*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_By
Neat LadyDedicated to Ummu nabil😍
Not edited🤒
Page 35
........Babu Wanda yayi magana cikin su har suka karasa gidan, tun daga gate din gidan zaka tabbatar da gidan ba karamin haduwa yayi ba yana tsayawa a bakin gate din ya danna horn a guje mai gadin ya leko ya ganshi ya hangame masa gate din shi kuma ya danna kan motar sa cikin gidan.
Yar rumfar da aka tanada sabida ajjiya motoci ya karasa ya ajjiye sannan ya bude kofar ya fito, ganin ya fita ya saka Nana ma ta fito Amatullah kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka take bude motar a hankali ta ziro kafufun ta da suka sha zanen Jan hennah ta fito daga motar.
Sai ka haura steps guda hudu sannan zai sada ka da kofar farko, mukulli ya saka ya bude suka shiga ciki yana gaba Nana na bayan sa sai Amatullah a karshe kanta na kasa.
Katon falo ne sosai Wanda yaji saitin kujeru guda biyu ga tafkekiyar TV kirar GL a ajjiye akan wani tv stand mai bala'in kyau, tsakiyar falon kuma sallahaya carpet ne kato mai kyau ruwan madara a shinfide a a kan sa kuma katon center table ne Wanda aka yi masa ado da flower mai kyau.
Gefe guda kuma ga dining table mai guda shida a ajjiye kusa da shi ga fridge da show glass Wanda aka cika ta da plates da cups da spoons, zama Ammar yayi a kujera suma suka zauna.
Gyaran murya Ammar yayi kafin yace, "Alhamdullah godiya ta tabbata ga Allah subahanahu wata'ala da ya bamu ikon shigowa cikin gidan nan lafiya, ina fatan yadda muka shigo lafiya Allah ya bamu ikon zama a cikin sa lafiya amin."
"Duk wani Abu da ya faru da bawa mai kyau ko Mara kyau daga Allah ne shine yake jarabbatar bayin sa da mafisu kala-kala in kuma kana daure ka cize sai ka tsallake, Nana kece babba a gidan nan ko ina nan ko bana nan Amatullah tayi wani Abu ba dai-dai ba ki tsawatar mata ba sai an jira ni ba sannan kuma kada matsalar ta zo daga wajan ki kiyi kokarin ganin kin jan girman ki Dan Allah, and u Amatullah kar naji wani Abu ta bangaren ki kema ki girmama Nana itace sama
dake a gidan nan ko ba haka ma ta Fiki shekaru so ki girmama na gaba dake,""Nana kada kiji nace kece babba ya saka kuma ki nuna wani halin daman, bana san tashin hankali Dan Allah dukkan Ku mata nane kuma daya kuke a waje na so pls kar ku caza min kai kuma kuma Ku caza naku kuyi kokarin ganin komai ya tafi dai-dai, ta side dina kuma insha Allah zan kamanta adalci a tsakanin Ku sannan in daya a cikin Ku taga nayi wani Abu ba dai-dai ba ta sanar dani kar ta boye min tazo kana kallo na da abin kuma tana jin babu dadi,Dan Allah Ku kiyaye."
Daga kai Nana tayi tace, "Insha Allah zaka same mu masu maka biyayya".
"Good, Nana muje na raka ki naki part din lokacin sallah yana gabatowa" ya fada yana mikewa tsaye mikewa itama tayi suka bi ta wajan dining table din suka bude wata kofa sai ga kofofi guda uku daga can bangaren kuma ga steps din da zai kaita upstairs nan, kofar karshen wacce take gefen haggu ta bude sai ga wani dogon waje Dan karamin kana karya corner ga katon falo nan mai dauke da komai da komai kamar waccan falon, dai bedroom guda uku daya da bandaki a ciki biyun kuma bandaki yana tsakiya,sai kitchen.
A kan kujerar ta zauna shima ya zauna yace, "Ga naki side din so pls Nana Dan Allah kar naji kar na gani kar ki sake maimaita min irin kalaman ki na jiya".
Daga masa kai kawai tayi Dan babu zarafin magana sabida yadda take jin kirjin ta na up and down, mikewa tsaye yayi yace, " zan dawo anjima ki kula da kanji" ya fada yana sakar mata murmushi yana fita daga side din.

YOU ARE READING
MASOYA UKU
Romanceta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.