page 32

3.7K 316 11
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                         32
Gumice ke tsatsafowa su ummul tako ina, yasan halin Alhj Baba yasan meze iya akan wannan jinjirar yasani zega laifin sane amma bari ya gwada d'aukar wayar tasa,jikinsa ba k'wari ya d'auki wayar ya danna lambar ya kara a kunne

"BAKA KUSA DA WAYAR NE?"  aka buk'aci sani daga d'ayan bangaren....

"Ea Baba bana kusa nashiga bayi gudawa nake tunda nazo gidan, akwai matsala fa Baba"  Gyaran zaman hular kansa yayi

"Mecece damuwar?" Ya tambaya cikin isa

"Baba wai bakwaini ta haifa ashe tun bayan watanni biyu, kaga kuma ni banzoba gashi yarinya har tayi k'wari a hannunta" Tsaki yaja kan yace

"Wannan wane irin mugun sakarcine? Bakwaini kuma? kana da labarin cewan na karbi fiyeda rabin kudin wannan jinjiran kuma ka sani ni bana asara sedai idan kai zakayi, kuma a kawomun Uwar zan had'ata da shap shooter ya mata wani cikin shap shap ta haihu a ta maye mana gurbin asarar mu sannan kuma ita jinjirar yaya zakayi da ita? Karka zomun da ita nan kaji na gaya maka wlhy" Muryanshi na rawa yace ze kawotan, kallon Ummul yayi Baze tab'a iya bari wani namiji ya rab'i matar saba, wato shikenan Alhj Baba sabida ya renesa seya hanashi walwala yana nufin iyalansa ma baze bari suyi k'wai ba? Mik'ewa yayi yace

"Tashi muje Ummul tashi mubar gidan nan akwai matsala, bazan k'ara cutar miki da rayuwarki ba, bazan yarda wani ya rab'eki da sunan zinaba wai dan ze miki wani cikin, gwandamun in mutu da inganki a wannan halin Alhj  Baba bashida imani ko kad'an" koda Bata fahimci kala mansa ba amma ta gano da matsala Naja ma agaba suka sanyata sunsha mamakin gate a wangale suka fad'a motar kuma acikin qalilan lokaci dabefi 50 mns ba suka hau titi da kyau, suna shiga gari Mamaki ya kama ummul ganin ko wane sighn boad zata gani setaga an rubuta masa jos nigeria wato jos ma suke kenan? Lallai ma Ameen namiji munafuki, kai tsaye kano suma nufa acen ya nemi gidan ajiyesu wanda Alhj Baba bemasan yana dashi a kano ba....

Bashida wani wanda ze gayawa damuwarsa amma mutumin farko daya fad'o masa shine Maheer....sun kwana biyu basuyi wayaba kasancewar ya dena amfani da layin da Maheer ya sanshi dashi, lalubar layin yayi ya saka shi ya dannawa Number d'in Maheer kira, yana ganin tak'i shiga ya gano yana london wata iriyar zufa ce ta keto masa, lalubar lambar maheer ta london yayi yae sa'a kuwa ya samu, a wannan lokacin Maheer yana cikin tsananin damuwa akan Nancy, koda yaga Ameen ne yayi mamaki, yafi watanni yana kiram wayansa baya tafiya sam!! Da sallamar  sa ya d'aga kiran suka gaisa yace dashi

"Kwana biyu Ameenu bana samun wayarka yaya wurin su ummul hope dai lapiya?" Susa kanshi yayi cikeda jin nauyi kan yace

"Abubuwa da dama sun faru abokina, dogon labari ne dabazan iya bakashi ba yanzu, naso ace kana gari ne mu hadu gani gaka amma yanzu yaushe zaka dawo?"

"Eeeh to akwai abinda zanzo yi Nigeria nanda 3 weeks idan beyi nisa ba, semu hadu daga na dawo idan Allah yasa muna cikin masu numfashi a lokacin" Nisawa yayi

"Babu damuwa Maheer amma dai ka sani ina tsananin buk'atarka a yanxu hakan, idan da hali karka wuce sati ukun da kace, bayan wannan idan akwai gidan dakakeda shi a nan kano ina son aron key zanje da ummul gidan akwai damuwa fa" Shiru kan yace

"Akwai gidaje ma abokina, zanwa kamala waya seka nemeshi ko, naga kaman hakan yafi kaima zan bashi wayarka"

"E hakan ma yayi amma dai a bani motoci guda biyu suma, zan bashi tawa ya ajiyeta a gidan ku kan ka dawo" Maheer be wani tsaurara tambayoyi ba, ya kawai masa fatan Alkhairi....har zasuyi sallama yace

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now