page 50

6.5K 372 52
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

          50

Jikin islam har rawa yakeyi sanda ta dawo cikin gidan, takardan data barshi akan gado ta d'auka amma ta gagara bud'ewa, tunawan datai da umma me ya bata damar juyawa tana d'ingishi da k'afarta ko 'yarta bata tsaya karb'a ba ta juya a sittin, da kanta tai tuk'i zuwa asibitin da takardan a hannunta, bata tsammanin ganin kowa a ICH wannan ya bata daman zuwa office na fareedah dan kuwa anan ta barsu, koda taje kuwa tai sa'a suna nan, wurin umma taje ta durk'usa da k'afufuwan ta tana kuka

"Umma dan Allah ki tallafeni ki ceceni ki kuma agajeni, Maheer ya sakeni umma kinga takardan daya bani wai inaso zan yi kisa harso biyu, wlhy umma k'addarane ya fad'o damu nida Hafsat amma  wlhy garin ceton tane ma nima na fad'o, ki cewa maheer ya taimakeni ya miyar dani d'akina wlhy shine farin cikina dan Allah kimun tallafi" Tunda Islam ta soma magana umman ke kallonta ta gagara koda motsi, ko ba komai ta tsorata da yanayin yaronta d'azu be tab'a mata kwatankwacin yanda yae ba d'azu  hankalinta yakai k'ololuwar b'aci tama rasa me zatace, yanzu mezata cewa Abba idan yaji? Farida ce tai k'arfin halin karb'ar takardan ta bud'e ta soma karantawa da sauri wata wawiyar ajiyan zuciya ta sauke ta zauna dafe da kai kantace

"Saki d'aya ne Umma,  dan Allah awa tufkar hanci, dan gaskia wannan ya zama hauka, daga faruwar abu bakada ilimi akanshi blindly kurin ka sako saki, an gayawa Maheer aure abun wasa ne wai? Ko kuma muya mayar shashashai? Ubanwaye ma yace dashi islam ta wurgo Hafsat d'in? Ita ta wurgo ta kuma suka fad'o a tare? Gaskia umma bakwa duba lamarin rayuwar maheer yanda ya dace abubuwa yakeyi gaba gad'i, ko zancen auren nan na hafsat haka yae iskancin nan yazo ya narke kuka amince masa batare dakoda jin ra'ayin yarinyar ba, wannan kurin ya isa ya haddasa fitina, tun wuri gwara a kirashi wlhy a nuna masa kuskurensa" Nisawa Umman tai kanta rik'o hannun islam

"Baze k'ara aikata wannan kuskuren ba inhar dai nice na haifesa, sannan ki koma gidan ki yanzu karnaji zancen kin tafi gidanku, karma ki gaya musu wannan mugun labarin, zanga maheer d'in ai"   Godiya islam tayi sannan ta nemi komawa hanyar gida....

****------****
    Maheer kai tsaye asibiti ya koma, Wurin da Hafsat take yaje ya tsaya wurin glass daze rik'a hangota, se k'wallan dake wanko masa ziyarar ba zata yake zubarwa, yayinda sakin dayawa islam ya masa tsaye a wuya, yana wa islam wani irin so dabaya tunanin amma tab'a halittar irin sa, tafiyar da yai yabar nata gida yasha wahalan rashin ta, har mamakin kansa yakeyi ya daurene kurun sabida yanuna mata iya karta, yanaji ajikinsa idan yaje gidan zuwa anjima ze dakatar da ita akan tafiyar da tai niyan yi....ya kasa barin hafsat ne tausayinta yakeji kamar me,  baiwar Allah tun tasowar ta a wahala take har yanzu...yana tsaye a wurin ya kusa da sauyawar yanayin kwanciyarta alamun ta motsa, be b'ata lokaci me tsawo ba ya  juya zuwa officr na Fareedah don sanar mata acen ya tarar dasu rai a b'ace, umman ma ta had'a fuska be damuba ya gayawa Fareedah a gaggauce suka fita zuwa ICH d'in..

Dr. Sam yarigasu isa wurin sabida shi dama yana aikin yamma ne, taimakon gaggawa ya bata ganin tayi regaining conciousnes nata, dama sun bada 24 hours ne idan bata farfad'o bama suna ganin se wani ikon Allah, idan kuma ta farfad'o Alhamdulillah....to 1 hour ya rage 24 hours din ya cika shisa ma yazo dubata, yaji dad'i sosai ganin ta farfad'o sedai batai masa magana ba, se binsa da kallo takeyi haka aka hana musu shiga su Maheer Fareeda ne kurun ta samu damar shigowa inda taketa murna dan suna shirin fidda rai da ita ne..

****----***
    Alhj Baba ba k'aramun tashin hankali yake cikiba, ganin babban mutum ya matsa lamba akan anemo masa shi, Abban Maheer ya matsa matuk'a akan  neman sa, wannan ne ya sanya ya gudu daga Nigeria gaba d'aya zuwa Ghana tafiyan dabesan ran dawowa ba sabida da asirinsa ya tonu gwara a tsinta gawar sa......Ga cutar dayawa d'an uwansa (Mahaifin Ameenu") sabida rikon amanar aminun ya bashi amma yaketa hallaka masa 'ya'ya yasan hakki kadai seyaci qaniyar sa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 04, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now