Page 31

91 4 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_



_{True love, intense jealousy & betrayal}_


By
Neat Lady




Dedicated to Ummu Nabil😍




Not edited





Page 31





........"Me aka zuba a abicin?" Ya fada yana kallan ta tana jikin sa, ganin haka yasa ya mike ya dauke ta cak ya kwantar da ita akan kujera ya kalli Nana yace, "Bani paracetamol da ruwa pls" ba musu ta juya ta dauko ta miko masa.

6allo maganin yayi ya kalli ta yace, "Mike kisha magani" tana dafe da kanta ta mike ya bata tasha ta kora da ruwa tayi ajiyar zuciya.

Umma dasu Rahma ne suka shigo falon suna kallan Amatullah dake kwance, kallan Umma Ammar yayi yace, "Umma me yake faruwa ne?".

"Bamu sani ba muma tazo ta same mu akan zamu ci abinci tace kar muci akwai magani a ciki."

Shiru sukayi kafin Amatullah ta mike zaune ta kalle su zatayi magana Ammar ya riga ta yace, "Ki bari ciwon kan naki yayi sauki sai kiyi mana bayani".

"Naji sauki, Umma Mama ta tura ni naje na dubo Humayrah bata da Lafiya naje zan shiga falon sai naji Aunty tana waya tana cewa......" Ta kwashe kaf labarin ta fada musu ta Dora da fadin, "Jin hakan sai hankali na ya tashi Umma sai nazo part din ki nace kada kuci sai nayo nan tunda daman akan Yaya Ammar din akayi maganin".


Ajiyar zuciya Umma tayi ta kasa cewa komai zuciyar ta na k'una, bata ce komai ba ta mike ta fice daga falon.

" Kin tabbatar abinda kika fada gaskiya ne?" Ammar ya fada yana kallan Amatullah.

Daga masa kai tayi tace, "Wallahi da gaske nake maka bazan yi muku karya akan abinda ba haka bane ba"ta fada idon ta na kawo ruwa.

"Oh why the cry now? Is okay".

Mikewa shima yayi suka fita shida su Ahmad aka bar Rahma da Nana a wajan, zama kusa da Amatullah Nana tayi tace, " Sannu" daga mata kai kawai tayi ba tare da tayi magana ba.

Basu wuce ko ina ba sai falon Abba dan baza su bar wannan maganar ba gwara ayiwa tufkar hanci, sai da suka kwankwasa yayi musu izinin shigowa sannan suka shiga, basu boye masa komai ba suka fada masa yayi shiru dan yasan halin matar sa tabbas zata aikata amma sai bai nuna musu ba yace, "Waye yazo muku da maganar?".

Ahmad yace, " Amatullah ce".

"Tana ina?".

" Tana part din Yaya Ammar. "

"Ku kira ta sannan a kira ita kaltume da Umman ku da kuma wacce ta kula da abincin yau, sannan kai Ahmad ka zagaya a tawo da Yaya."

Ba musu suka fita sukayi duk abinda akace musu kowa ya hallara kamar yadda aka bukata.

Gyaran murya mai martaba yayi ya kalli mai abincin yace, "Me uwar dakin ki ta baki yau ki zuba a abincin bangaren uwar gida?".

Jikin tane ya fara kyarma tana satar kallan  Aunty ita kuma tana galla mata harara, " Baza ki magana ba Kenan, Ammar kirawo min Galadima a waje a kaita prison " niyar mikewa Ammar yake cikin tsoro da hawaye tace, "Allah ya baka nasara Kayi hakuri ka gafarce ni ayi min afuwa".

Kallan Ammar yayi alamun kar yaje sannan yace, " To kiyi min bayani kamar yadda Na nema".

"Ina zaune jiya tazo ta same ni ta bani magani tace Kaine kace a zuba a abincin bangaren Umma snnan da bangaren yarima tace kace maganin tsari ne,wallahi ban san wani Abu bane a ciki dan Allah ranka ya dade Kayi min afuwa wallahi ban sani ba" ta fada tana kuka harda majina.

MASOYA UKUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora