page 22

3.5K 326 17
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

*Ina godiya masoyana Umm Nass wannan shafin kyauta ne agareki ki kacaccala yanda kike so amma plss kada ki Baiwa sana s matazu ko kalma daya lollxx*
                              
                     22
Yauma kamar kullum Maheer kwance yake acikin bahon wankan sa ya runtse idansa yana nazarin rayuwar duniya...Dukda yake yasan Anty Nasara mahaifiyarsu ta biyo na qyamar talakawa amma sam umma ita bata hakan takan yarda da qaddara sedai kurun bata hulda da talakawa ne ita...komai girman danganta karku idan bakada shi babu ruwan umma dakai sedai idan kazo mata tana haba haba da nan nan  dakai, amma ita taje maka batayi fara'arta da haba haba da mutane ya sanya  kullum gidan nasu baya rabo da en uwa, sab'anin Maheer da twin dinsa suna qaunar mutane sosai ga fara'a ta mahaifin  su dasuka gado ta sosan ma, Matsaloli guda biyu se mutan america su safiya da sha'awa sarakan rashin ji da jiji dakai waisu yaran masu kud'i sune sukafi kowa girman kai a gidan kaf!! Nisawa yae ya qara lumshe idansa yanajin dadin ruwan d'imin dayake cikinsa....rashin memory din Hafsat bashi bane damuwar sa a yanzu,damuwar sa biyu ce na farko dai qafarta yau zasu shiga aiki na biyu kuma rashin maganar ta muryarta kadai yanasi yajita koze samu nutsuwa me sanyi!! Yarasa menene yakeji game da wannan yarinyar abu d'aya ya sani yanajinta har cikin jini,jijiya da b'arqon sa...kai harma qasusuwan sa sunsan da zaman ta acikkn jinjinsa da jijiya sabida sukan amsa suma.....yana yiwa Hafsat Son so!!! Qaunace daga indallah be tab'aji yana sonta da aure ko soyayya ba amma ya kasa fuskantar inda zuciyar sa ta dosa akan hafsat!!!!  Haka ya gama wankan sa ya fito ya shirya tsaf ya nufi asibitin..... A kan hanyar zuwa asibitin islam ta masa waya dayike tana sokoto Hafsat tare da Mahaifiyar ta  take.....

"Honey dama cewa zan maka ko za'a d'auke lokacin bikin nanne naga saura kwana bakwai ko IV ba'a kawo ba gidan ma harsun soma mgana" Sajen fuskarsa ya kaiwa laluba kanya qara kame staring yace

"Afwan Babyna, wlhy rashin lapiyan hafsat ne ya sanya na shafa gaba d'aya da zancen iv d'in nan amm kuma kinsan abba daddy baze tab'a sauya date d'in aurena ba sabida commitment nasa yagama schedulling da komai akan hakan,so yanzu inaga zan miki transfer seki nemi wani buga iv a garin naku ya buga muku naku na mata, na daurin auren ma daddy ya aiko nine zan aiko dashi but na manta wlhy" Bataji dad'in kalaman saba koda yike itama    tanada damuwa sosai akan ciwon hafsat amma tana ganin be cancanci ya shaagala da sha'anin auren ba akan shi ace saura sati d'aya,cikin kasala ta furta

"Amma Honey hakan ai ba daidai bane, daga wurinku ake aiko da kati da alawa a al'adar sokoto fa" Haka kawai ya saka mata fad'a

"Haba Islam!! Ke bakya ganin ina cikin tashin hankali ne inada patient? Agidan mu wayakeda lokacin zuwa sokoto yin wannan abin, kinga dire al'ada gefe zanwa Ameena transfer koma namai magana asiya komai akai muku ina idan friend dina yazo babu damuwa?" Sekuma ya qarashe maganar cikin sigar rarrashi, hakuri ta bashi sukai sallama akan gobe   za'aje akai....

