Page 1

272 8 0
                                        

*MASOYA UKU*

Page 1

Not edited 🤙

............"Mama ni fa wallahi bazan iya zaman aure da Yaya Ammar ba, dan bana sonsa kuma bana jin zan so shi har abada" wata kyakykyawar matashiyar buduwa ta fad'a cikin tsiwa da rashin kunya.

"Wai ke Amatullah me yake damunki ne? Ana yi miki magana kina mayarwa dan baki da mutunci?. Ki nutsu ki dawo hankalinki ki tsaya mu yi magana cikin fahimta tun kafin Dadyn ki yazo, kin san dan ya zane ki ba wani abun bane a wajansa" matar wacce baza ta haure shekaru arba'in da biyar ba ta fad'a cikin fusata.

Zama Amatullah tayi tana kunbure-kunbure tana kunkuni. Wacce take amsa sunan Mama tace, "Amatullah haƙuri zaki yi ki amince da auren Prince kodan farin cikin mahaifinki, ni kaina ba son wannan auren nan nake ba har ga Allah, amma saboda halin mahaifinki yasa na amince dole. Kema ki nutsu ki san abinda ke miki ciwo, rashin amincewa da auren Ammar shine rashin kwanciyar hankalinki a cikin gidan nan, sanin kanki ne akan wannan auren mahaifinki zai iya tsine miki. A matsayina na mahaifiyarki ina so ki amince a auren nan kawai."

"Taɓɗi, yanzu akan wancan banzan sai Dady ya tsine min?...Shege sai girman kan tsiya kamar shine Yariman duniya gabaɗaya, wallahi na tsane shi kuma ni wallahi bazan aure shi ba" ta faɗa tana kau da kai gefe.

Cikin faɗa Mama tace, "Shikenan ki je ki yi duk abinda kiga dama, na cire hannuna daga kan ki tunda ke taurin kan tsiya gare ki, sai ki je Allah ya bada sa'a" tana gama faɗa mata haka ta miƙe fusace ta fita daga parlourn.

Taɓe baki Amatullah tayi ta ce, "Haka kawai a tauye min haƙƙi, ko bani da wanda nake so ai bazan auri wancan mutumin ba. balle ma ina da My Anwar. Haka kawai ina yarinta ayi min auren dole?." Haka ta dinga magana ita kaɗai har ta gaji ta miƙe ta haura sama.

Wani ƙatom bedroom ta nufa tana shiga ta faɗa kan gado tare da ɗauko iPhone 11 pro max ta danna tare da karawa a kunne, "Kina ina ne wai."
Daga can side "in akace, "Ina gida mana, da labari ne Besty?." Tsaki tayi ta ce, "Hmm, labari kai! Wai Dady ni yake so ya yiwa auren dole, kuma a rasa wanda za'a haɗa ni dashi sai wannan Yarima ɗin."

Cikin zumuɗi wacce ake wayar da ita tace, "Wanne Yarima kenan Amatullahi?."
"Mtsw! kef a banza ce wallahi, akwai wani Prince da ya wuce wannan mugun doctor ɗin na gidan Umma?."

Wani ihun murna tayi ta ce, "Wayyo Allah na! amma naji daɗin wannan labarin. Bestie zan zo na samu Dady da kaina nima ina goyan baya wallahi." Cike da mamaki tace, "Lallai Rahma, na yarda kin daina sona tunda har kike so ayi min auren dole da wannan mutumin."

"Sorry Dear ba haka bane wallahi, kawai dai abin ya sani farin ciki ne sosai. Kinga maganar nan baza ta yu a waya ba, bara na kammala abinda nake yi yanzu ki ganni".

Yatsine fuska tayi ta ce, "A'a bara nazo da kaina, babu abinda nake yi a nan kuma daman Mama ta bani saƙo na kawowa Umma." Bata tsaya jin abinda zata ce ba ta kashe wayar tare da miƙewa ta saka mayafi ta yafa ta sakko daga saman.

Da yake basu da nisa da gidan Sarki tana fito baya kawai ta zagaya tayi sai gata a ƙofar gidan. Babu wanda yayi mata magana dan ansan wace ita, sai zubewa da ake ana kwasar gaisuwa ita kuma tana amsawa cikin fara'a.

Da sallama ta shiga parlourn dake ɓangaren Umma, babu kowa a parlourn sai hadimai da suke ta aikinsu, gaishe ta suka yi ta amsa sannan ta wuce ciki, kamar yadda tayi tunanin tana zaune tana karatun alkur'ani mai girma.

Kusa da ƙafarta ta zauna tana wasa da adon lace ɗin dake jikin zanin Umma, sai da ta kai aya sannan ta rufe alkur'anin tayi murmushi tare da kallon ta tace, "Amatullahi na barka da zuwa".
Cike da shagwaɓa tace, "Umma barka da yamma" cikin fara'a tace, "barkan ki, kin wuni lafiya?".
" Lafiya lau Ummana, ina Bestie take?."

MASOYA UKUStories to obsess over. Discover now