page 30

90 3 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_


_(True love, intense jealousy & betrayal)_


By
Neat Lady



Dedicated to Ummu Nabil😍



_ina miko sakon gdy ta a gare ku masoya na Allah ya bar kauna._🥰



Not edited🤒


Page 30




........ "Tun dazu nake kwala muku kira kun kule daki, yan school din ku ne suka zo sai ku fito" tana gama fada musu haka ta juya ta fita tare da Jan kofar.


Ajiyar zuciya sukayi a tare Rahma tace, "Nagode Allah na dauka ta ji mu fa."

"Nima haka wallahi, Bestie maganar nan iya ni da ke ne pls".

" karki damu saka kayan ki fito bara naje wajan su" ta fada tana mikewa ta fita itama ta dauko kaya tana niyar sakawa.

Nana kuwa tana komawa gida ta Tarar dashi da yana zaune inda ta barshi yana jin shigowar ta ya dago ya sakar mata murmushi tare da miko mata hannu, mika masa itama tayi ya jata zuwa cinyar sa ya zagayo da hannun sa rike kugun ta yace, "sannu da dawowa".

"Yauwa, ai Alhamdulillah tama ji sauki sosai".

Bai bata amsa ba sai laluben bakin ta da yake yi Dan baya san yawan yi mata maganar Amatullah tana shirin yin magana ya fara mata hot romantic kiss dole yasa tayi shiru ta fara mayar masa da martani.

Amatullah kuwa sun jima sosai suna hira da yan ajin su kafin suyi mata sallama su tafi, bayan fitar su tayi ajiyar zuciya ta kalli Rahma ba tare da tace komai ba.

Rahma tace, "Akwai magana a bakin ki."

"Eh ina so naje wajan Yaya Ammar ina so naji yace ya yafe min da bakin sa."

"To tashi muje mana in zaki iya."

"A'a mu bari zuwa gobe naje yanzu bana iya tafiya sosai ciki na daurewa yake yi."


Haka rayuwar Amatullah ta cigaba da tafiya a gidan su had tsahon sati guda, taji sauki sosai yanzu ko rikewar cikin babu ta dan fara mayar da jikin ta farin ta yana dawowa sai dai har lokacin bata fita ba kuma bata sake ganin Ammar sai dai Nana, ta idar da sallar la'asar tana sanye da hijjab pink colour har kasa ko takalmin ta ba'a gani ta fto daga daki Mama Na zaune akan kujera ta zauna kusa da ita tace, "Mama yau zan shiga wajan su Rahma na gaji da zaman".

" To Amatullah sai kin dawo ki gaishe su" mikewa tayi ta fita ta amsa da to.

Da kallo Mama ta bita tana jin tausayin ta har ranta yarinyar karama kamar Amatullah ace tayi aure har biyu kuma ta fito, ajiyar zuciya tayi har Dady ya zauna kusa da ita bata sani ba sai da yace,

"Tunanin me kike yi?".

Juyowa tayi ta kalle shi kafin tace, " Amatullah yarinyar tana bani tausayi sosai kalle ta fa har yanzu bata cika shekara ashirin ba amma auren ta har biyu yanzu kuma tunanin na uku za'a yi, abin nan yana mutukar damuna wallahi kawai daurewa nake yi."

"Nima yana damuna ba kadan ba babu yadda zamu iya da kaddara dole mu karbe ta hannu biyu, addu'a zamu dinga yi mata Allah ya kawo mata na gari Wanda in tayi sai mutuwa kuma."

"Amin ya Allah, yanzu ka dawo".

"Eh na shigo lokacin kina tunani" ya fada yana mikewa tare da Shiga daki.

Amatullah koda ta shiga gidan bata wuce ko ina ba sai wajan Umma, dake la'asar ce tana zaune ta shiga da sallama.

Da fara'a Umma ta amsa tana fadin,"A'a Amatullah yau kice da kanki?".

MASOYA UKUWhere stories live. Discover now