*MASOYA UKU*
_(The three lover's)__(True love, intense jealousy & betrayal)_
By
Neat LadyNot edited🤒
*Dedicated to my lovely friend Ummu nabil🥰 i dedicated all dis book to u💃🏻*
_Har na rasa bakin da zance muku komai💃🏻💃🏻💃🏻 tabbas jiya naga masoya Wanda banyi tunanin ina dasu ba🥰🥰🥰 nagode sosai da addu'o'in ku da kuma shawarwarin ku Allah ya bar zumunci.🥰_
Page 19
.........Cak Yasir ya tsaya jikin sa yayi bala'in sanyi sabida jin abinda Ammar yace, dakyar ya karaso kusa dashi ya dafa kafadar sa yace, "Ammar wai kana nufin maganar da ka fada min Gaskiya ko kuwa dai wasa kake?".
Juyowa yayi idon sa ya kada yy ja yace, " Ba wasa nake maka ba da gaske nake Yasir sai da na tabbatar sannan nake fada maka kuma bbu tabbacin samun Lafiya ta sai nan da shekara daya zuwa biyu kaga bazan ajjiye yarinya sai dai tashi kawai na shiga hakkin ta in nayi hakan, nasan yadda sha'awar mata take in na Turke ta a gida ni bani da abinda zai bata in shaidan ya rinjayi zuciyar ta ta fara zina fa? Ko lesbian ko mastarbution fa? Kaga alhakin hakan na kaina tunda ni na kasa bata abinda ya rataya a wuya na sakin ta shine solution Yasir, na Sanar da kai ne sabida zan rubuta mata saki daya zan bar kasar nan zanje Germany a duba ni bayan tafiya ta sai ka yiwa su Dady bayanin komai sabida kar zu zarge ta" ya karasa fadar hakan a sanyaye hawaye sun cika masa ido.
Sosai jikin Yasir yayi sanyi tausayin Ammar ya kama shi yace, "Kenan kana nufin bb abinda ya taba shiga tsakanin ku?."
"Sau daya na kusance ta Inda ace bata taba sex da ita ba zan iya kin sakin ta zuwa wani lokacin sabida kaga bata san ya abin yake ba ba wani damun ta zaiyi sosai ba amma kaga yanzu ka ta sani kamar an lasa mata Zuma a baki ne kaga ajjiye ta ba abin ne me yuwa ba shiyasa na yanke wannan hukuncin kawai gobe zan bar kasar nan ka saka min ido akan asibintin can kafin na dawo."
"Yanzu yaushe zaka dawo in ka tafi?".
" ban sani ba Yasir zanje dai kawai sai an ganni".
"Ikon Allah hakika wannan itace kaddarar rayuwa shine kuma Ga koshi Ga kwanan yunwa, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi amma ni Inda zakayi ta tawa baza ka sake ta Gaskiya."
Murmushi me ciwo yayi Ammar yayi kawai baice komai ba ya koma ya zauna ya dafe kai.
Kusa dashi Yasir ya zauna ya dafa shi cike da tausayawa yace, "Dan Allah kar ka tayar da hankalin ka sabida kaga yanayin ciwon ka kayi hakuri ka dauka wannan kaddara ce Allah ya baka ikon ciyewa kawai."
Baiyi magana ba sai daga kai da yayi ya mike kawai ya koma cikin gida.
A bakin kofar ta ya tsaya har zai shiga sai kuma ya fasa yana jin tashin maganar ta kadan-kadan, Amatullah kuwa waya take da Anwar duk da bata jin dadin yanayin ta amma haka take Sanar dashi komai yazo karshe.
Baya Ammar yayi ya jingina da bango yana salati, tabbas ya zama dole ya sake ta tun kafin ta fara zuwa suna haduwa da Anwar din dan yasan wani case na abokin sa matar da aka aura masa bata San sa tana da Wanda take so bayan auren haka take fita ta sunan makaranta taje wajan sa suyi hira tun yana iya hira har ya kai su ga zina ba sau daya ba ba kuma sau biyu ba har matar ta dauki cikin saurayin nata, girgiza kai yake hannun sa na kan kirjin sa ya mike dakyar ya shiga daki.
Kwanciya yayi akan gado kafin wani lokaci zazzabi me zafi ya rife shi yana kwance yana rawar sanyi yana kuma hawaye sabida rashin me tausayawa kansa, dakyar ya mike yasha magani ya koma ya kwanta zuciyar sa na bugawa.

YOU ARE READING
MASOYA UKU
Romanceta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.