page 25

3.5K 339 15
                                    

[2/16, 11:35 PM] Billy Galadanchi🤪🤪: *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
[3/3, 5:54 PM] Billy Galadanchi🤪🤪: *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                                 25
A hankali ya gangara ya yae parking d'in motanshi, harga Allah baya cikin nutsuwar sa gameda Hafsat, yarasa dalilinsa najin haushin ta akan abinda ta masa abin ban mamaki kuma shine ya rasa meya sanyashi damuwa akan hakan? Ko gun Dr. D'in dayace zeje be biba, ranshine kurin yaji yana matuqar b'aci akan yanda be kula da Nancy ba yau...... Da k'yar ya iya saisaita kansa ya nufi guess house d'in daddyn sa cikin qunan rai,yayi matuqar mamakin jin cewar Mahaifiyar sa ta sanar masa dukkanin abinda Nasara ta aikatawa baiwar Allah yayi fushi me tsanani da har Maheer d'in dayazo d'aurin aure be gaya masa ba daya sani da tuni yarinyar tana waje ana kulawa da ita na mussaman....

"Yanzu sanar dani wane ci gaba aka samu ajikin yarinyar?" Kanshi aqasa yace anyi nasaran gyaran k'afar harma ta miqe kuma memory d'inta ya dawo normal idan ta  k'arajin sauk'i ma aka sallameta zan miyar da ita sokoto" Jinjina kanshi yae ya miyar da dubanshi kan jaridar Daily trust dake hannun shi kamar bazeyi magana ba se kuma yace

"Akace baku sanar da iyayenta daga nan gidan aka aikata wa 'yarsu hakan ba,ko miye dalili?"  

"Ea dama Abba rashin dacewar hakan kurin nagani, bazanso wannan maganar ta fita ba, tunda Allah ya kub'utar da yarinyar, kuma iyayenta ma ba wasu bane basu ma damu ba,ko mahaifinta tunda tazo nan garin basu zo dubata ba, kuma acikin watanni biyun datayi bekira waya so biyar ba yaji ya take ba, hasalima babu wanda yanemi ba'asin sanin inda aka ganta acikin su" kallonshi ya miyar akan Maheer yace

"Yace Mahee kai wanine kenan kake gani ko?" Da sauri ya kalli mahaifin nashi ya sani wannan kad'ai ya isa sanyashi ya dinga rigima,muryan shi na rawa yace

"Ba haka bane Abba rainane ya b'aci dasu mutane idan basu suka haifi yara ba sekaga ko mutuwa yaran zasuyi ko oho" Gyaran zaman shi yayi

"Su waye iyayen nata to?" Kallon Abban shi yayi

"A yanda naji dai wai mahaifinta ne ya rasu yabar dukiya me yawa, to ita kad'aice dashi shine se qanin mahaifinta ya auri maman nata ya kuma karb'i dukiyan azuwan ze riqewa yarinya shine fa zaman yaqi dad'i  harya saki maman ta ta koma k'asarsu Niger to yarinyar se wahala takesha, yanzu gashi karatun nata ma data gama cin wuyar shi ya lalace sanadiyan haka nazata sunje sun mata defring ashe basuje ba....school d'inda take zuwa wani zubin da k'afa tun daga low cost har D'an fodio" wara ido yae ya jinjina nisan wurin kan yace

"Sanda naje sokoto nace zanje naga jami'ar d'an fodio nayi mamakin nisan ta, batada banbanci da jeji ai akwai nisa sosai, harna qosa naga isarmu bazakacemun mutum ze iya zuwa gun da k'afa ba tun daga gwiwa lowcost sabida nasan Gwiwa lowcost ai na sanar maka inada gida acen cen nake sauka idan naje sokoto, da nisa sosai fa" 

"Allah abba ni shaidane takanje gida da qafa ko tazo da qafa ma, ai wasu mutanen basuda imani" kishingid'a yae kan kujerar dayake kai

"Kaima meya hana kaje kamata, ina kace d'alibar kace k'awar iyalanka kuma"

"Allah ko abba nazata iyayenta sunje" D'an guntun tsaki yaja

"Wanda be baka tranport kaje skul ba kaga alamun ze damune dan bakaje ba, kaida kace basa ma zuwa dubata kuma kace ko a waya basa kira, yaya zakayi wannan tunanin, yanzu abunyi mu had'e ta dasu sha'awa sedai iyayenta suna haqqin sanin me muke shirin yi, sabida haka ka shirya zamuje gobe sokoto" Be isa yayi musu ba dukda ba hakan yaso ba, had'e ta dasu sha'awa na nufin komawar ta london kenan gaba d'aya da zama da karatu toshi yaya ze rayu babu ita a rayuwarsa?....seda abban yace

"Ka tashi ka tafi mana",tukunna ya miqe,yana godiya yabar parlor d'in.

***************
     *Bayan kwana biyu*
Har akayi discharging na hafsat maheer be k'ara komawa asibitin ba, abun duk ya dameta Islam da kanta tayi mamakin hakan duk sanda tace asibiti driver ke kaita tayi tambayar harta gaji amma be kulata ba, yau da akayi sallamar Reedah tana wurin kasancewar me gidanta ya sanar mata za'ayi sallamar, da suka gayawa maheer ma se cewa yayi akaita gidan umman shi, sunsha mamakin bece gidan islam ba, amma haka suka d'unguma har islam d'in.

Hannu bibbiyu umma ta tarbesu aka kai hafsat b'angaren da aka ware mata kusa dana su Shauty da sophie har ta k'ara jin sauk'i su kuma sukayi k'awanya a parlor suna zuba zance Umma se washewa islam baki tabke tana sakota a hira ita kuwa kunyarta sosai takeji ta kasa sakin jikinta, su sophie se yatsina suke an kai musu ita kusa dasu sufa basuga dalilin nanuk'e musu datayi ba yarinya se san abun duniya sun tsaneta wlhy.....

Maheer se bayan isha ya shigo gidan, bayan sun gaisa dasu Reedah ya buk'aci sanin inda take aka gaya masa tana can sama...kai tsaye saman ya haura ya k'wank'wasa  d'akin a hankali, cen k'asan muryanta tace

"Bismillah, wanda seda ta fad'a so uku tukunna ya jiyota, ya turo k'ofar a hankali ya shiga, kallon sa tayi dan batayi tsammanin ganin saba ta sare akan ya tafi abunshi kenan

" Sannu da zuwa yaa maheer" shine abunda ta fad'a kanta a k'asa...Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace

"Yauwa ya jikin ki?"

"Da sauk'i Alhamdulillah" zama yayi akan gadon cen nesa da ita

"Ga sabuwar waya na siya miki dan taki ko labari, nayi k'ok'arin miki welcome back na layukanki duka biyu sedai d'ayan na Airtel dole sekinje da kanki wannan na mtn gashi nan banma gwadaba amma bari na gwada akan wayan yanzu" murmushi tayi

"Allah ya k'ara girma na gode sosai" Be kulata ba har messages suka fara dira akan wayar daga kunnawa kai idanshi yae akan wata number data turo message yafi so 20 se shigowa sukeyi ba adadi ya tsaya cak!! Akan lambar ya soma bud'awa

("Nayi kewar rashin ki nayi kukan nisan dakika mun nayi dana sanin rashin zame miki dan sandan ciki domin baiwa lapiyarki kariya, nayi sake dakika zamto acikin halin rashin tuna komai gaki kwance k'afa a karye Allah ya baki lapiya...Naki me k'aunarki Mahal")

Wannan shine saqo na farko dayayi tozali dashi a wayar

("Babu a duniya me iya sanya na nisanceki ki warke ki dawo gareni muyi auren mu na soyayya...Naki Mahal")

("Ina kukan rashin ki, ina keawarki abar sona, Allah ya tashi kafad'unki") haka messagea suka dinga shigowa sama da kasa na Mahal ya zauna harya manta da wanzuwarta agun seda ya gama karanta su tsaf!! NA K'ARSHEN  ne yafi tsorata shi

("Labarin samuwar lafiyar ki ya riske ni daga gun Mahal!! Naji ance kin warke ina nan zuwa gareki soon tawan, bazan rayuba idan baki abar sona, ina fatan kiga saqon nina") wato dama Mahal shiya miyar wani sha ka tafi? Lallai ma wannan yaron yazo da salon raini, mik'ewa yayi yana kallonta, ta tabbatar ba haka idanshi yake sanda ya shigo ba to meye damuwar?

"Bana son wannan sim card d'in bazakiyi amfani dashi ba, zan siyo wani da safe, ki rik'e wayar a gunki" kai tsaye yacire layin a wayan ya ajiye mata wayar, cikin rauni tace

"Amma yaa Maheer naga layin ya hau lapiya, kuma komai nawa na school da bank da komai dashi nake using" wata muguwar harara ya wurga mata, cikin d'aga murya yace

"To nace bazaki yi amfani dashi ba ko kinada ja ne!" Nan da nan idanta ya kawo ruwa

"Kayi hakuri ba haka nake nufi ba, abari da safe akawo sabon" seyaji kuma duk beji dad'in hakan ba daya mata amma bece komai ba ya fice daga d'akin...

************
     Bayan ya tafi kuma dukse ya kasa nutsuwar sa, ya gigice ya d'imauce ya rasa meke masa dad'i yafa kasa gane inda zuciyar sa ta dosa gameda Hafsat, abu k'alilan ya fusata sa akanta, abu kad'an indai ya shafeta yake susutar dashi wani zubin, yau kam be tab'ajin kwatan kwacin azabar radad'i da zafin zuciyaba kamar irin wanda yaji yau ganin saqon nin nan, yana mamakin wanann dama Mahal son ta yakeyi yake masa wayau? Lallai ma yaron nan....

   Islam ma bata ganewa komai ba yau din dasuka je, sabida yasha mur baya ko magana,beko kwana a d'aki d'aya da ita ba.

Mom Nu'aiym ce

Inshaa Allah na dawo kenan daily update💃💃💃💃💃

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now