page 21

3.4K 324 28
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

*Assalamu Alaikum...masoya kuma makaranta wannan novel din ina me baku hakurin abinda zan fada, dan Allah kuyi hakuri daga page 20 na jiya nadena baiwa kowa daga farko, inasha wahala wurin turawa gaskia, dan Allah dukmeso ta nema a group kotaje wattpad nagode sosai da qauna.*

*Maman Ramly wannan shafin nakine kyaita, ina godiya sosai da comment*
                              21

Haka Anty Reedah da mijinta Dr. Muheeb suka shigo suka samesu, ya kasa ya tsare tamkar ya rungume ta yakeji ita kuwa islam ta kifa kanta jikin gadon tanata kukanta a hankali.......Hannun Maheer d'aya  tsaqale acikin na patient d'in yanzu kam qwallan ma ya gagara yi  se numfarfashi yake saukewa da sauri da sauri itakam Hafsat batasan ina kanta yake ba oxygn mane aka sanya mata, kallon  muheeb yae ya saketa da sauri yaje wurin shi ya riqe masa hannu

"Ka taimaki baiwar Allah nan muheeb banaso acire mata qafa qaramar yarinya ce muheeb, dan Allah ka dubi maraicinta ko aure batayiba ace a gundule mata qafarta waze aureta?" Rungumeshi Muheeb yae

"Calm down Twin kaji, komai zezo da sauqi na nemi transfer ma zuwa asibitin frnd dina me zaman kanta ta qashi dake kano, ni kasan ba ainahin wurin qashi nake ba amma nasan sosai akan bangare, zan duba qafar kuma yanzu da condition dinnan idan muka dauketa komai ze iya faruwa se dole an ciwo kan numfashin ta, abu na gaba shine ka sanar wa iyayenta cewar ka kama mutanen dasuka saceta sedai ka boye sunan yayarka dana qawar ta kakuma ce zaka dauki mataki akansu karka fadi wani dalili se bakasan komai ba faqat" binshi yae da kallo shikuwa ya sakeshi yaje ya duba qafar.....tabbas karaya ce ta wurin Ankle dinta sedai wannan karayar bazata wuce sati uku ba, kuma a yanda yaga hoton babu wani nama dataci sosai sedai fa tabbas koda zasu gyara qafar har abada bazata tab'a dawowa normal ba seta dan karkace idan akayi sa'a karkacewar bazata nuna ba amma idan akai rashin sa'a sedai yazamana qafar ta karkace yanda ze nuna sosai kamar me dingishi ko kurkuwa ma dan idan daya tafi daya tsyi dole seda sanda.....dafe kanshi yae cikin bacin rai anty Nasara tayi aiki irin na jahilai kuma jakai, talakan data raina yafita har a wurin Allah indai ze fita jin tsoron Allah......waigowa yae ya bayyanawa Maheer abinda yake hange ya qara da cewar

"Abari amma Dr. Sunusi yazo muji nashi tunda a wannan gefen guru ne yafini sani, sabida haka ka shirya muje gidansu hafsat a gaya musu abinda ya dace su sani sannan aga yanda zamui mu koma kano da ita amma gaskia dole se anyi amfani da private jet na Abba wurin daukarta" Hakan kuwa akayi Baba azumi se gwatsina takeyi akan qaryane seda sukaje taga yanayin hafsat itama seda tae qwallah jin an daureta a tsaye kusan watanni biyu ga kuma yanda jan buzu ya dawo kala kala ajiki, Mahaifiyar hafsat kasa kuka tae se zare ido takeyi dukta rikice........

*****************
     Maheer ga mahaifiyar hafsat a asibiti amma ya kasa ya tsare yaje ya riqe hannunta yanata mata addu'a yana tofa mata yana ganin kota farka a firgice zata tashi dukda likitan ya sanar masa abincin dasuka bata ta hanci ya taimaka mata zata farfad'o anytime soon.....amma cire ox da aka daura mata,ganin haka ya sanya ta koma qaramin dakin dake farkon shigowa cikin dakin....

Hannunta ta motsa kad'an dayake yana riqe da hannun seya kaiwa wurin kallo ya dawo da dubanshi zuwa gareta a hankali ta bud'e idanta qura masa idanta tae na wasu en daqiqu batare data qifta ba shi dinma kallon ta yake har yana washe baki ya matsa daf da ita ya tallafi kanta

"Sannu Hafsat ya jikinki kin farka, inane yake miki ciwo sannu kinji yanzu kin dawo gida  komai ya wuce ki kwantar da hankalin ki" kallon sa tae alamun bata fahimtar komai ya kalleta sosai ya fara sunsuno wani abin, saketa yae yaje ya kira Babarta itama tazo tayi maganar harta gaji amma shiru hafsat ba amsa se kallon su takeyi tamkar wasu wawaye.......Ana haka ummul ta shigo itada Ameen, sukai kanta amma ga alama ba wanda ta gane se kallon mutane takeyi, fareedah ma da Muheeb dasuka gama kaiwa qarshen neman hanyar kaita kano suka shigo......da kanshi muheeb ya dubata yanda yaga kowa ya zagayeta har islam itama tazo amma batawa kowa magana ba se kallon su takeyi

"Lost of memory!" Ya furta a hankali bayan ya gama tab'a kanta dako ina amma bata ko damuba se binshi takeyi da ido, wannan yarinyar taga rayuwa ya furta a sarari, cikin gaggawa ya nemi hoton qwalwa batare daya musu bayani ba kiran wani dr. Kurun yae ya qara dubata sukazo aka tafi da ita hoton Kai....

Tunda aka gayawa maheer da sauran mutane cewar a kai ake hangen matsalar se suka rikice, abin ya daurewa kowa kai ga ummul dama tana cikin damuwa, Ameen kullum sesunyi fad'a yana cewa ya auretane danyaci riba da yaran dazata haifa amma wata biyu shiru babu ciki, tana mamakin sa ko shekaru biyu tayi batai ciki ba aibata cancanci hakan daga gareshi ba zaman su yaqi dad'i, har yana cewa dole tasan yanda zatai da samu ciki inba haka ba akwai damuwa cox bazeyi asaran kudinsa a banza ba...... Maheer  ko yanzu mota ya koma yarasa meyasa yakeji kamar ana cewa za'a kashe shi duk sanda akace ga abinda ke damun hafsat, kwana  biyu ma beje lecture ba, yanzu baya iya koda qwalla ne akan Hafsat tun ranar dasuka baro gidan nasara take kiransa baya d'auka sam!!  Har dakanta taje ta gayawa ummansu abinda tae tare da yin qarairayi ta kare kanta  umman tamata fada amma ta yarda bada hannunta akawa er mutane hakan ba....Abba ne kawai besan miyan da ake shaba sabida baya garin.

*************
    Bincike ya nuna qwalwar hafsa babu inda ya tab'u amma fa tayi lossing memory dinta gaba d'aya wanda suke saka ran ya dawo bada jimawa ba, a wannan ranar suka wuce kano domin yiwa hafsat aikin na qafar.......

Mom Nu'aiym

*mu hadu a page na gaba anjima da yardar Allah.

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now