page 28

68 3 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lover's)_

_(True love,intense jealousy & betrayal)_



By
Neat Lady



Not edited🤒



Dedicated to Ummu Nabil😍


Special gift to my friend Zainab🥰💃🏻




28




......... Suna waje zazzaune kowa yayi gujum-gujum ana kallan dakin da aka shiga da Amatullah, mikewa Dady yayi yace, "Anyi kiran sallah bara muje masallaci" ya fada yana tafiya Ahmad ya rufa masa baya.

Mikewa suma sukayi a wajan sukayi sallah bayan sun idar suka zauna kowa yana nasa tunanin har su Dady suka dawo, kamar an cillo shi haka suka ga Ammar ya shigo wajan da mamaki suke binsa da kallo ya kalli Dady yace, "Dady me yake damun ta?".

"Bamu sani ba Ammar jiran fitowar su mukeyi".

Nufar dakin yayi sai kuma likitan ya fito kowa ya mike ana jiran me zaice, kallan su  yayi sosai kafin ya gyara tsayuwar sa yace, "jinin ta ya hau da zancen da nake muku a lokacin da aka kawo ta jinin ta ya kai 190 sannan ga ulser da tayi mata mugun kamu, yanayin fitar numfashin ta ma ya canja amma Alhamdulillah yanzu mun shawo kan matsalar komai yayi dai-dai ta samu bacci ."


Yaya ta kalle shi tace, "Zamu iya shiga mu ganta kenan?."

"Eh zaku iya sai dai kawai kar ayi hayaniya sabida kar a tashe ta."

Shiga sukayi gabadayan su banda Ammar da ya koma ya zauna duk mararin ganin ta da yake yi lokaci daya kuma yaji babu shi hankalin da tunanin sa sun koma tunanin duka meya saka ta a wannan halin, kukan Yaya da ya jiyo ya saka shi mikewa da sauri ya shiga bai kai hankalin sa ga kan gadon ba sai Yaya da yake kalla.

"Duba Ammaru kalli yadda Amatullahi ta koma lokaci daya kamar ba ita ba ko ina na jikin ta ciwo ne, wanne mugun abun ta hadu dashi?" Yaya ta fada tana kuka tana kuma nuna masa Amatullah dake kwance.


Idon sa ya kai ga kan gadon ya zuba mata ido yana so ya tantance itace ko kuma na ita bace ba, matsawa yayi sosai yana kare mata kallo shi Kansa sai da ya tsorota da yadda ta koma yayi shiru kawai yana tunani.

"To ina mijin nata ne wai?" Maganar Ahmad ta katse masa tunani.

Juyowa yayi a hankali yana bin Ahmad da kallo sai a lokacin Aunty Hafsa take kuma tace, "Ita kadai fa ta shigo banga kowa ba kuma yadda ka ganta a haka tazo babu takalmi, babu mayafi, babu dankwali kalli kayan jikin tama duk sun fita daga hankalin su, anya ba daga wajan kidnappers ta gudo ba?."


Dady yace, "Duk ku kyale wannan maganar a bari taji sauki zatayi mana bayanin komai."

Haka kuwa akayi suka zauna banda Ammar dake tsaye har lokacin yana nazari akan maganganun su, Yaya ce ta kalle shi tace, "Ammar ka koma gida fa ka baro Yar mutane ita kadai ba'a haka."

Dago kai yayi ya kalli Yaya ya lumshe ido bai kuma motsa ba, "Ka tafi akace dare yayi, kuma kuzo mu koma a bar Hafsa a nan ta kwana da ita" ya fada yana kallan Mama da Yaya.


Komawa Yaya tayi ta zauna tace, "Ai sai dai ku tafi ni kam babu Inda zani."

Kallan Hafsa Ammar yayi yace, "Duk abinda ya faru ko yaushe ni ki kira ni".

" Baza'a kira ka ba kana da Amarya ka dinga fitowa" Yaya ta fada shi kuwa har ya fice daga dakin ma.

Har Ammar ya karasa gida jikin sa a sanyaye yake ganin halin da Amatullah take ciki duk ya dame shi, yana hawa sama ya ga Nana zaune tana kallo da alama dai jiran sa take yi.

MASOYA UKUNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