page 29

3.4K 304 18
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                          29
Islam ta k'urawa babynta ido cikeda so da k'auna da kuma tausayi me tsanani!! Bata tab'a kawowa aranta duniya zata mata atishawar tsaki haka ba, bata tab'a kawowa ranta akwai ranar dazata haihu babu dangi a tare da ita, bata tab'a kawowa ranta zata haifi 'ya ba uba ba, ko a mafarki bata zata zata haihu ba asibiti ba, ta samu rauni amma bame kulawa da ita, Bata tab'a zata zata haihu ta rasa romon dataga ana yiwa masu jego ba, tasha ji Baba Azumi na fad'en idan ta haihu kunu zata dinga mata me kyau jikinta yayi k'wari da wuri, tasha ji Baba Azumi na fad'ar zata mata wankan iccen Dogon yaro na ruwa me shegen zafi, Baba Azumi taci burin sanyata a kujerar mata ta dinga turara mata kasanta ance yana maganin tusar gaban da mata keyi bayan sun haihu.....Bata tab'a zata, zata a haihu. Babu uba ko wani jigon dazewa abinda ta haifa Hud'uba da kiran salla ba, Bata tab'a koda a mafarki tunanin cewar zatafi haifi abinda ze rasa sunan da za'a kirasa dashi Ashe Ameenu ninketa yayi baibai ta hanyar sanyawa ainahin fuskar sa *WATA FUSKAR!!* ya danne wata salahar Fuskar da Mummunan *WATA FUSKAR!!* sa lallai tana cikin B'akin ciki, tasha ji yana fad'a cewan Duk sanda ya haifi Namiji ze bashi sunan mahaifinsa na ainahi wato Musa idan kuma Macece ze sanya mata sunan mahaifiyarsa wato *NANA KHADEEJAH* da wannan ta dauki jinjirar ta mata huduba da kanta tana sharar k'wallah lokaci d'aya kuma tana mata kiran sallah ta mata hudu ba da sunan Nana khadeeja....tausayi sosai ta baiwa Naja daya sanya ta kasa daurewa ta sanya kuka.

********************

      Abubuwa sun soma yiwa Baba Azumi yawa sosai, ta soma neman sukunin ta ta rasa, bashi ya mata dabaibayi wanda taketa ci da sunan ummul zatazo amma shiru kakeji tamkar an shuka dusa kwanakin cen gwal d'inta ta eba ta siyar babu yanda ta iya akan zata rage bashi yanzu gashi marasa mutuncin mutane sun taso ta agaba, har yanzu a k'asan ranta ummul take jira ta tabbatar ummul tanacen abunta k'asar waje tana hutawa, bata raba d'aya biyu cikin ummul ya kusa zuwa duniya da wannan take ganin dole su dawo gida.....yau dai kam rana ta b'acewa Baba Azumi sabida tanaji tana kuma gani aka zo aka wuce da ita station akan bashi belinta an gagara karbowa sabida yayan ummul yace shiba ruwanshi yayita gargadin su akan hakan wata er sandar mace har duka ta tik'a mata tsabat haushin datake bata sabida had'e kai masu binta bashin sukayi suka kai k'ararta, taci azaba kan abada belinta, se fad'i takeyi suyi hakuri 'yarta ummjl tazo wai me kudi take aure dansunje yawon shan iskane turai amma dasunzo zata bada, wasu kam kallon mahaukaciya tuquru suke mata.

*****
    Maheer ya dawo Niger ansha love shida islam se narkewa take wai ita adole me ciki, shi kuwa ko motsin kirki tayi seyaji a ranshi bayan zuwansa da one month suka juya zuwa London inda itama tunda jikinta yae kwari  aka soma nemar mata gurbin karatu a turai din inda ta samu nasarar shiga level one a bangaren turancin data faro....dayake su cen abinsu akwai tsari sanda kayi joining college sannan semester ka ze fara....
Tir k'ashi!!!

