*MASOYA UKU*
_(The three lovers)__(True love, intense jealousy & betrayal.)_
Ina ganin comments dinku sosai da addu'o'in Ku gare ni ina jin dadi sosai nagode muku sosai sosai.
Page 6
Not edited🤙🏻
........... Biki na dad'a matsowa ta ko Ina shirye-shirye ake bana wasa ba, b'angaren ango ma shirin biki yake cikin kwanciyar hankali cikin farin ciki da annushuwa, ita kuwa amarya mantawa take ma za'a yi wani bikin ta sabida yadda ta maida hankalin ta wajan Anwar baki daya Koda yaushe suna mak'ale a waya hakan ya sa zuciyar ta ta sake karyewa ko tayi niyar mantawa dashi sai ta kasa sabida wata sabuwar kulawa da yake Bata Mai cike da so da kauna.
Shi kuwa Anwar Yana yin haka ne dan ya kawar da hankalin ta daga son auren gabadaya hakan yasa yake dad'a cusa mata k'aunar sa a zuciyar ta Yana Kuma zuga ta akan ko anyi auren kar ta sake su rabu yayi mata alk'warin zai aure ta in ta kashe auren ta fito.
Shi kuwa Ammar a kullum son Amatullah sake shigar sa yake bashi da wani sukuni a tare dashi indai Bai ganta ba, Yana zaune a garding shida Yasir suna tattauna maganar biki Amma gabadaya hankalin sa baya wajan Yasir yana can tunanin Amatullah da yau kwana biyu kenan bai saka ta a Ido ba.
Yasir ya lura gabadaya hankalin sa baya tare dashi hakan yasa ya dafa shi yace, "Wai Ammar tunanin me kake yi ne haka?." Juyowa yayi ya kalle shi ya koma ya kwanta a jikin kujera ya fara wasa da yan yatsun sa kamar yadda yadda saba yace, "Ni bana tunanin komai,cigaba Ina jinka."
"Ta yaya zaka ce min ba tunani kake ba bayan gabadaya hankalin ka baya tare dani, Ammar ka sassautawa kanka wannan zazzafar soyayyar fa Dan nasan bazai wuce tunanin Amatullah kake ba ba ace Kar ka sota ba Amma ka dinga sassautawa sbd gudun matsala ga Kuma ciwon da kk fama dashi".
Lumshe Ido yayi ya Bude a hankali yace, "Yau kwana biyu ban sata a Ido na ba dole na shiga damuwa ai, wallahi zuciya ta har zafi take Dan Allah taimaka ka Kira min ita in ba haka ba bazan tab'a fuskantar abinda kake fada ba."
Cike da tausayawa Yasir ya dauko waya a aljihun sa ya Kira number Amatullah, tana zaune suna charting da Anwar kiran Yayan nata ya shigo wayar ta, dauka tayi tare da yin sallama.
Yasir yace, "Sister kina Ina ne?". Daga can bangaren ta amsa da "Ina gida yanzu dai na dawo daga makaranta." "okay ko Zaki kawo min aron power bank din ki waya na charji yayi low gashi ban tawo da nawa ba."
"Shi kenan kana Ina na kawo maka?". "Ina baban gida,side din Ammar kiyi sauri" Yana Gama fadar hakan ya kashe wayar bai jira yaji ne zata ce ba.
B'ata Rai tayi cike da Jin haushin Ammar tace, "Aikin banza duk yadda naso da gujewa wannan mutumin yau Sai na ganshi Allah yasa dai baya nan na huta da ganin mummunar fuskar sa" ta fada tana daukar power bank din ta fito daga d'aki.
Tafiya take a hankali kamar wacce take tsoron taka kasa har ta isa cikin gidan Sarki, Bata wuce ko Ina ba sai part din Ammar tun daga nesa ya hango ta ya zuba mata Ido kamar yaga sabuwar halitta zuciyar sa na harbawa da sauri kamar zata faso kirjin sa hannu yasa ya dafe gefen zuciyar sa Yana ajiyar zuciya tare da lumshe ido.
Ita kuwa kanta a sunkuye ta k'araso wajan tana zuwa ta kalle shi ta gefen Ido ya wani basar kamar bashi ba, a dakile tace, "Ina wunin ku". Bata jira ya amsa ba kawai tace, "Yaya Gashi " ta fad'a tana Mika masa power bank din.
Karb'a yayi tare da yin murmushi yace, "Yauwa kanwata sannu da kokari" murmushi tayi kawai bata ce komai ba.
Mikewa Yasir yayi yace, "Jira ni bara na fito" ya fad'a Yana shiga cikin part din Ammar ya barsu su biyu a wajan.

STAI LEGGENDO
MASOYA UKU
Storie d'amoreta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.