page 11

3.9K 369 27
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                          11
Kallon Mahal take cikeda mamakin sauyawar halayensa, yanda yake roqarta akan ta daure ta auresa, cikin sanyin murya tace

"Kayi hakuri Mahal wlhy bawai sanka ne bana yiba ko kuma na rainaka, ko d'aya wlhy ka sani bazan iyaba, na sani auren huce haushi kake shirin yi dani bawai soba, hakan kuma na sani cewar bakada labarin azabar da zansha a hannun su Ummul idan sukaji wannan maganar, ina roqon alfarma agareka daka janye wannan qudurin naka" nisawa yae yace

"Amma menene zesa ki damu da abinda  zasu mikin keda bawai dad'ewa zakiyi a gidan ba, auren danakeso nanda sati biyu ayi, dan Allah ki dubi maraici na" Nisawa tae

"Banida wani gata a duniyar nan sesu mahal, bazan lamunci watsar da dangina akan ka ba, ka sani ni marainiya ce sabida su Baba iro sune iya yena, mahaifina ya rasu bayan nini kadai suka haifa a duniya!! Ya rasu ya barni inada qananun shekaru mahaifiyata er jamhoriyar Niger ce haka bayan rasuwar mahaifina ta auri mahaifin su ummul babu kalar qiyayyar daban ganiba nida ita qarshe ya saketa kuma taso tafiya dani ya hanata, a yanzu haka tana aurenta acen Niger da yaranta uku, ina shiga a Nigeria idan nae rashin su Baba iro? Bayan sune gatana gaskia ka sani wlhy bazan iyaba dan Allah kai hakuri" murmushi ya sakar mata yace

"Bazan takuraki ba Nancy amma dai zan baki lokaci  zuwa wani satin kiyi nazari akai" shiru ne ya rataa wurin kanta nisa tace

"Banaso ka wahalar da kanka wurin neman aurena Mahal, sabida ni bazan tab'a iya aurenka ba har abada" Tana gama fadar hakan tae ciki abinta shi kuwa ya dafe kansa dukda haka bata tsiraba seda sukaci mutuncin ta sosai!

************

    Sosai Maheer ya tattare nutsuwar sa yana kallon islam!! Duk ta masa fari tamkar batada jini, tayi baqi da komai.....gyaran zamanta tae kantace