***************

    Tunda yaje asibitin ya kasa sukuni cox ana kan aikin qafar basu fito ba, tunawa da yae agidan sa na kano daza'a kawo islam akwai wuraren da babu funiture ya manta ba'a saka ba, tsaki yaja ya kira islam

"Honey ina wuni yaya anfito aikin ne?" Ga alama tunkan su fara magana harya qosa  da maganar

"Ammm cewa nayi kin iya tuqi kuwa?" Bataji dad'in yanda yae ba amma jiki a sanyaye tace

"Ea na iya amma automatic kawai ban iya manual ba" jinjina kansa yae kamar tana ganinsa

"Kije gidan cen tunda key yana hannun ki ki shiga bed room d'ina ki duba a drower mirror akwai key's na motocin gidan farar jeeb dinda ke gidan kawai ce auto seki dauketa, idan ackin qannenki maza wanda ya iya tuqi seki bashi benz black sabida hidin dimun gida ke kuna ga naki hidima, sannan kuma gobe zan aiko kamala dukkanin abu nawa dayakeda muhimmanci agidan nan ze kwashemun shi zuwa sabon gidanki na sokoto, ku koma wannan gidan keda en gidanku da kowa ma, amm sannan kuma akwai d'akuna biyu acikin gidanki na kano dava komai aciki yaya kikeso ayi dasu, a zuba wane color zan kira company tun ban manta ba, amma se kuma nangidan shima daki biyune da furniture sauran tile ne kawai me za'a saka zanwa wani company magana a sokoto  yazo yae wannan gyaran" Godiya taita masa kantace

"Dan Allah Maheer hidimar nan tayi yawa ka taimaka kabarshi a hakan zamu saka anan din, Allah ya saka da alkhairi yabar qauna na kanon ma inda aka gyara ya wadatar" Shiru kamar bazeyi magana cen se kuma yace..

"Amm dan Allah salaha karkice zakiyi bidi'o in nan wlhy samun lapiyar hafsa ce a gabana, ki taqaita zanzo iya dinne kinji babyna, idan zakiyi jmahagulgulanki kiyi amma karkice ban zoba" Numfashi ta fesar
."Dinner da walima kawai zanyi karka damu, se magaana ta gaba yaya zancen  tariya sokoto ne ko kano" gyaran zamansa yae

"Kano za'a kawoki Mana ai nanne garinmu, abu na biyu sokoto sabida nan nakeyin aiki dole mu koma sannan na sanar dake bazaki ci gaba da karatu bako? Zan miyar dake wani skull daban bansan wannan yawon" haka taita binsa da toh har sukai sllam, annan ta durqushe taita kukan wahalar data daukarwa kanta...

Lapia lau aka wa hafsat aikin qafar anyi nasarar daurin sedai fa dawuya be karkace ba se wani hukuncin na Allah.

***************
    Yau Ameen da ummul suna zaune a parlor ya hade girar sama data qasa, tamkar be taba dariya ba ummul ta kallesa tace

"Yaa Ameen banida lapia ciwon mara nake da yawan tashin zuciya gashi daga zaran na zauna kome nake se bacci" wani annashuwa da annuri ya bayyana a fuskar sa na lokaci d'aya  ya kalleta

"Auu haba, barin kira miki Familu Dr. Dinmu ko" kallon mamaki take masa yanda ya sauya to ciwon nata ne abun murna, haka Dr. Yazo ya duba ta ya tabbatar cikine da ita 2 months mamaki ya kama Ameen shida yake da saurin gane ciki, kodan tayi period se biyune ya sanya yake tunanin babu, ya kalli Dr. Din

"Takan yi period fa yallabai yazace ciki har 2 months?" Murmushi Dr din yae

"Zata dena ne wasu matan sukanyi hakan, so kawai ta dena aikace aikace cikinta baya so shisa take ciwon mara" ranar murna awurin Ameen ba'a magana aikam hafsat har  abinda ba'aso seda aka mata!! Kanta ya d'aure ta soma tunanin anya nrman haihuwabaure da watanni biyu hankaline kuwa? Amma dai dukda haka zataga qarshen abin.

Mom Nua'aiym

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now