Page 20

82 4 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_


_(True love, intense jealousy & betrayal)_



By
Neat Lady




Not edited🤒



Dedicated to Ummu nabil😍



Page 20


........tunda ya shiga jirgi yake jin bugun zuciyar sa karuwa da ya tabbatar dai yayi nisa da Amatullah wata kila har abada, sanda jirgi ya daga sai da hawaye masu zafi suka sakko daga idon sa ya lumshe ido ya jinginar da Kansa a jikin kujera.


Lokacin da jirgi ya dira a kasar Germany ciwon Ammar ya tashi numfashi ma dakyar yake yi, numfashi yake dakyar ganin haka ya saka aka dauke shi aka nufi asibitin dake airport din.

Taimakon gaggawa suka shiga bashi ana kokarin ganin numfashin sa ya daidaita,an sha wahala sosai kafin numfashin ya dawo dai-dai bacci ya dauke shi.

Sai bayan two hours sannan Ammar ya farfado, a motar asibitin aka kaishi har hotel din da yayi booking suka bashi magunguna sannan suka koma.

Ammar dake zaune yayi shiru ya rasa me yake masa dadi cikin sane ya kulle yasan yunwa yake ji dan ya manta rabon sa da abinci, oder din coffee da biskit kawai yayi a waya, bb jimawa akayi knocking ya bude ka karba ya maida kofa ya rife.


Bude kofin yayi ya kai coffee din bakin sa kamar madaci haka yake jin sa amma  haka ya rintse ido ya haddiye yana yatsine fuska.

_Anwar nake so shine zabin rai_ maganar da ta dawo kwakwalwar sa kenan bai san lokacin da ya saki kofin dake hannun sa ba yana rike kai sabida yadda yake sarawa.

"Why Amatullah? Why? Me nayi miki haka? Wacce irin tsana kika yi min haka? A washe garin Daren mu na farko kika ce na sake ki, meyasa?" Shi kadai yake magana yana dafe kirji.

"Insha Allah zan yi kokarin ganin na manta dake duk da nasan bazai yu ba hakan amma zanyi kokarin na rage wani abun" da haka ya mike dakyar ya shiga daki dan shi Kansa bai san me ya kawo shi garin ba.

Zuwan Amatullah Zaria bai saka ta manta da komai ba sai kara mata yawo da abin yake a kai kullum da Ammar take kwana take tashi ta kuma rasa dalilin hakan.


Haka rayuwa take tafiya ta bangaren Ammar da zama kawai ya shiga makaranta ya kara course akan aikin sa, Amatullah kuwa ta kasa mantawa da komai duk da Anwar yana debe mata kewa da kuma fada mata yarda rayuwar auren su zata kasance, kamar koda yaushe tana kwance a daki tana waya da Anwar tace, "sabida bana so su Mama su gani babu idda a kaina shiyasa na bar garin ka saura kwana nawa na gama iddar ka kara hakuri komai ya kusa zuwa karshe."

Daga can bangaren Anwar yace, "To shikenan matata Allah ya  kaimu lokacin amma Gaskiya na k'agu sosai."

"Kar ka damu lokaci ya kusa zuwa" ta fada gaban ta na faduwa tana fargabar ranar da Anwar zai san ba budurwa bace ba.

Haka suka cigaba da hirar su cikin soyayya, sai da yaran Aunty Hafsa suka dawo ta kashe wayar suna hira da ita.

********

"Sannun ka da hutawa" wata doguwar mace black beauty ta fada tana zama kusa da Ammar.

Daga kai yayi ya kalle ta yace, "yawwa sannu" ya fada yana maida Kansa ga danna wayar da yake yi.

"Da alama dai yau lectures din kaima ya baka wahala" ta fada da murmushi tana kallan Ammar.

Dan murmushi kawai yayi baice komai ba dan ya lura yarinyar akwai naci.

MASOYA UKUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora