Page 13

89 4 0
                                    

*MASOYA UKU*
_(The three lovers)_


_(True love, intense jealousy & betrayal)_

By
Neat Lady😍

Not edited🤒

Page 13

Isar su gida suka shiga direct part din Ammar suka wuce bai tsaya Bata lokaci ba ya fada bandaki ya watsa ruwa ya dauro alwala ya tayar da sallolin da ake binsa shi Kuma Yasir ya fita daga dakin, part din Umma ya wuce Yan biki ana zazzaune ana ta Shan Hira , gaisawa sukayi da mutanen parlourn snn ya wuce cikin wjan umma.

A tsaye ya same ta a kofar daki tana Shirin fitowa parlour tana ganin Yasir ta  tsaya tace, "Yasir wai Ina kuka shige tun d'azu ana neman ku Anki a samu Koda wayar daya daga cikin ku ma, Ina kuka je?". Yasir yace, "Umma Daman Ammar ne ciwon sa yaso ya tashi Amma bai tashi ba shine muka je asibiti aka saka Masa ruwa da da allurai yanzu Haka Mun dawo Yana dakin sa ma."

"Subahanallah! Yasir me yasa baku sanar Dani ba tun dazu? Amma dai yaji sauki ko". "Alhamdulillah yaji sauki sosai Dady ne yace Kar a fad'a muku Kuma na d'auka ma anga fitar mu anzo a Sanar dake, yaji sauki sosai Yana d'aki sallah na baro shi Yana yi."

Umma tace, "To shikenan Allah ya Kara lfy, bara muje mu Masa sannu, sannun ka kaima da k'okarin" murmushi yayi ya juya ya bar wajan.

Gidan Mama ta nufa ana zazzaune a parlour ana Hira ya shigo ya gaishe su yace, "Dan Allah Mama fa?" D'aya daga cikin bakin tace, "Tana part din Yaya". Juyawa yayi tare da fadin nagode ya fita daga parlourn.

Part din Yaya ya nufa a parlour ya same su ita da Yaya da Baba Asiya wato kanwar mahaifin su, Zama yayi yace, "Mama sannun ku ya taro?" Mama ta Masa da, "taro alhamdulillah, kune masu taro ai ku da kuke angwaye." Murmushi yayi Yaya tayi caraf tace, "Ina Ammar din ne Wai? Kodan ba yau za'a Kai Masa matar ba ya saka ya b'oye? Ya fito ai tunda gobe i yanzu matar sa tana tare dashi." Kallan ta Yasir yayi yace, "Kar ki dau hakkin bawan Allah bashi da Lafiya fa yanzu aka sallamo mu daga asibiti."

A tare suka furta subahanallah me ya same shi, Yasir ya amsa da, "ciwon sane yaso tashi Amma dai bai tashin ba ya dai kusa, likitan yace akwai abinda ya Bata Masa Rai sosai shine dalili."

Yaya ta karyar da Kai tace, "Yo ya wuce wancan Yar banzar yarinyar Amatullahi nifa daman ban yarda da wani sace ta akayi ba kawai dai ya fada ne, tun lokacin yanayin sa ba dai-dai yake ba akwai abinda ya faru ya b'oye ne kawai."

Baba asiya tace, "To ai gwara muje mu duba shi daga baya ayi maganar," ta fada tana mikewa, Mik'ewa Yaya da Mama sukayi suka fito suka nufi cikin gidan sarki.

A can suka tarar da Umma a zaune sabida ya samu bacci kuma ba'a so ana tada shi in yana bacci,  Yaya ta kalle shi tace, "Oh ji yadda ya fada lkc daya, Allah ya Yaye Masa wannan cuta dai Kuma ta rasa lokacin  da zata tashi sai yanzu da ya angwance."

"Allah ya bashi lfy, ai gwara muje tunda yayi bacci Kar mu tashe shi," Mama ta fada tana niyar fitowa, tare suka fito gabadayan su, Yaya tace, "To mu shiga gidan amarya Mana tunda dai Mun fito". Tsayawa Umma da Mama sukayi Yaya ta kalle su Mama tace, "sai Kun dawo" tab'e baki Yaya tayi tace, "Gulma" suka tafi ita da Baba asiya.

Wata Yar kofa suka bude suka shiga sai gasu a parking space din gidan Amatullah, kallan gidan Yaya tayi ta saki tsaki tace, "ko uwar meye babu a gidan da za'ace sai gobe za'a kawo amaryar oho" ta fad'a suna shiga cikin gidan, Masha Allah kawai baba Asiya take fad'a an Gama komai a gidan an saka komai gida ya dau haske yayi kyau, parlour ne guda biyu a kasa da bedroom guda biyu da kitchen da dining room, sama Kuma parlour ne guda daya da bedroom biyu da varanda wacce aka saka Mata lilo da fridge, in ka zauna akan lilon kana hango mutanen harabar gidan sarki.

MASOYA UKUTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang