page 45

3.1K 304 18
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

        45
Harara Fareedah ta wurgawa Anty Nasara

"Haba Anty, waime ya sanya arayuwa ke bakya k'aunar kiga an rabu lafiya ne?" Huci ta somayi

"Wlhy se umma taga wannan iskancin,dama zaman kenan da kukeyi a london, shisa mana matarka taga abinda ta gani ta tashi hankalinta...... Shidai kan Hafsat yai yaci gaba da jijjigata, anan ne mommy tashigo hankalinta bekaita wurinba seda Nasara ta nuna mata

" kalli Hafsat Umma, Maheer yayi zina da ita yau Allah ya toni asirin su" wanka mata lafiyayyen mari umma tai kai tsaye

"Maza Fareeda kauce mun zan duba ta, ke kuma Nasara karki fita tsaya a wurin" tafad'a tana tunkarar Hafsat d'in da kanta, Dubawa tayi sannan tace

" ki suturta mata jikinta mijinta ya dauketa kukaita mota kije asibitin ku da ita, lallai a dubata da kyau, kinsan matsalarta akuma duba wannan raunin dataji ajikinta" To fareeda tace aka daura mata zani da hijab Maheer ya kinkimeta, har lokacin Anty Nasara se sauke numfarfashin wahala takeyi, bayan sun fito umma ta kalleta

"Muje d'akina"  ta furta, sannan batare data jira cewarta ba ta juya, seda Umma tajima da fita sannan tabi bayanta bayan ta zaro wayarta ta danna lambar islam

"Ke wlhy, wawiya ce toki sani wlhy yaudai da idona na kama Maheer da Hafsat sunyi zina, in tak'aice miki ma jini ya b'alle mata inaga dama sun saba yau akazoyi kila cikin shege ne da ita ya b'are, an kwasheta a sume kije tana asibitin su  Fareedah ki ganewa idanki" zabura islam tayi tana salallami, lokaci d'aya ta soma kuka, ta rasa wanda zata gayawa tunda innan ta ta wuce!!!!!! Zarar Hijabi tai ta zura ta barwa yarinyar da aka kawo mata me reno mamaa ta fita da sauri, driver na ganinta ya taso da escort biyu, ta shige mota suka cira!

**********

    Ba wani abu bane ciwon daine ya tashiwa hafsat, amma da sauk'i bekai wancen ba, an samu ta farfad'o sedai ta gagara bari a mata d'inkin wurin se kuka takeyi tana  cewa tsoro takeji,  Dr. Samha aka k'ara baiwa damar dubata inda kai tsaye tace za'a iya barin wurin hakan yankuwar bekai ace se anmata d'inki ba, sabida ba wani sosai bane daze gagara warkewa da ruwan d'imi, a cikin satima idan jikinta yanada kyau zeyi healing da kanshi, da wannan aka barta akan baza'a mata d'inkinba.....Anty Fareeda ta kalli Maheer sunbar hafsat tana bacci sun koma office d'in fareeda tace dashi

"Maheer meya kaika? Wane haukan ya kaika hayayyak'ewa mace haka, bazamuce baka saba ba tunda yake kanada mata harda arziqin 'ya, meye na yuwa mace wannan hawan k'awarar?...." Lokaci d'aya kunya ta dabaibaye Maheer yace

"Anty Reedah ba haka bane ba wlhy bansan ma anyi ba, bani acikin hayyacina sedaga baya" D'an murmushi tayi bataso ta k'ureshi ta kula kalaman suna masa nauyin fad'a

"Babu damuwa, amma kanada aiki, dan yarinyar seta dinga gudunka yanzu kam...kuma ka sani seka barta ta huta koda na one month ne, and nxt time plss kamata a hankali, hanyar budurwa komai yawan shekarunta se'a hankali ake mata wannan dakayi yanzu, a hankali zakabi da ita idanma tanada k'arancin ni'ima seka nemi wata hanyar ta sauk'ak'a mata, barema ina zancen saukar ni'ima ga yarinyar datake a tsananin tsorace, Dr. Samha tace ko suman datayi tsorone, dan Allah ka rik'a yin komai a hankali, lastly kuma kaida Anty Nasara kasan dai seta gayawa matar ka ko?"

*************
   "Ke Nasara waime sa koda wane lokaci kikeyin abu kamar wata k'ank'anuwar yarinya ne? Tayaya zaki kalli idon k'aninki kice masa yana zina?" Cikin takaici ta furta

"Yaro da matarsa dan rashin tarbiya seya kawo mace cikin gidan ubansa ya hayayyak'e mata har haka, inada yak'inin cikine da ita Allah ya toni asirinsu"

"Waike bakida hankaline? Toki sani Hafsat Matar Maheer ce, ubanku da kanshi ya d'aura auren su, yace kar a gayawa kowa, ban gaya kiki bane ba sabida nasab halinki sarai, kuma ko yanzu akul d'inki kika gayawa matarsa wannan maganar kotajin wai matar sace Hafsatun" wara idonta tai

"Matarsa kaman yaya?" Dak'uwa ta mata da hannunta

"Kamar yanda nake mata a wurin ubanki, ki sani aurensu yafi watanni shida, watak'in yaune ya samu keb'ancewa da matarsa harya mata aika aika haka" tana tab'e baki na bak'in ciki tace

"An nunamun umma banida muhimmanci a gidan nan, ace anwa k'anina aure na biyu banida labari, to narigada na gayawa islam komai a waya wlhy....." Zaro ido waje Umma tayi😳😳😳 kantace wani abun wayanta ya soma ringing, a hankali ta d'aga ganin Fareeda ce ta kara a kunne

"Umma mun shiga uku, wlhy islam tazi har asibiti anwa Hafsat Allurar bacci ta shak'eta gatanan yanzu ba kanta, sanda tazoma bama nan nida Maheer yanzu bamusan abinyiba, ga jikinta cen ya rikice da k'yar aka k'waceta a hannunta" Allah umma tasoma kira kanta ce

"Ganin zuwa wurinku" ta mik'e ta sab'a hijab, Nasara ma ta biyota....

"Karki biyoni wlhy, karma ki sake zuwa inda nake!!!!

Mom Nu'aiym

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now