Yau  a parlor islam ce kwance tana narka shagwab'a tayi matashin kai da cinyar  Maheer dayake  biye mata ya sanya hannunsa yana wasa da sumar kanta dake a kwance, ita lallai yau chicken byte takeso, kuma anje siya sunce seda safe gashi 8 yayi, kiran Sophie yayi tazo tace gata

"Kin iya chicken byte ne?" Ya tambayeta kanshi tsaye kallon shi tayi ta dan saci kallon islam, a ranta tace wato matarnan tunda tazo muke cikin takura indai tana ganin yaa mahee durun uwa iri iri ko,

"Ea bazance ban iyaba amma muma Nancy ke mana, tafi kowa iyawa" jinjina kansa yae

"Jeki ki kiramun Hafsatun" juyawa tayi aranta tace so daya mukayi a gaban Nancyn Allah yasa ya kwab'e" tana zuwa ta turo ta, k'irjinta na  dokawa ta iso parlor d'in tunda sukazo da islam batada sukuni, tarasa mesa takejinta a takure sannan kuma batason ganinsu kullum.manne da juna tarasa dalilin jin hakan, ada tasan taso maheer amma yanzu ta sani koda a k'afa zasu d'aura mata shi bazata jasa ba sabida sam ita bazata iyaba, tanada wasu dalilai data barwa kanta sani..

"Yaa Maheer sannu da gida"

"Yauwa sannu Hafsat, am chicken bytes zakiwa baby, shi takejin ci kuma near by shops dinnan babu wai seda safe suke ta cewa" wani k'ututun bak'in ciki ne ya tasowa Hafsat amma seta kanne tace

"E babu damuwa, munada kayan hadin barinje na hada mata" Bece komai ba ta juya tana had'awa tana mita harta kammala ta kawo, agabansu ta ajiye tana kallon islam da wasa irin na ftnds dinnan tace

"Maman biyu ga wannan karki cinyemu" murmushi islam tayi sannan cikin isa tace da ita

"Kekuwa ina d'an drink dazan had'a da? " miyarda dubanta tayi zuwaga maheer ta shagwab'e fuska

"Ni honey kace da ita ta had'amun ko smoothie ne dabashi da wuya nafison Banana smoothie yafi rik'e ciki"  kallon mamaki hafsat ta mata shi kuwa Maheer yace

"Kinji me tace kije ki had'o kin wani tsayawa mutane akai" zuwa wannan lokacin seda tayi kuka a kitchen tana mamakin sauyawa halin qawarta.....

**********
    A wannan daren Nancy ta kwana tana bak'in cikin faruwar wannan abin,tasani Maheer baya mata wulakanci shida sophie amma shauty da islam suna yawan kaita mak'ura aciki islam tafi bata mamaki, ita bazata fito ta mata wulakanci ba amma sedai tana mata abubuwan datake so taga sun k'ureta tayi wani abin daze ja mata raini!!! Mamakin wannan halin na islam na cikin damuwar ta......Bazatace Komai ba akan wannan abin tayi alkawari zata jure amma tasan wuyace zata shata ta hango wulakanci tsantsa acikin take taken da islam keyi tun zuwanta, ta dinga mata abubuwa tamkar wata 'yar aiki tana tunzurata zuwa bango, amma ba komai zata jure!!!

**********
    Duk wani juyin da maheer zeyi tunanin Nancy ne danqal acikin kansa, yana cikin tsantsar damuwa mara adadi, yana kula sosai da yanayin islam da yanayin d'abi'un datake nunawa agaban na Nancy, bayaso ya mata magana ne tazo tana mar wani kallo na daban,yasan mata seya sanya wani abu aranta daze k'ara dagula zaman, yana hango yanayin Nancy da kuma b'acin ran datake shiga duk sanda ta mata irin wannan abun, ya kula ma tun dawowar da yae da islam Nancy walwalarta ta ragu sosai, ya kula kuma takan zauna skul ko bata komai har yamma sabida batason ganin abubuwan da islam keyi sam ya kula tana cikkn damuwa abun yana damunsa!!!

Mom Nua'iym ce

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now