Page 9

88 6 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lovers)_

_(True love, intense Jealously & betrayal.)_

Page 9


Not edited🤙🏻

............Shigowar Aunty Hafsa ya saka Amatullah ta mik'e ta fada jikin ta ta fashe da kuka, Aunty Hafsat ta dago ta daga Cikin ta tace, "what is wrong with u sis? Meye kike kuka?".

Kin daina kukan tayi Aunty Hafsa ta shafa Bayan ta tace,"Oh relax sis, dan zakayi aure shine Zaki dinga kuka haka? Kinga malama ki kwantar da hankalin ki a dadin ki ma kina kusa da gida Ni da nake nesa nace me?"

Janye jikin ta tayi ta koma bakin gado ta zauna Tana shawarar ta yarda zata sanar da Aunty Hafsa wanann magana, Aunty Hafsa ta zauna kusa da ita tace, " wouldn't glad to see me ko? Shikenan let me go back where i came from" ta fada tana mik'ewa.

Da sauri ta rik'o hannun ta tace, "I'm sorry my sis ba haka bane ba nayi murnar ganin ki Mana kawai bana dan Jin Dadi ne."

"To naji, yanzu meye shirye-shiryen bikin naki? Kinga yanzu saura baifi 3wks ba ya kamata ace kin shirya komai yanzu."

"Hmmmm My sis kenan, Nidai Ina Muniba da Munira suke?". Aunty Hafsa tace, "Suna wajan Mama kin San dake yayi tafiya har Bayan bikin ki ma Ina nan Dan kusan wata daya zaiyi".

Mik'ewa tayi cikin farin ciki tace, "Wow gaskiya nayi farin ciki, I will see my children for a long time" ta fada tana ficewa daga dakin a guje, Aunty Tayi murmushi tace "Amatullah tana Nan da halin ta".

Lokaci na dad'a tawowa ana ta shirye shiryen biki, Ammar kuwa tun lokacin da wannan maganar ta shiga tsakanin su da Amatullah Basu sake had'uwa ba ko a hanya, ta b'angaren ta kuwa hakan yayi Mata dan Bata da lokacin sa love kawai suke sha ita da Anwar, Aunty Hafsa ta zage sosai Tana gyara kanwar ta da kayan gyaran jiki kala-kala abin ka da farar fata Nan da Nan fitar ta ta sake haske har yellow take shi sabida yadda Tasha gyara.

Rahma ma ba'a barta a baya ba da ita ake ta shirin biki Amma Amatullah ko a jikin ta kawai tana daurewa ana Shirin da ita sbd ita kadai tasan abinda ta shirya.

Ammar kuwa Khadil da Yasir ne kawai suke Shirin su dan shi yanzu bikin ya fice masa a Kai tunda ta furta ga Wanda take so, kamar kullum suna zaune a parlourn dake side din Ammar Khalid ya Kalli Ammar da yake ta Danna waya tace, "Wai Ammar baka ji Ina maka magana ne?".

Dago Kai yayi tare da yatsine fuska yace, "kaga ni fa babu wani events da za'ayi a daura aure ayi walima is ok".

Khalid yace, "Bafa ka Isa ba Sai an hada Koda Dinner ne kai ko baayi dinner ba ai akwai kamun amarya Kuma zaka je, so ka daina zancen babu wani events da zaka yi."

Ammar ya d'ago Ido ya zubawa Khalid su yace, "Ni babu wani events da zanyi na fada maka". Yasir da yake Jin su yace, "Wai Ammar kamar ba auren so zaka yi ba? Haba ka daina irin wnn ka saki jiki mu Sha shagali Mana,Wai tsaya ma kaje ka samu Amatullah kunyi magana ko tana da wani abun da take so.?"

Ammar yace, "Ni zanje ma na same ta? Kaima kasan is not possible naje wajan ta sai dai ka Kira a waya muji yanzu."

Kafin Yasir yace wani Abu Rahma da Humayra suka yi sallama suka shigo parlourn, gaida kowa suka yi cikin dar_dar Rahma tace, "Yaya Ammar wajan ka muka zo".

Ya d'ago ya daga Mata gira alamun Ina Jin ki, Humayra ta kalla sannan tace, "Daman munzo ne akan kudin da zaka bamu zamu had'a cocktail party." Dago Kai yayi da kalle ta hakan ya saka hantar cikin ta ta kada ta sake sunkuyar da Kai.

Dauke kansa yayi daga kansu yace, "cocktail party na mefa? Birthday zakuyi ko bikin ku za'ayi ne zaku had'a cocktail?".

Kallan Rahma Humayra tayi suka rasa abin cewa suka yi shiru, maganar sa suka ji yace, "ku fice ku bani waje in baku da abin cewa."

MASOYA UKUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora