuwa red colour, matse yan yatsun sa yake kamar yadda ya saba suna bada sautin kassss kasss, kallon Amatullah tayi amma hankalin sa baya kanta, tsaki kawai yake ja yana kwafa.

Tafiya suka cigaba da yi har suka karasa gida, Amatullah ta bud'e suka fita ita da Hamza suka shiga gida, sai da ya tabbatar sun shiga sannan ya ja motar sa ya bar wajan.

___________

Gudu yake shekawa akan titi kamar Mara hankali, over taking kawai yake babu ji babu gani mutane sai nuna shi suke, gefe ya samu yy parking ya kifa Kansa akan sitiyarin motar yana sauke numfashi,  tabbas sai yau ya tabbatar yana k'aunar Amatullah bai taba sanin haka yake son ta ba sai yau, dago kansa yayi yana ajiyar zuciya yace, " Tabbas bazan tab'a bari Amatullah ta auri wani bani ba duk yadda zanyi sai na raba wannan auren koda ya kasance anyi shi, Amatullah tawa ce ni kadai ba ta sani ba babu Wanda ya isa ya mallake ta in ba ni ba" yana gama fadar haka ya bude robar ruwa yasha yaja motar sa ya bar wajan.

💐💐💐💐💐

Amatullah kuwa tana shiga gida sallar la'asar tayi ta dauki littafan ta ta nufi gidan sarki dake anan suke had'uwa gabadaya ayi karatu.




Yawan comments yawan typing.

MASOYA UKUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora