page 40

3.8K 326 19
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

        40

"Inna kina kallon kuwa Maheer ya soma sauyawa? Bakya kula da yanayinsa tun zuwanki dabashi yace kizoba dase nace wataqil beso kika zoba"  Tab'e baki tayi

"Waccen mayyar ce dai  keso ta zuzuta masa tunani, na mata gargad'i akanshi, bazan lamunci wata banza ta hanamu cin duniyar mu da tsinke ba, gidan talakawa ake kishiya idan ka shiga gidan masu dashi wlhy baka bari wata tashigo maka, Allah ya rufa mana asiri bazamu bari ta tona mana asiri ba, Allah ya sani bazan lamun taba" Gyaran zama Islam tayi

"Inna to meye abin yi? Nifa ina ganin kamar dan itama yaje cen gidan da zama, nasan ba'a zama gun me jego amma ina kwana biyunnan duk tare muka yisu, kuma se yanzu ya koma cen" kallonta innar tayi

"To wai meye dalilin sa na barin gidan ma dahar kika barsa ya tafi"

"To inna kinga cewa fa yayi dani wai tunda kizo yanajin kunya dole ya koma cen" Goron hannunta ta gutsura

"Tunda haka yace ki d'auka haka d'inne kuma kinga ai baze yiyu ma ace wai yaje guntaba ga qanninsa agidan, kedai kurin mu sanya ido muna ganin abinda be mana ba, mu tashi tsaye mu nemi mafita"

"Hakane Inna dolene ma wannan ai".

***************
    Ummul se mugwayen mafarkai takeyi da matsafa wai sun farka cikin ta sun ciro mata baby sun kashe babyn itama sun kasheta, mutanen dabatasan ko waye ba amma a mafarkin tana ganin su kamar matsafa da jajayen kaya, abin ya dameta sabida kusan sati d'aya kullum setayi, ta rasa wa zata gayawa  wannan maganar, Naja take gayawa tanata kuka

" wlhy kinsan  Allah hankalina a tashe yake, musamman da mafarkin ke nunamun suna yawan cin galaba akaina, nasani hakk'ine wlhy hakk'in Nanuwa ne yake d'awainiya dani, duk wata masifa danake gani Baba Azumice ta janyomun, sabida tun asali ni. Ameen bani yace yanaso ba yar uwata yakeso k'anwata, amma  Babar mu ta dage seda ta juye abun a kaina, watak'il kuma ajalina ta gayyato da hannunta, dan wlhy ina cikin damuwa da firgici....." Nisawa Naja tayi

"Anty kiyi hakuri kuma ki dinga adu'a inshaa Allahu lapiya lau zaki sauka kamar yanda yanzu Nana ta girma ta zama big girl haka zaki haife cikin ki lapiya lapiya da yardar Allah" Shiru tayi tana nazarin rayuwar duniya ko banda k'addara  akwai hakk'in cin amana kenan haka wani yake da Allah, da zaran ka masa cuta tun a duniya zaka soma fanshewa...

Zuwa yanzu Baba Azumi ta soma rikicewa da rashin Ummul, tana cikin tsananin damuwar rashin ta, abubuwa sun soma yi mata yawa gashi dai Ameenu yana iyakar k'ok'arin sa akansu amma ita hankalinta yafi kwanciya akan taga yarinyar ta a kusa da ita.....

***************
     Duk juyin dazatayi shi take gani take kuma tunawa, ya tsaya a ranta yanayin wasan daya mata jiya, har Allah Allah takeyi daren yau yayi su koma kwanciya wuri d'aya yafita tun safe be dawo ba amma bazatace ga second d'aya daya shud'e batare da tunanin sa aranta ba, a jiyan ya mata abubuwan dasuka tsaya a ranta matuk'a, Ashe dama haka yaa Maheer yake, dama Ashe akwai irin wannan fain cikin da ake cewa yana saka mutum kuka? Ita harga Allah jiya seda tayi k'wallah dayake mata wasan nin dako sanda take k'arama bazata ce ga sanda tayi irin suba, daren jiya har doki ya mata, seda ya tabbatar ya sanyata bacci ma tukunna shiya kwanta nashi baccin tana......... Wuraren k'arfe bakwai ta gota ya dawo gidan, kai tsaye d'akinsa ya nufa, harya shiga ya fito yayi kiran sophie ta kira masa Nancy, cikin mintuna k'alilan segata a d'akin, sanye acikin shigar ta ta alfarma doguwar rigan material me laushi, da akwai aljihu aduka gefen na rigar tayi kyau sosai babu kallabi a kanta, se sumar kanta data zube a k'asa batare data tufe shiba, wanda tsayinsa ya kusa zuwa kan mazaunanta

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now