*MASOYA UKU*
_(The three lover's)__(True love,intense jealousy & betrayal)_
By
Neat LadyNot edited🤒
Dedicated to Ummu nabil😍
Special thanks to omamaAbubakar my wattapad fans🥰 thanks u for ur support i really apparent🥰
27
......... Sai da ya tabbatar ta galabaita ran ta gab yake da barin jikin ta sannan ya bude ya jawo ta kamar kayan wanki ya fito da ita ya barta a kofar dakin, fridge yaje ya bude ya dauko ruwa mai sanyi gaske bai tsaya wani tunani ba ya juye mata shi a jiki.
Bata farfad'o bai kuma damu ba ya saka kafa ya shure ta yayi ficewar sa daga gidan ma gabadaya.
*ANWAR*
Tunda ya bar gidan da Amatullah take yake jin sa wani iri zuciyar sa babu dadi ya kuma kasa mantawa da abinda yayi mata.
Yana zaune a gidan da ya koma yayi shiru ya rasa abinda yake masa dadi, tsaki yayi ya cillar da pillow dake wajan yana dora hannun sa a ka.
Ya ma rasa tunanin me zaiyi gashi Mum ta dame shi akan akan ya bata Amatullah su gaisa bata samun wayar ta ya rasa me zaice mata, ajiyar zuciya yayi a fili yace, "ya zanyi ne wai? Meyasa na kasa mantawa da ita? Ohffff anya na kyauta mata kuwa? Wannan shine sakamakon kaunar da ta nuna min? Gaskiya banyi mata adalci ba Allah bazai barni ba sai ya saka mata, yanzu ya zanyi kenan?".
_ka ku6utar da ita daga hannun Auwal iya haka ma da kayi baza ta manta da kai ba kuma zaka goge wani kaso daga cikin laifin da kayi mata_ zuciyar sa ta ba shi wannan shawarar.
Gasgata maganar yayi cike gamsuwa ya Mike ya fita daga gidan.
*AMATULLAH*
Sai da ta kwashe over one hour sannan ta farfad'o tana Jan numfashi sabida har lokacin jin ta take kamar tana cikin dakin, da batayi yin kurin mikewa ba sai kuka da take a wajan cike da tausayin kanta ta rasa me yake mata dadi.
Kuka take sosai ta rasa me taimakon ta sai da ta gaji sannan ta share hawayen ta da rarrafe ta shiga daki tana tunanin ta inda zata gudu da daga cikin gidan.
*AMNAH*😍
Duk wata kulawa da Amarya take mafarkin samu ta same ta a wajan Ammar sosai yake lalla6a kamar kwai duk da cikin zuciyar da cike take da tunanin halin da Amatullah take ciki amma baya nuna mata ya daure yana nuna mata kauna sosai.
Tana zaune a daki tayi shiru taji motsin sa a bayan ta, juyowa tayi suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kai sabida kunyar sa da take ji.
Zagayowa yayi ya zauna kusa da ita yace, "Tunanin me kike yi?."
Wasa take da zoben hannun ta kanta a kasa tace, "Babu komai."
"Hmmmm kina tunanin abinda ya raba ni da Amatullah ko?" Ya fada yana kallan ta.
Sunkuyar da kai ta sakeyi bata amsa ba ya gyara zama yace, "banga laifin ki ba dan kinyi wannan tunanin amma kar ki dauke ni ki saka ni cikin maza masu auri saki ba waccan ma na fada miki kaddara ce kuma ita wannan kaddarar itace ta haduwar mu, dan in badan na rabu da Amatullah ba da yanzu banje Inda zan ganki ba amma duk da haka zan fada miki sabida na rage miki shakku a ranki, kina jina?".
Daga kai tayi alamun eh.
"Kwanan auren sha hudu na saki Amatullah badan ina so ba sai dan shine mafita da masalaha a gare mu, a cikin wannan kwanakin na gamu da rashin lafiyar da bazan iya saukewa Amatullah hakkin ta na aure dake kaina ba nasan kema kin san yadda sha'awar mace take a jikin ta kuma mace kamar ta sabuwar Amarya in na barta a lokacin ban san lokacin warkewa ta ba na zalunce ya gaskiya, bata sani ba nima ban sai takardar saki ta gani ni kuma na bar kasar shine na koma Germany a zahiri kamar karatu nake amma a bad'ini ganin likita nake yi da zaman banzan da nake yi sai na Shiga makaranta."

CZYTASZ
MASOYA UKU
Romansta aure shi badan tana so ba sai Dan biyayya yayin da shi Kuma ita yake bala'in so, tayiwa saurayin alkwarin ko tayi aure baza ta rabu dashi ba zasu kasance tare.