page 2

5.1K 436 25
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                                      02
**********
     "Wainikam Islam ina zakijene haka? Goman dare yarigada ya wuce fa? Kuma sanin kankine munada test gobe morning abinma daya sanya nazo hostel kenan sabida in sanmu nutsuwar karatu" tsaki taja ta kunna turaren wuta me dad'in qamshi ta tsuguna aciki bayan ta lullub'e jikinta da barko batare data kulata ba, ita kuwa da abin magana baya isarta se cewa takuma yi

"Islam wainikam kinawa kanki adalci kenan kike gani? Kinawa iyayenki adalci kenan islam, bakya jin tsoron Allah kenan islam, bakya gudun mutuwar ki tazo miki kina cikkn wannan halin, bakya tsoron cututtukan zamanin nan, bakya gujewa fad'awa cikin wutar Allah, bakya tsoron 'yq'yayenki su tambayeki game da rayuwar daza'a   goranta musu kinyi islam? Dan Allah islam ki rufa mana asiri ki dawo hanyar daya dace" miqewa tae

"Ki adana kalamanki Nancy!!! Wata qil zasu miki amfani anan gaba, idan kuma zaki dauken lalurorin dake kaina ne na komai sena fasa sana'ata na zauna kimun su, gaskia wlhy kin soma isana huldar nan fa bawai dole bace kuma ina qabarinki daban nawa daban? To meye na damuwa?" Qwallan ta ta share daya silalo mata bata qara cewa komai ba.....Allah ya gani tanason  Islam bata mata fatan fad'awa halaka amma yazatayi iyaye suna suke taka muhimmiyar rawa wani xubin wurin gurb'acewar tarbiyan yaran su.... Babu me kulawa da karatun Islam, babu wanda yake damuwa da suturunta babu wanda ya tab'a cewa islam ina kima samo abu kaza!!! Yaya tarbiya zata ingantu? Yaya yarinya bazatabi ko wacce iriyar hanya ta nemi kud'i ba??.....

********
   Tunda ta soma cin hanyar motar ke biye da ita tana yin tata tafiyar tamkar hawainiya.... Ba ai mata magana ba kazalika ba'a dena binta ba, tundaga gate din na jami'a har zuwa gidan man ada!! Ganin ta yanki dogon titin Rima Tv dayake tsit ya sanya ma mallakin motar yaje yae parking a gaba da ita kad'an kana ya bud'e motar tashi qirar range rover 2018 black wuluk ya fita, ji yajingina jikin motar  ya hard'e hannayenshi  asaman qirjinsa yana nazarin tafiyar nutsuwar da yarinyar keyi, yanda tae tamkar ma bata gan shiba shine  abinda yafi bashi mamaki dabita sabida ya saba harka da en matan jami'a wannan slow dayaje badole seya tsayar dasuba su zasu tsaya har sumai tayin number wayar su kuwa, gabanta yasha yace

"Kenake bi en makaranta Ina san zanyi magana dake kina mun yanga, dan Allah ki bani time d'inki" ya soma furto maganar tamkar  wanda akawa dole" rausayar da kanta tae kantace

"Bana saurarar mazaje a bakin titi, bana magana da maza akan hanya, gidanmu babu nisa danan wajen amma idan ka matsu zaka iya ci gaba da bina zuwa qofar gidan mu" kallon mamaki ya bita dashi, tsakani da Allah kuwa tai tafiyarta ya jima yana kallonta kanya tashi motarsa yabita a baya..... Yaso ya basar amma ya kasa,yaso ya wuce abinshi  amma yarasa dalilin dayisa zuciyarsa take azalzalarsa akan yarinyar dako fuskarta be tab'a gani ba kasancewar da niqabi sanye a fuskarta ga madubin data sanya baqi wuluk ta rufe idanta dashi......har duka isa qofar gidan yana biye da ita, ita kuwa tae shigewarta ta barshi a waje yana mamakin hali irin nata!!!!! Ganin yafi 20 mns tsaye bata dawo ba ya sanyashi kiran wani yaro yace dashi..

"Kasan budurwar dake nan gidan yaro?" Kallon sa yaron yae

"Susu biyu ne se qaramar su, Akwai Ummul akwai kuma Nanuwa wacce aciki?" Shafa tsajensa yae

"En matan guda biyu inaga daya ce daga cikin su a jami'a take kaje kamun kiranta bansan sunan taba, amma dai ba jimawa tashiga gidan kace nace wacce take sanye da niqabi da mudubi acikin kalar kaya koraye" juyawa yaron yae yace

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now