Page 14

80 6 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lovers)_


_(True love, intense jealousy & Betrayal)_



By
Neat Lady


Not edited🤒


_Wannan page din gabadaya sadaukarwa ne ga Ummu nabil dina.🥰_

Page 14


.....Jin an rike ta ya sake firgita ta tana zare ido, cikin muryar marasa lafiya yace, "Tsoron me kike ji?" Jin maganar sa ya saka ta sauke ajiyar zuciya.

Sakin hannun ta yayi ya koma inda ya tashi ya zauna yana dafe kansa lokaci daya komai yake dawo masa kwakwalwa.

Ganin hakan ya saka jikin ta yayi sanyi ta taka a hankali kanta a kasa taje gab tashi ta rage tsaho tace, "Sannu Yaya Ammar ya jikin?" Banza yayi mata dan bala'in haushin ta yake ji kamar ya tsako ta haka yake ji a lokacin.

Ganin hakan ya saka jikin ta ya sake yin sanyi ta zube a k'asa tana zubar da hawaye tace, "Nagode da taimakon ka gare ni, Allah ya rufa maka asiri kamar yadda ka rufa min nawa hak'ik'a in badan kai ba da yanzu ban san a wanne hali nake ba a wajan iyaye na nagode sosai."

Banza ya sake yi mata dan har yanzu bai wuce ba, ace matar sa guda ta gudu tabi wani kuma ya same ta a jikin ta ina k'imar aure take a nan.

Ganin hakan ya sa jikin Amatullah yayi sanyi ta mike a hankali tana niyar tafiya taji yace, "bani wayar ki" ya fad'a yana miko mata hannu har lokacin idon sa a kulle yake.

Gaban tane ya fadi tsoro ya kamata gashi bata da ikon hanashi a wannan lokacin, tana tsaye inda take ita bata kai masa wayar ba kuma ita bata bar d'akin ba, bud'e ido yayi ya kalle ta akayi sa'a itama shi take kallo suka had'a ido cikin sauri ta sunkuyar da kai hannun ta na rawa.

"Bakiji me nace miki bane?" A razane ta d'ago kai tana takawa a hankali ta mik'a masa wayar, karb'a yayi ya ajjiye kusa dashi ya sake lumshe ido, juyawa tayi Kamar wacce Kwai ya fashewa a ciki ta bud'e d'akin ta fita.

Jin fitar ta ya saka yayi ajiyar zuciya yana jin kamar ya yaje ya dawo da ita ta tsaya yana kallan ta ko ya samu saukin yadda zuciyar sa ke harbawa, bud'e kofar da akayi ya saka ya d'ago kai da sauri duk a tunanin sa itace ta dawo amma sai yaga Khalid da Yasir yaja tsaki yana kau da kai.

Zama sukayi Khalid ya kalle shi yace,"Sannu Ammar ya jikin naka?" Daga masa kai kawai yayi alamun da sauki, ganin alamun ya samu sauki ya saka Khalid yace, "Wai meye ya bata maka rai haka?" Dogon numfashi yaja ba tare da yace komai ba, Khalid ya kalli Yasir yayi masa alamun kawai su kyale shi bazai fad'a ba, Khalid ya sake cewa, "Any way tunda baza ka fad'a ba shikenan, naga Amarya ta fita yanzu ina fatan dai ka fada mata abinda yake ranka?".

Lumshe ido yayi ya bude ya kalli Khalid kawai still baiyi magana ba, yasir ya zauna kusa dashi yace, " Ammar yanzu fa ba da bane yanzu ka riga ka aure ta matar kace babu wani sauran baza ka fada ba sabida kar raini ya shiga tsakani babu wannan yanzu, gaskiya zamu fada maka mu baza muga abinda zai cutar dakai muyi shiru ba tsakani da Allah indai kace a haka zakuyi rayuwar aure kai kana Santa kana ganin bata kai ka fada mata ba ita kuma tana ganin ba ka ce kana Santa ba koda tana sanka itama baza ta fada ba kaga kenan babu wata rayuwa me dadi da zata gudana a tsakanin ku, in Baka nuna mata kauna ba ta yaya zaka kawar mata da tunanin samarin ta a rai? Mace tana da rauni sosai kuma tana san wanda ya damu da ita mace nasan a kula da ita a nuna mata ita mace ce amma kai kana ganin tayi kankanta da ka bayyana mata abinda yake ranka, kamar Amatullah baza ta rasa saurayi ba ko nace samari ma in Baka nuna mata so na baza ta manta soyayyar da samarin ta suka nuna mata bafa abin zai dinga yi mata yawo tana tunanin da wane ne da yanzu yana nuna min so da kulawa."

MASOYA UKUHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin