page 9

3.4K 318 28
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                         09
Shirinsa yae tsaf cikin shiga ta alfarma tamkar babu abinda ke damunsa kansa ya qurawa ido a mudubi yana kallon yanayin ramar dayae, ya rasa dalilin dayisa ya kasa jurewa idansa ganin islam!! Mesa zeje gunta? Mezata gaya masa? Me zeje shima yace mata? Ina dalilin wannan soyayyar dayike mata? Yana jin zafinta tamkar ya kashe ta amma soyayyar dayike mata ta wuce tunaninsa besan yana santa ba seda yae wa ennan kwanakin  beji muryarta ba!!! Sanye yake da wani irin lallausan farin yadi me asalin kyau rigar guntuwace iya cinyarsa da wandon ta dinki big man amma me kame jiki hannun rigar dogone ya daure da clips yasha hula a kanshi qirar mu had'u a banki   kalarta baqa wuluq, agogon hannunsa baqine takalmin kansa baqine kallon saman mirror d'in yae d'auki black shade d'insa ya manna a idon sa ya juya bayan ya zari key na benz d'insa baqa......

*************

   *Sokoto*
Cikin awanni hud'u ya isa a sokoton, kai tsaye gidansa ya nufa yaci abinci yae sallan azahar sannan ya miqawa kamala key yace

"Gidan da kake miyarda islam kaje ka d'akko ta ka kawomun ita anan, bana samun wayanta dan haka ka aika amaka kiranta daga ciki" durqusawa yae ya karb'i  key d'in ya juya bayan daya dire masa  yan kakkun fruit's agabansa......

    Yauma se kuka Islam kewa Nancy ita kuma se faman rarrashi takeyi

"Dama shisa nace miki ki kame kanki daga bin mazajen nan na banza....... Baze amfaneki da komai ba se tarwatsa miki future kuma kije lahirarki skelin zunubin ki ya rinjayi na ayyukan alkhairin ki islam, tunkan aje ko ina kin had'u da musibar rashin me aurenki, batun yauba ya dace islam kisan cewa kanki kikewa mugunta yau ina Ashraf? Halinki nabin maza ya kore miki shi, ina Aminu bawa? Shima yabi ruwa yae tafiyarsa, mazaje nawane sukai ta kansu wane namijinne ze auri karuwa  islam, nasha fad'a miki abinda kike  international karuwan cine me lisence bazan boye miki ba hadda laifin innah dan Baba nagani ba gayamun akaiba bayaso, har cewa yake na miki magana akan halayenki na banza yanzu wa gari ya waya? Wannan ma basanshi kike ba ai kud'insa ne ya rud'eki dabadan kud'iba nasan bazaki zauna zaman kuka haka ba"  wani yawu me d'aci ta had'iya sannan ta kalle ta kallon nutsuwa tace mata

"Bawai banason Maheer bane wlhy ina sonsa sedai bawai akan inason sa nake kukan  nan ba abu biyu ne suke sakani kuka,na farko koda zamu rabu da Maheer bata wannan hanyar naso mu rabu ba yanayin daya ganni a riqaqqiyar karuwa me zuwa kwanan gida, na biyu kuma na kwad'aitu da dukiyarsa tunda ya furta kalmar so agareni nake hangoni acikin gidansa na alfarma ina wulaqanta naira,  Nancy shejarata ashirin da uku acikkn talauci se zuwan Maheer na somawar warewa, ina samun kudi har kyautar miliyan ammun a kwana d'aya amma ni zanbaiwa wani labarin kud'in karuwan ci basa tab'a albarka!! Rasa kike me kikai dasu, amma kudin Maheer ko naira dubu biyar yaban senaga albarka ta" d'an guntun tsaki taja tace

