page 33

3.8K 344 37
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                               33
Alhj Baba ya shiga rud'u da tashin hankali me yawan gaske, neman Ameenu yake hankalinsa a tashe, duk garuruwan dayake tsammanin ganinsa yaje amma ba labarin sa....a gaba ya sanya  Babban yaron Ameenu da izgilanchi iri iri dakuma  treatening nashi akan hallakar da iyayen sa...dolensa yakaishi gidan Ameenu na kano inda suka tarar baya nan, tsammanin Alhaj Baba zuwa yanzu shine Ameen yabar k'asar kwata kwata don haka ya kud'irta aranshi idan ma ya kamashi har 'yar tashi ze yanka agabanshi besan haka bane dabe nuna masa ze karbi matar tasaba, kuma matarsa seya wulak'antata ya sanya dukkanin samarin dake masa aiki sun hauta agabansa, duk gatan daya masa ya d'aurasa akan hanyar samun kud'i zema iya cewa gabaki d'aya yafishi samun kud'in gefen  wannan harkar yaya ze masa haka?! Duk wani hanyar daze sanya ya ganeshi ya gujeta danko ko kud'ad'e ya dena cirewa ta banking sa to a ina ze samu kud'i? Hankalin Alhj Baba fa ba karamun tashi yayi ba......

*******************
    Ameenu kuwa dabara ya masa, sabida yasan yanda sun tab'a samun yaron dayak'i bada yarinyar sa da matarsa ta hanyar inda yacire kud'ad'e banki ya gano shi, wannan ya sanya yawa abokin shi dasuke huld'ar fata waya wanda dama akwai kud'insa a hannunsa ya tura masa 3 million d'insa acikin acc d'in Ummul dako ATM nata batasan inda yake ba seda yasha wahala ma tukunna ya samu aka mata ATM d'in yake zarar kud'ad'en suna lalurarsu har yanka yawa Nana khadeejah aketa ji da iya, ankuma kaisu asibiti itada uwarta an duba lafiyar su da komai Alhamdulillah..... 

***************

  Tun faruwar wannan lamarin Nancy bata cikin nutsuwar ta, ta rasa dalilinta najin hakan game da Maheer, bazatace ta tsaneshi ba amma sam batajin sansa aranta kamar da, kodan tana jin tsananin takaicin islam ne yasa ko meye dalilin ta oho? Tasani ada ta bautawa san Maheer takuma sha d'awainiyar begenshi amma zuwa yanzu tunani take kaman zallan burgewa ne kawai baso a ranta, ta misibar shak'a da wannan izgilancin daya mata, shime dala kenan ko? Masu kud'i kenan ko? An had'u da kwad'ayayyun iyayenta anje basu abun duniya sun bada aurenta batare da izinin taba sam!  Bata masan anayiba, banda Abba ma daya nemi amincewarta Baba iro ko gaya mata beyi ba sanda ta kirashi ma seya nemi tsinemata akan hakk'inta....haka mamanta ma data kirata seta ce ta amince mesa basu ko duba kawaici ba? Kodan islam ai sace noo ko? Wannan auren ta kudiri niyyan wahalar da Maheer akanshi kuma ze ganene.....

***************
    Sosai suka zanta da Ameenu gameda abubuwan dayake aikatawa da wanda ke gudana a yanzu, Ran Maheer ya b'aci da shashamcin  Ameen....ze dinga rayuwa kenan acikin tsoro da b'oyo se kace d'an fashi, sun jima suna meman mafita, basuda dabarar dayafi ya kwashe 'en kud'ad'ensa ya koma wata k'asar xuwa wani lokaci shida iyalansa wannan kuwa ze d'auki lokaci dan haka gwara su zauna da shiri....Ameenu ya sanya kamala harkan visa dinsu da komai daya shafi barin k'asar.

**************
      London
Koda Jirgin su maheer ya dira a london seda k'irjin sa ya doka yana tunanin yanda ze kalli Hafsat, yana tunanin abubuwa da yawa masu dama....haka ya isa gidan jikin sa ba k'wari ko kad'an da sallamar sa ya shiga cikin parlor d'in inda ya tarar  sophie ce  zaune tare da Nancy suna kallo sunashan Banana smoothie...a tare suka mik'a suka gayar dashi inda Sophie ta k'arb'i jakar hannunsa Nancy kuma ta k'arbi wacce ya ciro daga bayan shi adaidai lokacin da Islam ke dannowa parlor d'in kai, da sauri har tana had'awa da gudu tazo ta sanya hannu ta tureta ta karb'e jakar hannun shi

"Kajimun  yarinya da iskanci fa, kina agola dan er masu gida ta karb'i jakar hannun yayanta kekuma asuwa da wani salon karuwan cin zakizo kice sekin karb'a" kalaman na islam ba k'aramun dakarwa Hafsat k'irji sukayi ba  gashi turin data mata seda ta fad'i...k'ura mata ido Hafsat tayi ta kasa furta komai yayinda  sophie iyayen fitina ta gagara hak'uri tace cikeda tsiwa

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now