page 41

3.6K 333 14
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

      41

Maheer dake baccin sa sama sama yake jiyo sheshekar kukan Hafsat, ita arayuwa ta tsani fitina, dame yinshi ranar dukda islam ta gano Maheer mijintane kenan seta hallakata kasheta ma zasuyi ita da uwarta, Har lokacin idanshi jajir yake kamar gaushin wuta, dak'yar ya samu sassauci ya saukesu akanta

"Hafsat Lapia dai?"  Dagowa tai sukayi ido biyu,ta k'ara shagwab'e fuska

"Toba islam baceba taketa xagina,Har Umnana take cewa karuwa,waini karuwa ce waye waye,Allah kuwan nina gaji da wannan abin,ka miyar dani gida nayi makarantan acen" Dafe kanshi ya k'arayi dake barazanar tsage masa ya tsani fitina, wannan Islam tazame masa rigima arayuwa, ko yanzu yasha fad'an daya mugun b'ata masa rai gun Abba akan islam, wai mahaifinta tasa yakira Abba akan wai tanaso ta sanya suna amma an hanata sakawa, shine Abba ke fad'a akan ba'a sanar masa ta zab'i wani suna ba dabaze hana a saka mata ba, ya bada umarni tare da bada damar a saka sunan  da uwar keso.....yasha fad'a akan soma nuna rashin adalci har yana ik'irarin raba auren sa da Hafsat tunda ita dama baso takeyi ba, danshi yayi idan baze adana zamtowa hafsat matarsa for d tme bng ze raba auren....tunda yaji qazafin da suka masa yaji gaba d'aya daga islam din har iyayensa sun sire masa, yasani be bata zab'in sunaba amma bata ce dashi ga wanda takeso ba, yana mamakin ma yanda ta lalubo sunan mahaifiyar Abba danshi maganat br tab'a had'ashi da ita ba, baya ma raba d'aya biyu inshaa Allahu Anty Nasara ce.....gyaran kwanciyarsa yayi zuwa zama ma ya janyota jikinsa..

"Hafsy na kiyi hak'uri kinji, komai yayi farko zeyi k'arshe, kuma wannan muguwar kalmar datake jifanki dashi zan mata magana karta k'ara sam bazan lamunci wannan furucin akan princess naba" Lafewa tagi ajikinsa

"Ni Yaa maheer Allah seka miyar dani Nigeria, Islam ta sakoni agaba, auren ma nawa akanta yazama kaman dodo, se b'oyewa akeyi,kuma ace ta hanani sukuni ni idan aka barni anan Allah bazanyi karatu ba" Shagwab'ar nan ta Hafsat tana burgeshi, sumar kanta ya soma shafa mata

"Kinga Princess hakuri zakiyi, ke kinga alamun zan iya rayuwana bake aciki? Tayaya zan bari kimun nisa ne wai? Idan kika koma Niger duk wasu harkoki nawa kin dakatar dasu, ki kwantar da hankalinki  bazan bari ta k'ara miki irin wannan ba zan mata fad'a kinji" K'ara matsawa tayi jikinsa sosai yana kakkamashi

"Idan ta k'ara zagina nina ramawa zanyi, dan kawai taga ka mata ciki ta haihu se wulak'anci nima ai zan haihune" murmushi yayi

"Ko mesa yanzu hafsat ke wawta oho?" Abinda ya fad'a kenan aranshi kanya nisa yace

"Ea fa hakane, kema zaki samu babyn ki, kuma akan sunan danace na baiwa yarinya hafsat kiyi hakuri wani uzuri ya taso da dolene seya kasance an sauya, amma na miki alqawarin indai inada rabon tara 'ya'ya anan gaba, inshaa Allahu zan miki Takwara" Murmushi tayi

"Babu komai, dama mamanta ta gayamun bazata bari asaka ba, kuma banji komai ba kaima tafika Gaskia, sunan kiahiyartane fa, ayi haka" Dariya yayi

"Halinki nakeson babyn ta d'akko shisa, amma ko yanzu ina mata fatan ta dawo kamar ke" Murmushi ta k'arayi

"Yaa Maheer dan Allah idan bazaka damuba na tambayeka mana?"

"Ba komai Bismillah ina jinki"

"Meyake damunka? Kasan idanka ya sauya launi zuwa ja, yanayin ka gaba d'aya ya nuna kana cikin damuwa kana kuma jikinki yayi zafi alamun kanada zazzab'i, iskar nimfashin kama ta sauya zuwa d'imi, menene damuwar? Bayan zazzab'in nan na tabbata akwai abinda ke damun ka na b'acin rai" Nisawa yayi

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now