"Da farko dai ni sunana Salahatul islam Idris me walda, mahaifina da mahaifiyata haifaffun en sokoto ne acikin qaramar hukumar silame dake cikin jihar ta sokoto, wannan kyawun halittata ta bahaushe ce kawai dani sabida iyayena duka hausawa ne, haka na ganni ina kamada mahaifiyata sosai komai nawa natane, mun taso a unguwarmu dake tudun wada mahaifina walda yakeyi itace ta kawoshi zaman sokoto ma, wannan dalilin ne ya sanya ake ce masa idi me walda, ya taso da matuqar son yaga yaranshi suna karatu sedai bashida qarfi ina da yayyu guda hudu duka maza,  biyu uwarmu d'aya ubanmu d'aya biyu kuma yaran kishiyar Mahaifiyatane amma ubanmu d'aya, dukkansu suna fara karatu har matakin jami'a amma da qyar biyu suka qarasa kuma suna nan har yanzu cikin gidan ba aikin ayi tun daga bautar qasa, biyun kuma sune muke uwa d'aya uba d'aya wanda khamis yanzu yake aji hudu shi kuwa Asheer yana gun bautar qasa dalilin dayisa se yanzu suka kai nan shine sabida kosun fara rashin transport kawai seya tsayar dasu, so biyu khamis yana fara zuwa coe rashin transport yana daqushe karatun harya watsar wannan ma dasuka kammala da taimakona ne!!! Nice na taso me nutsuwa acikinsu amma se Allah ya mayar dani haka tunda na soma karatun gaba da secondry school....so da dama nikan tashi agidan mu babu abinda zamuci wani zubin haka zamu wuni ina kallon yaran kishiyar Babarmu suna cin abinci amma bazasu bamu ba... Haka  sabida ita en uwanta sunada rufin asiri mukuma bamuda kowa se Allah, bayan dana samu admission a jami'ar usman d'an fodii na soma zuwa school sena soma had'uwa da ibtila'in rayuwa... Wani zubin inaji ina gani lecture zata wuceni sabida rashin transport.. Idan zanje makaranta na dinga kame kame kenan na rashin suturar zuwa makaranta wannan abin yana damuna bame qawance dani sabida hatta turaren sakawa banida shi wani lokacin ma sekaga vaselin dazan shafa ya gagaremu senaje a hakan ta fata duk furfuri!! Haka idan nawa mahaifina zancen siyen handout baya kulawa seyace babu har wani zubin nakanji tamkar indena zuwa makarantar!!  Haka dai naketa daurewa har muka qarashe zangon karatunmu na farko,nida Nanuwa ajinmu d'aya  kuma mumu kad'aine yaran bayin Allah, abinda na kula dashi shine  Ita nanuwa bata sakin fuskarta nima muna qawancene kawai amma befi naga face dibta so biyar ba, wani zubin tare da ita muke soleta har gida qasa, idan mun fita bama rabuwa se munkai dandima se kowa ya dauki hanyar gidansu da qafa, ganin inashan wahala ya sanya mahaiyta tace in dawo hostel da zama na daure haka nan na dawo tare da neman Nancy akan ta dawo amma se Baban ta yaqi  yarda, sedai takanzo duk sanda takeda  test ta kwana karatu......zamana a hostel ya sanya na had'u da qawaye iri iri kala kala, dana gari dakuma b'ata gari ganin banida gata ya sanya wata qawata danai a hostel  me suna jameela ta dinga nunamun hanyar yin zina amatsayin sana'a amma fir senaqi yarda haka ya sanya ta soma rarrashina harna soma kaucewa hanya, wani zubin takanzo da maza muje hira a mota kuma takan bani kyautar sututu da kud'ad'e jamcy na yawan nunamun cewar ina cikin musiba  na talauci gashi handout ma ya soma gagarana siya, Namcy ta soma ankaewa da yanayin dana soma shiga na wani sauyi ta matsamun na bata labari ta hau wa'azi da ban baki, harta mun magiya, a haka dai ta saisai toni tayi sa'an rabani da jamcy!!!

Bayan nan kuma se Allah ya had'ani da wani saurayi me suna suraj haka na daddage  ina qaunar suraj, suraj ya yaudareni har gidan mu yaje ya gayar da iyayena ya kuma tura neman aurena, komai suraj yana mun   nafita a qangin talauci har ina samu in taimaki iyayena da qawata Nancy dake shan wahala matuqa agun Qanin mahaifinta dake riqon ta da matar sa, Suraj ya sabarmun da kud'i seya kashemun dubu hamsin a rana qarshen wata yana bani dubu dari yace nai laluran school suraj dan kasuwane kuma d'an siyasa ne riqaqqe!! Katsam rana d'aya suraj ya bijiro mun daneman hadin kaina akan mui zina, na nuna masa muda zamuyi aure menene abin rushing yayi yayi nace harammun bazan ba musamman shida yakeda matansa biyu yaje ya rage zafin sa anan, daganan ya nunamun gini yakeyi kuma yanada kwadayina, dayaga bazan yiba seya dawo rarrashin akan nai hakuri koda wasanni yana tattab'ani munayi tunda ba komai bane, haka na saki jikina dashi ganin kamar a hostel mafi akasarin mata suna yi, inajin suna hira mukanyi wasanni ta hanyar tabawa juna sassan jikinmu...wannan shine babban kuskuren dana tafka!!!! Na saba sosai da wasannin da suraj kemun ganin na fara sabawa ya sanya suran ya qara tadamun maganar zina, nace bazanyiba bece komai ba ya tafi tun daga ranar suraj seda yae watanni uku baya waiwayata ko wayana baya d'auka na shiga damuwa sosai, abubuwa ukune suke neman zautar dani na farko dai Ina matuqar son suraj a rashinsa har rama nai da kuma ciwo, na biyu kuma shine tsantsar talaucin dayamun dirar mikiya nasoma sabawa da kudi a wannan lokacin ina aji biyu kuma tun a zango na biyu na hadu da sura farkonsa kusan shekara munyi rayuwa me ma'ana sosai na shaqu dashi....haka kuma abu na uku shine tsantsar sha'awa na saba da wannan wasannin banzar, sena kasa sukuni inji ina son kasancewa da suraj harna soma jin koma waye zan iya wasannin dashi, adu'a naketayi haja dai har Allah ya karkato da suraj awurina, koda yadawo ko wasanin baya mun yace dani  harammune nai hakuri koda wancem yaji wa'azi  ya tuba, haka muka qara watanni biyu bama komai daya danganci wannan ko riqen ahnnu bayayi kuma duk abinda yakemun ya linka!! Ranar mukaje shopping akan kayana ya qare yace muje na rakashi yaudai na gayar da mamansa haka mukaje gidan  ba komai a raina......"😭😭😭😭😭 shiru tayi tana sharar qwallah kantace cikin raunin murya

