*MASOYA UKU*
_(The three lovers)__(True love, intense jealousy and betrayal)_
Not edited
11
Amaryar Amatullah na gano zaune kusa da Rahma da Humayra ko wacce taji kunshi da kitso, Shigowa Aunty Hafsa tayi tace, "Amatullah ga me make up din tazo fa kamata yyi kuzo a fara lokacin kamun nan Yana matsowa."
Mikewa Amatullah tayi jikin ta a sanyeye dan tunda Anwar ya Kira ta ya kashe Mata jiki gabadaya bikin ya fice Mata a rai, tsara Mata kwaliyya akayi irin ta kamu, tabarakallah shine abinda kowa yake fada in ya Dora idon sa akan Amatullah, kowa ya Gama shiryawa aka tafi wajan kamu.
Waje ya tsaru an cika ana jiran isowar amarya Amatullah dake zaune a mota mamaki ne fal ranta wai itace yau ake bikin ta kuma wai da Yaya Ammar ba Anwar ba, take ran ta ya baci ta hade rai zuciyar ta na rawa, mc ce ta fara sanar da isowar amarya hakan yasa kowa ya maida hankalin sa kansa kofar shigowa.
Tun tana cikin mota ake zuba mata hotuna har ta fito, Rahma ce a gaban amarya aka saka wakar godly suka shiga suna takawa, tunda ta shiga wajan kowa hankalin sa ya dawo kanta masu cewa masha Allah nayi, masu cewa wannan ba bahaushiya bace na fada kowa yana fadar albarkacin bakin sa akan halittar Amatullah.
A can kuwa Khalid sai lallaba Ammar yake akan ya tashi ya shirya suje wajan kamun nan Amma Sai wani basarwa yake dakyar suka shawo kansa ya shirya, Yana fitowa suka zuba masa Ido sbida yadda Kofi din shaddar ta amshi jikin sa, Yasir yace, "Masha Allah gaskiya kayi Kyau ana ganin ka anga ango" murmushi yayi suka fita suka hau mota suka nufi wajan event din.
An gayyaci masu hotuna da videos kala-kala tun daga Kan gidan tv gidan redio babu Wanda Basu hallarci wannan taron biki ba, masu jaridu suna aikin su suma duk inda ka zaga zancen bikin Ammar da Amatullah ake yi wasu wuce labarawa bane wasu suce turawa, dakee Ammar ba boyyeyen mutum bane a duniya sabida asibitin sa yana daya daga cikin manyan private hospitals na garin, hakan yasa gari ya sake dauka manya masu kudi da yayan su kaita dodo wajan hallartar bikin
Shiga Ammar wajan ya hargitsa wajan kowa da abinda zaice wannan yace tafi shi Kyau wannan yace ya fita kyau dan mace ce ita, haka akayi shagali aka watse amarya da ango suka fito suka shiga mota.
Babu Wanda yayi wa wani magana kowa da sakar da yakeyi a zuciyar sa, har suka isa gida babu Wanda yace k'ala, sai da ta bude kofa zata fita taji yace, "sai da safe". Bata amsa ba tayi gaba abin ta Dan haushin sa take ji.
Tana shiga ta tarar da Yan Mata ana ta hira shige su tayi tayi daki tana shiga ta fincike dankwalin ta fada bandaki, babu jimawa sosai ya fito daure da towel a jikin ta zauna a bakin gado sai tsaki take yi, Rahma ce ta shigo ta zauna kusa da ita tace, "Kaga amaryar Yaya Ammar wallahi ba karamin dacewa kuka yi ba kowa sai fada yake."
Tsaki ta sakeyi ta mike ta karasa bakin wadrop ta bude ta saka Kaya da hijjab ta tayar da ikama, Bayan ta idar ta zauna kawai tana tunanin yadda auren Nan zai kasance Bayan ita ba Ammar take so ba Anwar take so, Rahma ce ta zauna kusa da ita a kan sallayar tace, "Amatullah Wai har yanzu baki cire tunanin Anwar din nan a ranki ba? Kar ki manta fa an kusa daura Miki aure Wai yaushe soyayya ta rife Miki Ido haka?".
Ajiyar zuciya tayi kawai ta mike ta kwanta a kan gado ta rife Ido badan tana jin baccin ba.
Washe gari haka suka Sha shagalin cocktail party dake iya kawayen tane babu maza hkan yasa Ammar ma baije ba, Sai dare suka tashi hankalin amarya Amatullah gabadaya hankalin ta baya wajan tunda suka yi waya da Anwar shikenan lissafi ya kwance Mata.
Washe gari ya Kama ranar Asabar duk inda ka zaga a gidan sarki baka Jin komai sai karar busar aljaita ko wanne bangare ana ta hada hada wannan yayi Nan wancan yayi can, mahaifyar ango tana hakimce fuska cike da farin ciki da walwala ana zuwa ana Kai gaisuwa.

VOCÊ ESTÁ LENDO
MASOYA UKU
Romanceta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.