"Kinga matsalarki ko Islam, babu Allah a ranki ko kad'an yanzu bakiji tsoron Allah ba dukkanin bayananki selfish interest nakine kawai kike fad'a haba mana islam dan Allah kiji tsoron Allah!! So nake inji kona istigfari akan abubuwan dakika aikata" kallon ta islam tae

"Indai ze aureni zan tuba wlhy" haushi ya qara kama Nancy tace

" Auu danshi xaki dena badan Allah ba? Ki tuba wa Allah kiyi komai dominsa ze cika miki burinki haba mana islam" nisawa tae

"To Nancy namiki alqawarin inshaa Allah na dena, na tuba sabida Allah kuma koda Maheer be dawo gareni ba zan dena zinace zinace har abada daga waccen danai" murmushi Nancy tae

"Nagode sosai Islam Allah ya baki ikon yin taibatun nasuha kinji qawata" murmushi tae ta rungume ta

"But i still missd him ya zanyi nancy" kan wanu yae magana sejin muryan yaro sukai a tsakar gida

" Innan salaha wai inji wani mutum yace sunansa Kamala salaha tazo suje inji Maheer" miqewa innan tae daga hura gawayin datake

"Tana ciki jeka zan gaya mata" kan innan ta shigo har islam ta miqe ta soma neman mayafi koda inna tazo sunkai waje, suna ganin kamala suka fad'a mota....

**************
   Sunyi zaman fiyeda 30 mns be shigo ba, islam dukta gama rudewa se zufa take duk AC dake parlor nan, se dukan uku uku qirjinta keyi  tana zare ido tana jin qarar bude qofa ta miqe tsaye!! Kallon wurin take harya tura kofar ya shigo qirjin ta se dukan uku uku yake, a hankali ya tako ya qaraso daf da ita har suna jiyo bugun zuciyar juna, Kuka takeyi ta kasa tsayarda hawayenta!! Shi kuma idanshi yayi jajir tamkar gaushin wuta!! Dukta qarisa rikicewa wannan daf da ita daya matso, wannan ne karonsa na farko daya matseta har haka!! Kana kallonta zaka hango yanda jikinta ke qyarma dukta rikice kallon shigarta yae yau kad'ai yaga islam da hijabi, idonshi ya sauke akan qafafuwan ta,qafan islam kawai ta cancanci yabawa bare fuskarta da surar jikinta!! Miyarda dubansa yae zuwa gareta yace murya na rawa

"Islam Why? What on earth kika nema kima rasa? That u stood so low!!! Mesa aduk sana'o in dake duniya se zina Islam!! Kinsan ko handa na tsani zina dame yinta? Kin tab'a sanin aibun zina? Zinar taki ma bawai da saurayinkiba with any man!! Meaning bakya gudin komai? Azabar Allah, daga qabari har xuwa tashin qiyama har yakaiga murqusaki cikin wutar sa islam? Ashe bakya tsoron cututtukan zamanin nan, ashe bakya tsoron mutunci da martabar iya yenki idan kinsan duk bakya tsoron wa ennan mesa arayuwa zaki shiga rayuwata? Ni dukkanin abubuwan dana lissafa ina tsoron su yaua zakimun haka?" Jin yayi shiru ya bata damar d'aga idanta ta kallesa dan tunda ya fara magana ta dire idanta a qasa!! Zubewa tae saman gwui wanta duka biyu

"Maheer dan san manzan Allah ka bani second chance!! Wlhh zan sauya, zan sauya to a good and better person please karka fita arayuwa, kayi wannan jihadin ka fitar dani acikin wannan musibar ka tallafi addinin islama Maheer ka aureni, wlhy na tuba tsakanina da Allah bazan qara ba" ta qarashe maganar tana kuka sosai me sauti!!!

Qura mata manyan idanuwanshi yae ya kasa koda motsi shin menene mafita? Ya amsawa Islam tayinta yayiwa addininsa hidima kokuma aa ya barta besan me iya auren karuwa ba?"......

*Mom Nu'aiym*

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now