"Maheer bayan mun shiga gidan har parlor muka zauna wata yarinya dagani er aikin gidance ta wadatani da abubuwan sha shi kuwa ya shiga ciki, nasha lemo da cake da aka ajiyemun dama na kwaso qishiruwa kuma naga alamar ba kowa tunkan suzo naji kunya....haka ta kasance Maheer daganan se farkawa nai na ganni cikin jini da wahala ko yatsana bana iya d'agawa, alamu duk suka nunamun fyad'e suraj yamun tun daga yanayin zogin danaji jiki na yanayi aciki, ina nan kwance ina tunanin meya faru se ganin suraj nai ya shigo dagashi  se boxers   yana murmushi ina hawaye nace

" suraj mekamun mesa zaka cutar dani?" Dariya yae yace

"Soyayyace ta sanya haka Islam kiyi hakuri" kukana ya qaru jinya tabbatarmun na qarasa rufe jikina da bargon dake wurin nace

"Wlhy senayi qararka a kotu azzalumi kawai" kallon cikin idona yae yana wani shu'umin murmushi yace

"Waye ubanki islam? Me waldar? Me zaku iyayi dani? Aganin bansan darajar kudi na dakuke taci bane islam? Inada hankalina wlhy nasan me nakeyi ki sani  ba'a cin kud'ina haka kawai kuma kije kotun qoli shari'a zan iya kune zaku wahala tunda kune talakawa, ina zamana kika zo har gidana kuma waye shedarki? Banza jaka" kukana na tsananta haka na barwa Allah ban gayawa kowaba se kawai na hakura, tsawon watanni biyu suraj ya dena kulani kuma tun daga lokacin   da abin ya faru har akai watannin biyu na nemi al'adata na rasa!!! Shiru tai na some seconds tana sharar qwallah kan taci gaba... Koda na ankara na gayawa jamcy setace muje asibiti gwajin farko aka tabbatar inada ciki, da taimakon Allah fad'uwar gaban jin inada ciki shine yayi sanadiyar soma bleading dina har cikin ya b'are nasha wahala seda akamun wankin mara  banji ba ban gani ba!!! Daga wannan lokacin kuma se jamcy ta fara tsora tani akan nazo mui karuwanci kota nunawa kowa takartar miscarriage din dan shegen dana samu ya fadi har akamun wankin mara, sabida bazata rufamun asiri haka kawai ba ita idan ta kaini gun manya zata samu kudi, nayi nayi jamcy ta rufan asiri taqi haka na yarda akan zanje so biyu tace itama ta yrda, mutumin farko dana fra had'uwa dashi shine ya bani kyautar miliyan daya, ya baiwa jamcy dubu dari uku, na biyu kamma daya tashi seya 1.5m wannan ya qara bud'e idona tunda nasan dad'in kud'i shi kenan sena manta batun yi so biyu haka na manta haramcin aikata abin,Nancy har kuka takemun akan ma tuba na dena amma Allah be sanya nayi nadama se zuwanka, babu memun fada agidanmu mahaifina be taba bincikar inda na samo kudi ba" .....jin tayi shiru na mintuna biyu ya bashi damar miqewa tsaye ya miyar da hannayensa guda biyu baya yana zagayen parlor d'in yarasa mezece laifin waye to? Iyayen ta ko suraj ko kuma ita kanta?

Mom Nu'aiym.

Zan shiga hidima kwana biyu wataqil kujini shiru sedai yanda ta yiyu.

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now