page 43

3.6K 326 36
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

      43

Ranar maheer bashi yabar gidan Islam ba se washe gari, se zuba love akeyi ta bashi hak'uri kuma yaji dad'in hakan, yana son mutum yayi kuskure ya kuma bada hak'uri, yanda aka nanuk'ewa juna tamkar ba jego akeyi ba, shinshina da shafe shafe yashashi a wurin islam seda ta tabbatar ta gamsar dashi da wasanni tukunna ta tsiri kukan ya kwana mata, Bayason rigimar islam sukai sharad'i akan daga ranar baze k'ara kwana mata ba se Inna ta wuce, haka tace ta yarda sabida ta shrya shagaltar dashi kullum idan yazo.....wannan ma yana daga cikin shirin Anty Nasara na ganin bayan auren islam wanda ita a zatonta sone.......

*********
  Tun wuraren k'arfe tara na dare Hafsat tawa su Sophie sallama ta wuce d'akin yaa Maheer, dayike sunada Exams setaje da takardunta tana dubawa, tun tana saka ran ze dawo har bacci ya d'auketa be dawo ba, ba ita ta farka ba se  asuba, tasha mamakin inda yaje ya kwana be gaya mata ba, gata acikin damuwar abinda ya samu ummul har Baba iro sunyi waya akan Jikin Baba azumi ba kanta, gashi kuma yazo ya tafi ya barta ba sallama ba waya har yanzu baya kiranta a waya, tarasa dalilinsa nayin hakan......tamkar wacce k'wai ya fashewa a ciki haka tamik'e zuwa d'akinsu acen tayi wanka ta shirya ta wuce school tanada exams by 10:am......tana cikin school bus wayanta yai k'ara

"Yaa Maheer" shine sunan data gani rad'au ya aiko mata message, a hankali ta bud'e message d'in

"Good morning princess, hope kin tashi lapiya, jiyan na kwana wurin su islam ne, dafatan bakida matsalan komai?" Wani abu dabatasan ko meye shiba ya taso mata ya tokare mata k'ahon zuci, wani d'aci taji a yawun bakinta kanta ya sara mata, kashe wayanta gaba d'aya tayi aka huta, ta jingina da sit na kujerar datake kai, a hargitse tayi Exams din ta fito, amaimakon taje gidama library taje tanata karatu har yamma kuma bata bud'e wayanta ba, se bayan isha ta koma gida da azababben ciwon kan data rasa dalilin sa a rayuwa......sophie ta had'u da ita a parlor tana shan ruwa a cup

"Ke Hafsat yau ina kika shiga anata nemanki, ko wayanki baya tafiya" a wahalce ta d'ago ta kalleta

"Ina library karatu nayi ko gobe inada exams morning" jinjina kai tayi

"To ai dakin gaya, yaa Maheer se masifa yake mana akan ina kikaje har yamma mukace school mudai mukasan kin tafi" guntun tsaki taja a hankali kan tace

"Shima dai yasan ba b'ata zanyi ba a garin nan" ta wuce d'aki abunta, dama sunyi gulmansu da shauty akan be kyautaba jiya ya kwana cen gidan sun gano fushi tayi......

    Yauma haka islam ta mantar da Maheer komai arayuwa, kissa da kisisna da iyayi, daga k'arshe ta bashi maganin bacci, bashi ya farka ba se washe gari karfe goma na safe, yasha mamakin wannan baccin, da girman sa baya iya tuna sanda ya rasa sallah asuba da sunan wai bacci ya sure shi, Amma kuskuren datayi sega tablet a gabanshi bata daukeba ta manta, ya shak'a sosai da ita har meeting yakeda ta hanashi ya halarta yanzu.....da fad'a suka rabu yau kam.

*************
     Yauma Nancy dukda daren suna ne amma bata koma gidan ba se bayan isha, bayan an sanar mata yaa maheer yace taje gidan islam su dafa abinci ze gayyato mak'insa by 12:noon sabida suma suga yanda suke nasu shagalin biki, yaji haushi dabata jeba duk bayan mintuna seya yiwa Sophie waya tace batazoba har dare, dama ta k'are da school seta wuce abinta gida, interval nata da exams kusan 2 weeks ne amma haka ta mak'ale a library da waya a rufe..........se wuraren sha d'ayan dare suka dawo dukkansu lokacin tana parlor zaune maid d'insu ta kawo mata snacks da drink tana sha....se yamutsa fuska takeyi kamar an mata dole, yau a cike take fam da Maheer tamkar zata fashe haka takeji, kai tsaye wurinta yanufo, tana sanye da gajeren boxer irin na maza, da guntuwar farar vest ta baje sumar kanta har tana sakkowa tana rufe mata fuska lokaci zuwa lokaci takan kai yatsunta ta sak'aje wacce ta zubo a bayan kunnenta, Tsaye yayi a kanta ya murtuk'e fuskar nan itama kuwa ko kallonshi batayi ba ta had'e wannan fuskar tata abinda kake fin shekara baka ganiba a fuskar ta fushi ba.......ko Gayar dashi batayi ba shima bece mata komai ba, sophie sarakan iyayi ne tazo wurinta

"Ke Hafsat kwana biyun nan lafiyan ki kuwa, ki kama waya kin gark'ame ba inda banje nemanki ba a school dana kammala exams, kuma kinsan dai koma menene baki kyauta ba ko yaa Maheer zeyi bak'i gobe suna kink'i kizo mu masa girkin dayace alhali ya sanar mana dukkanmu" D'agowa tai ta kalli sophie, ita kanta ta tsorata da yanayin Hafsat idan nan tamkar ba nata ba, hadda bak'in ciki ya soma komawa brown akan jan dayayi, alamu ma sun nuna kuka tayi da sauri sophie ta sunkuya

"Dama bakida lapiya bamu sani ba? Mesa baki fad'a ba" ga jikinta da zafi sabida wahalan data baiwa kanta ga rashin cin abinci amma haka ta daddage

"Ni lafiyana k'alau yawan duba takadda ne kurun ya sanya idona yai haka" kallon tuhuma sophie ta bita dashi

"To amma duk duba takaddan ne ya sanya jikinki ya soma zafi, gudun magani ko? Umma zan kirawo a waya yanzu kuwa"  rik'e hanunta tayi tana yunk'urin mik'ewa

"Karmuyi haka dake, wlhy lafiyana k'alau yanzu se umma tamun fushi kinsan halinta, kaina ke ciwo kuma ki tambayi catrina nasha magani ciwon kai" jinjina kanta tayi alamar gamsuwa

"Yakamata kije ki kwanta ki huta, yafi wannan zaman anan kinji swt hrt"  gyad'a mata kanta tayi da murmushin yak'e a fuskarta wanda akace yafi kuka ciwo a tare suka bar wurin, shi kuwa yana nan tsaye tamkar wani statue, kai tsaye d'akinsu na usul ta wuce tai kwanciyarta, kallon ta sha'awa tayi

"Ke Hafsat ina  yaa Maheer yana gidan me zakizo nan ki kwanta kuma, kefa Hafsat wlhy zan gayaki da anty Fareeda, ji yanda ya damu dake d'azu yakira yakai so goma komafi wlhy akan kinzo gida amma shine yanzu zaki k'yaleshi" Lumshi idan ta tae kanta yana ci gaba da sara mata, amma kanzil bata ceba, Catrine ce tashigo akan wai yaa Maheer yace Hafsat taje d'akinsa yanzu, bata kulataba kuma tafi 25 mns bata tashiba, harya cire rai da zuwanta ta mik'e tana ganin jiri taje d'akin nasa....... Mik'ewa tsaye yai cikeda masifa

"Hafsat ni kika raina ko? Ni zaki rainawa wayau? Tun yaushe na aika akiramun ke? Tukunna ma ubanme ya hanaki zuwa kiyi aikin dana sakaku?" Wannan fad'an dayake hadda zugar islam akan wai tana bak'in cikine an fasa sanya sunanta yasanya tak'i zuwa har tana cewa wai tunda takira ta zageta karta shigo mata gida kuji sharri!!!! Da k'yar ta iya d'aga idanta ta kalleshi

"Kayi Hakuri" shine abinda ta furta kanta zauna ragwaf akan gadon kasa zaman tayi taje luu ta kwanta kanta yana meci gaba da tsananin sarawa tamkar ze tsage gida biyu, ita da kanta tasan hadda yunwa bawai ciwo ba amma yanda takeji bazata iya cin komai ba.....binta yai da kallo yana nazarinta, jikinsa ne yai sanyi yabita zuwa gadon ya tallafo kanta sosai ya tsorata da zafin dayaji ajikinta, yakula dazaran ranta yana a b'ace se zazzab'in nan ya tashi mata seya kaita asibiti tukunna zeji  meke sanya ta yin hakan, kar azo memory ya k'ara guduwa ya shiga uku

"Hafsat bakida lafiya sosai ne haka wai?" Cikin rashin sanin me tace da k'unan rai tace

"Da inada miji aida yasan banida lafiya, dayike ni gauruwa ce aidole inyi hak'uri na zama wacce ta rako mata duniya, ko albarkan kiran waya bana samu, kaje kaji da kanka gun Mowar gidan mana tunda yake albarka sanin zaka kwana a guntama ban samu ba sedai na nemeka na raba dare ina jiranka baka zoba, kai kuma wuni d'aya kacal daka nemeni dannaje nawa mowar gidan baka samu ba har ka rufe idanka kanacin mutun cina, babu ruwanka dani ko yanzu kana iya tashi ka koma gunta ai"  Ya k'ara tabbatar wa kanshi fushin dai na kishine kuma yasan be kyauta ba

"Kiyi hak'uri Hafsat wlhy bada sona bane"

"Ni dason nawa ai ya Maheer, wannan ce soyayyar dakake cewa zaka nunamun kanamun tunkan ayi sati harka soma nuna mun rako mata duniya kurin nayi, mesa acikin kwanaki uku kacal zaka dasamun so da k'aunarka azuci sannan ka soma azabtar dani, wlhy seka ciremu " wowta take zazzaga masa meze cire ya tambayi kansa? Ba amsa

"Kiyi hakuri abun dukba haka bane ba, kuka ta saka masa, lokaci s'aya kanta ya k'ara hargitse mata da ciwo me tsanani, dafe goshi tayi tana sauke numfarfashi a hankali, daga haka kuma seyaji shiru bugun zuciyarta ya tsaya cak!!!! Kamar yanda numfashin ta ya d'auke cak!!! Lalubar hannunta yayi ya cira shi ya sako yaga yazo lagwaf....

" suma tayi" ya furta a sarari....tunawa yayi da maganar likitan ta tun a Nigeria....
"Idan kukayi sa'a zata warke na har abada, amma sekun kula idan damuwa ta mata yawa zata rik'a suma kuma ba'ason irin wannan suman sabida wani zubin dagashi basa tashi se k'abari" wata mahaukaciyar k'ara ya sake had'eda kiran sunanta, su sophie  duk hankalinsu yadawo kanshi suka fito a guje har catrine ma suka nufi d'akin....

  Mom Nu'aiym

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now