Page 12

92 4 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lovers)_

_(True love, intense jealousy & betrayal)_

By
Neat Lady🥰

_Hakika jiya naga masoya fiye da yadda nake tunani nayi farin ciki naji dadin yadda kuke nuna min kauna da kulawa, ina tajin korafin ku dai akan na saka suna na gashi nan na saka kuma insha Allah zan cigaba da sawa, nagode muku Allah ya bar zumunci._

Not edited🤒

Page 12

Cikin fusata da b'acin Rai da kishi Ammar ya k'araso inda take bai tsaya wani tunani ba ya dauke ta da Mari kafin ta dawo hankalin ta ya sake dauke ta da wani marin, rudewa tayi ta saki kuka tana rike da kuncin ta gudu biyu, damkar hannun ta yayi yaja ta ya bude mota ya cilla ta ciki ya zagaya har ya bude zai shiga sai ya yatsa ya juyo ya kalli Anwar da ya zuba musu ido, tsaki yayi ya shiga motar ya fincike ta a guje yana tunanin dole ya dauki mataki akan Anwar.

Kuka take sosai a cikin mota nadamar abinda ta aikata da Dana sani sun taru sun Mata yawa, a guje yake Jan motar da burin sa kawai yaje gida lfy Dan shi kadan yasan yadda yake ji a kirjin sa, kukan da take yi ne ya cika Masa kunne ya taka burki ji kake kuwwwwww ya kalle ta a fusace yace, "na rantse da Allah in bakiyi min shiru ba sai na Miki dukan da sai kin kasa tashi wallahi" ya fada a fusace Yana nuna ta da yatsa yana wuci.

Babu shiri tayi shiru ta koma kukan kurame sabida yadda ta tsorata da lamarin sa, kwafa yayi ya kunna motar ya cigaba da tafiya. Allah nee ya kaisu gida lafiya sbd yadda Ammar yake jin zuciyar sa kamar zata fito waje sabida bala'in bugu har ya Fara daina gani sosai.

Yana yin parking din mota ya kwnatar da kansa jikin sitiyari Yana numfashi sama-sama, sai da ya samu mintina biyu a Haka sannan yayi karfin halin dagowa ya zuba Mata runanun idon sa yace, "fitar min a mota" ya fada cikin tsawa. Babu shiri ta bude ta fita jikin ta na rawa.

Tsayawa tayi ta kasa shiga ciki Dan Bata San me zata ce musu ba, gaban tane yake faduwa Jin yanayi a gidan hakan ya tabbatar Mata kowa Yana nan neman ta ake, a hankali ya fito daga motar bai ko kalle ta ba ya nufi cikin gidan ganin hakan ya saka itama tabi bayan sa jikin ta a sanyaye.

Yana shiga kallo ya dawo kansa umma ta Mike ta kalle shi tace, "Ammar ka samo....." Maganar ta makale ganin amatullah ta shigo kanta a kasa idon ta na zubar hawaye.

Yaya ce tayi wajan ta ta rike ta tace, "Amatullahi Ina Kika je haka? Me ya fitar dake a ranar auren ki uhum?" Shiru tayi ta kasa Basu amsa sabida tsoro da fargaba Mama ce tace, "Tambayar ki ake Ina Kika je?". Shiru ta sake yi Bata bada amsa ba sai hawaye dake fita a idon ta.

Cikin tsawa da hasala Dady yace, "Dan uban ki baza ki fada Mana inda Kika je ba sai na mare" jikin tane ya cigaba da rawa bakin na motsi Amma ta rasa me zata ce sai satar kallan Ammar take taji me zaice, cikin fusata Dady yayo kanta zai dake ta Ammar yayi saurin cewa "Dady sace ta akayi". Cak ya tsaya ya juyo ya kalli Ammar yace, "Sace ta akayi? Kamar ya kenan ban gane ba yi min bayani sosai".

Cikin karfin Hali Ammar yace, "cikin samarin tane wani ya sace ta badan Allah ya kaini wajan ba da yanzu sun bar garin da ita" kallan mamaki kowa yake yiwa Ammar mama tace, "Garin Yaya za'a shigo har gida a sace ta Ammar, gida da security ba babu Kai dai kawai kana so ka Kare tane."

"No! Mama ba Haka bne ba ta fito zata shiga babban gida aka dauke ta sumar da itama sukayi yanzu nan ta farfado a mota." Kallan rashin gaskiya Dady yayi masa yace, "Kai ya akayi kasan sace ta akayi bayan muna tare da Kai anan dazu?".

"Wani friend dina ne yayi min waya yake fada min a gaban sa hakan ya faru shine fitar da kaga nayi, wannan maganar duka a kyale ta ku barta taje ta huta" Yana Gama fadar hakan ya fice daga falon Yana hada hanya.

MASOYA UKUWhere stories live. Discover now